|
Rana da wajen da aka haifi Sheikh:
An
haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953[15 ga Sha'aban
1372 AH] a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma
sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'.
Sheikh
Ibrahim Zakzaky shine dan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan
Tajuddin dan Imam Hussain. Shi Imam Hussain wani bawan Allah ne daya
fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan
Fodio[RA] ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a
lokacin da Shehu Usman dan Fodio[RA] ya nada Mallam Musa a matsayin Amir
na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi
shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin
iayalen su kuma suka zama yan uwan juna ta wannan tun a farkon karni na
19.
Mahaifin Sheikh
Ibrahim Zakzaky ya rasu ne tun shekara ta 1972, sai dai mahaifiyar sa
har yanzun tana nan raye, Sheikh shine na biyar a wajen mahaifin su.
Karatun sa:
Sheikh
Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar
koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar
yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen
manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru
goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara
ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake
Zaria. Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon
larabci ta Kano watau School for Arabic Studies[SAS] wadda aka gina tun
1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita
ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. Kusan baki
dayan alkalin alkalan jihohin Arewa daga wannan makaranta suka sami
horon su. Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin fadada ilmin
sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama
karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba
kamar sanin gwamnati [Government] da ilmin tattalin arziki[Economics]
inda yayi jarabawar GCE a kansu. Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta
gaba[Advanced level GCE] akan wadannan maddojin:Government,
Economics,Hausa,da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija
wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979
inda ya fara karatun digirin farko [B. Sc] akan sanin tattalin arziki
[Economics].
Sheikh yayi
musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a
cikin makaranta da kuma matsayin kasa baki daya inda a shekara ta 1978
ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama
mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara
ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare
Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga
Shari'ah a baki dayan kasar.
Sheikh
Zakzaky bisa sha'awar da yake da ita na fadada karatun sa ya ci gaba da
zuwa wajen malamai da suka hada da Malam Sani Abdulkadir, Malam Isa na
Madaka, Malam Sani Na'ibi da kuma Malam Ibarhim Kakaki dukkanin su a
birnin Zaria. Haka nan kuma a Kano Sheikh yayi karatu wajen Shawish
Abdallah na Sagagi da Malam Nuhu limamin Yola.
Ayyukan sa:
Babban
aikin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya sanya a gaba shine karatu da kuma
yada ilmi tun yana matsayin dan makaranta har ya zuwa wannan lokacin. An
mayar da koyarwan sa cikin yan littafai a harshen Hausa da Turanci
wadanda aka watsa su a ko ina cikin kasar sannan da yawa daga cikin
wa'azuzzukan sa a yanzu suna cikin CD na Computer da kaset-kaset na
Recorder a ciki da wajen kasar. Dr. Iqbal Siddiqui ya taba siffanta
Sheikh a matsayin "Kashin bayan harkar musulunci a Nigeria" Babban
manufar harkar musulunci da Sheikh yakewa jagoranci shine wayar da kan
musulmi abin daya doru a kansu a matsayin su na daidaiku da kuma
al'umma.
Yanzun haka
harkar musulunci tana da makarantu dake karkashin ta na Primary da kuma
gaba da Primary sama da dari uku wadanda suke a garuruwa daban daban
dake fadin kasar. Wadannan makarantu an yi musu suna da makarantun
Fudiyya. Haka kuma akwai cibiyoyi da da wuraren bincike da dama a manyan
garuruwa na kasar karkashin wannan harka. Harkar ta mallaki jaridar da
tafi ko wacce a kasar shiga ko ina da harsheen Hausa wadda ake kira
Al-mizan. Sheikh ya sami matsala da hukumomi cikin kaki ko fararen kaya
wadanda suke ganin cewa irin salon wa'azin nasa yana barazana ga mulkin
su. A lokacin General Sani Abacha an kama Sheikh ne da tuhumar yana
wa'azin 'babu hukuma sai ta Allah'.
A
halin da ake ciki dai yanzun haka harkar musulunci karkashin jagorancin
Sheikh Ibrahim Zakzaky ta cika shekaru 30 tana kira kan komowa
karkashin tsari na musulunci.
Tsawon tsarewar da aka yiwa Sheikh:
Sheikh
Ibrahim Zakzaky ya kwashe shekaru tara a tsare a kurkuku daban-daban na
kasar, daga shekara ta 1981-1984 an daure shi a kurkukun Enugu sai kuma
kurkukun neman bayanai da bincike na jami'an leken asiri na kasa dake
Lagos[Intorregation center] a shekara ta 1984-1985 sai kuma Kiri-kiri a
shekara ta 1985 kurkukun Port harcout daga 1987-1989 sannan daga
1996-1997 duk dai a can Port Harcout. Sai kuma kurkukun Kaduna a 1987
sannan daga 1997-1998.
Tafiye-Tafiyen sa:
Sheikh
Zakzaky yayi tafiya zuwa kasashe kamar su Britaniya, Saudi Arabia,
Iran, Lebanon, Afrika ta kudu, Amurka, da Rasha. Dukkanin wadannan
tafiye-tafiye yayi sune ta hanyar gayyata don dalilai na addini ko
halartan tarurrukan karawa juna ilmi.
Mata da yara:
Sheikh yana da mace daya da kuma yaya tara.
| |
Tuesday, 16 July 2013
Takaitaccen tarihin rayuwar jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky (h)
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment