Monday, 15 July 2013

RADDI AKAN MASU KARYATA AUREN MUTU'AH



Daga sheikh Nuru Darus-thaqalaini
Salaamun alaa manit-taba'al-hudaa.

TSOKACI AKAN MAGANGANUN AMMAR ABU TURAB [AL-MUZAWWAR]

Duk mai karatu, kuma ya ke da lura da fahimta da kuma hankalin da Allah ya tanadar masa don tantance gaskiya da qarya, haske da duhu, ko da kuwa bai da ilimi, ya san inda wannan tattaunawa ta fuskanta, ta inda qoqarin da Ammar Abu Turab (Al-muzawwar) ya yi na qwatar xan'uwan Malam Rabi'u bai haifar da wata natija ta hankali ba, balle ma ace ta ilimi, domin ba bu komai a cikin wannan rubutu na sa face maimaici ba komai. Domin dukkanin maganganun na sa xan'uwansa ya kawo mafi jullinsu, kuma mun kawo warwararsu har waxanda shi kansa Malam Rabi'un bai kawo ba. Ya jama'a masu hankali shin wannan ba za mu iya kiransa da vata mana lokaci ba da rashin aikin yi? Ko kuwa irin halin da kuka saba ne da kuyi ta maimaita abu xaya don ku kautar da abinda muke kawowa na tsantsar gaskiya da hujja yankakkiya?!

Alaa ayyi haalin, wannan bai gajiyar da mu wajen sake fitowa da jama'a abin da ya tabbata na gaskiya. Don haka zamu bi maganar Ammar mu xauki masu dama-dama, waxanda ba shirme ba bu maimaici mu fitowa da jama'a wasu nuquxoxi da ya kamata su riqe da suke tabbatar da halascin auren na mutu'a, ba haramcin ba.

Ammar ya fara da maimaici akan ruwayoyin Khaibara, waxanda duk maimaici ne akan maganganun da Malam Rabi'u ya kawo, ta inda tun a baya mun kawo "Tahqiiqaat wat-tanqiihaat" na manyan Malamansu masana ilimin Hadisi waxanda suka tabbatar da waxannan ruwayoyi na hanin auren mutu'a na Khaibara da irin jahilan Wahabiyawa ke riqo da su dukkaninsu na qarya ne, kamar yadda ya gabata a maganganunmu na baya da abin da kowa ya ce akan nuna Hadisan Khaibara na hanin mutu'a duk na qarya ne, mai son qarin bayani ya koma baya [http://www.facebook.com/notes/fayza-ummi-ahmad/raddin-da-mujaheed-nuruddeen-ibn-muhammad-yayi-akan-maganar-muhammad-rabiu-a-sha/167250780004934], wanda daga ciki mun kawo:

1-      Ibn Hajar mawallafin Fat'hul-baariy.
2-      Al-ayniy – daga Ibn Abdul-barr.
3-      Al-qisxalaaniy – daga Baihaqiy.
4-      Ibn Qayyim.
5-      Ibn Kathiir.

Wanda qo an qi ko an so kamar  yadda mu ka sha bayani, shi Hadisi ko Tarihi ya kan zamo tabbatacce kuma ingantacce ya yin da aka sami sanadinsa ya cika dukkanin qa'idojin inganci, sannan kuma da tantancewar Malaman Hadisi da suka tabbatar da ingancin Hadisi. Fat'hul-baariy xin nan kowa yasan Sharhi ne na Sahiihul-Bukhaariy wanda Ahmad bn Aliy Ibn Hajar, wanda aka fi sani da Asqalaaniy ya wallafa, kuma a ciki ya yi tahqiiqi ya tabbatar da waxannan Hadisai da suka nuna hanin auren Mutu'a a Khaibara duk na qarya ne ba su tabbata ba domin ba bu wanda ya san waxannan ruwyoyi daga Malaman Siirah da masu naqalto Hadisi. Haka nan ma sauran Malaman duk Tahqiiqinsu ya na qaryata ruwayoyin Khaibara ne, ga misalign maganganun Malamai uku:
  • Ibn Hajar a cikin sharhinsa na Fat'hul-Baariy daga As-suhailiy yace: "Kuma wannan Hadisin yana tattare ne da tsoratarwa akan matsalolinsa; domin a cikinsa akwai hani akan auren mutu'a ranar Khaibar. Kuma wannan (hanin) babu wanda ya sanshi daga Malaman Sira da Ruwwatul-athar (Masu naqalto Hadisi)" (Malam sai aje a duba: Fat'hul-baariy 9/210).

  • Haka nan dai Malam Ainiy da sharhinsa yace: "Ibn Abdul-barr yace: Kuma ambaton hanin mutu'a a ranar Khaibar kuskure ne (Galax)" (Umdatul-qaariy: 17/246).

  • Haka dai Al-qisxalaaniy shi ma da sharhinsa yace: "Baihaqiy yace: ba bu wanda ya san shi daga cikin Malaman Sira (Tarihi)" (Irshaadus-saariy: 11/397, 9/232).

Shin 'yan'uwa na masu neman gaskiya Tahqiiqin waxannan gingima-gingiman Malaman zamu karva waxanda duniyar Sunna da su take alfahari da riqo, ko kuwa tahqiiqin irinsu Ammar, Rabi'u, za mu karva, waxanda ba bu wanda ya san Shuhurarsu akan wani Ilimi ko da a iya garinsu balle Qasarsu har kuma akai duniya?! Mutanen da na sha faxa su kansu "Muqallidai" ne, su ma riqo suke yi da waxannan Malaman, su kan su tunaninsu, hankalinsu ba hujja ba ne a kansu balle waninsu?! Mu dai akan Hadisan Khaibara na qarya da aka dangantawa Manzon Allah (S) da Wasiyinsa (A), tahqiiqin Malamanku da suka nuna duk na qarya ne ya ishe mu, ba mu buqatar naku 'yan aci a basu!


Ruwayoyin kuwa da Ammaru ya kawo akan haramcin auren mutu'a, ban ga fa'idarsu ba, domin mu da kanmu a rubutun na mum un kawo wasu daga ciki, kuma muka kawo ingantattu da suke karo da su. Wanda daga ciki ne shi Ammar ya kawo Hadisin Sabratal-juhaniy, sai dai abin tausayi shi kansa Malam Rabi'u ya kawo xaya daga cikin Hadisan Sabrata xin inda muka mayar masa da martini kamar haka:

"To amma da shi Malam Rabi'u idanuwansa sun kai kan waxannan Hadisan da suka zo a wannan lamba ta (1406) da bai yi hanzarin kawo shi a matsayin hujja ba. Saboda Hadisin farko ma na wannan lambar (1406) ko kuma a wata Xaba'ar Hadisi na (3485), yana nuna tsantsar halasci ne, kuma Manzon ne ma ya umarta a lokacin da aje ayi auren mutu'ar a wannan Yaqin, wanda qarshen maganar ma ga abin da Manzon (S) ya ce: "….. Duk wanda ya kasance a tare da shi akwai wannan matar ta mutu'a to ya sake ta". Shin ka sani ko fagen fama za'a faxa aka ce su sake su, ko kuwa gida za'a dawo?! Ga nan matanin Hadisin:

"وَحَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا لَيْثٌ عَنِ الرَّبِيعِ بْنِ سَبْرَةَ الْجُهَنِىِّ عَنْ أَبِيهِ سَبْرَةَ أَنَّهُ قَالَ أَذِنَ لَنَا رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- بِالْمُتْعَةِ فَانْطَلَقْتُ أَنَا وَرَجُلٌ إِلَى امْرَأَةٍ مِنْ بَنِى عَامِرٍ كَأَنَّهَا بَكْرَةٌ عَيْطَاءُ فَعَرَضْنَا عَلَيْهَا أَنْفُسَنَا فَقَالَتْ مَا تُعْطِى فَقُلْتُ رِدَائِى. وَقَالَ صَاحِبِى رِدَائِى. وَكَانَ رِدَاءُ صَاحِبِى أَجْوَدَ مِنْ رِدَائِى وَ كُنْتُ أَشَبَّ مِنْهُ فَإِذَا نَظَرَتْ إِلَى رِدَاءِ صَاحِبِى أَعْجَبَهَا وَإِذَا نَظَرَتْ إِلَىَّ أَعْجَبْتُهَا ثُمَّ قَالَتْ أَنْتَ وَرِدَاؤُكَ يَكْفِينِى. فَمَكَثْتُ مَعَهَا ثَلاَثًا ثُمَّ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- قَالَ « مَنْ كَانَ عِنْدَهُ شَىْءٌ مِنْ هَذِهِ النِّسَاءِ الَّتِى يَتَمَتَّعُ فَلْيُخَلِّ سَبِيلَهَا".

Shi wannan Hadisin da aka ruwaito shi daga Sabratal-Juhaniy ya na da hanyoyi da yawa wasu Hani wasu Halasci, waxanda Muslim da wasunsa sun fitar da su daga Ma'abota Sunan da Musnad, wanda akwai ruwayar da ta ke nuna Hanin ya faru ne a Fat'hu Makkah wato a watan Ramadhaan a shekara ta takwas bayan Hijira".

Sai Hadisin da shi Ammar xin ya kawo na ruwayar Iyaas bn Salamah bn Ak'wa'u, wanda shi kansa tun kafin Ammar xin ya kawo su shi ma mun kawo shi kuma mun yi magana akan sa, inda muka ce:

" Sannan akwai wata ruwayar  daban da aka fitar da ita daga Muslim a cikin Sahihinsa, daga Iyaas bn Salamah bn Ak'wa'u daga Babansa ya ce: "Manzon Allah (S) ya yi rahusa a shekarar "Auxaas" a cikin Mutu'ah sau uku sanan ya hanata".

To abin lura anan shi ne shekarar "Auxaas" shi ne dai shekara ta takwas bayan Hijira, don haka anan akwai rikitarwa da kuma tanaqudi mai ban mamaki ta inda ya tabbata da Hadisan da ma su wannan magana suke quduri da su akan shafewar Halascin, aka Mutu'ah ta kasance Halas har lokacin "Hajjatul-wadaa'i" wato shi ne shekara goma (10) bayan Hijira. Ga Hadisin da ke tabbatar da hakan akan Auren mutu'ar yana nan da Halascinsa har shekara goman bayan Hijira:

Malam Daaramiy ya fitar da shi a cikin Sunan xinsa yace: "Ja'far bn Awn ya bamu labari daga Abdul-Aziiz bn Umar bn Abdul-Aziiz daga Rabii'u bn Sabrata daga Babansa ya bashi labari akan sun kasace tare da Manzon Allah (S) a Hajin ban kwana sai yace: "Ku yi mutu'a daga waxanan matayen, domin mutu'a a wajenmu Aure ne (Wannan maganar kuwa tana dukan bakin masu cewa ba aure ba ne), …………….. [har inda Manzo (S) ya ke ce wa] …. Sai yace: ya ku mutane haqiqa Ni ne na yi muku izini akan yin auren mutu'a da mataye, to ku sani haqiqa Allah ya haramta shi har zuwa tashin Alqiyama …….." (Sunanud-Daaramiy: 2/140)".

Inda mu ka qare da wannan maganar:

"Don haka wannan ruxanin ya afku akan wannan ruwayar yana daxa tabbatar da qaryar Hadisin da ke nuna Hanin, sannan ma kuma ga wasu tilin Hadisan da suke nuna qarya ake yiwa Annabin Allah (S) akan wai ya Hana, dukkanin Sahabbai sun tafi akan Umar xan Haxxabi ne ya hana, kuma ba su yarda da wannan Hanin nasa ba saboda sun san savawa ne da Qur'ani da Sunnar Manzon Allah (S)".

Wanda a bisanin wannan ne ma muka goye da: [KAXAN DAGA CIKIN HADISAN DA SUKE KARO DA WANNAN HADISIN NA HANI].

INDA A WANNAN HADISAN NE MUKA KAWO HADISAI TABBATATTU INGANTATTU DAGA MANYAN MALAMAN SUNNA XIN DA SUKE GOGE DUKKANIN WANI HADISI MA DA YAKE NUNA ANNABI (S) NE YA HARAMTA MUTU'A, ga kaxan daga ciki:

  • Malam Muslim ya fitar a babin "Nikaahul-Mut'ati" ruwayoyi da yawa daga Jaabir bn Abdullah, da Abuz-Zubair, cewar su sun yi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi), da zamanin Abubakar, har lokacin da Umar xan Haxxabi ya hana.

  • A cikin Sahihul-Bukhari kuwa cewa yayi: an saukar da Ayar Mutu'a a cikin littafin Allah, mun aikata ta tare da Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) kuma Qur'ani bai sauka yana haramta ta ba kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) bai hana ba har ya Rasu. Sannan wani mutum kawai yazo ya faxi son ransa. (Sahihul-Bukhari: 5/185).

  • Wani dalilin daban akan rashin shafe ta shi ne Shaharar ta (Mutu'a) ga Sahabbai da Tabi'ai da "Fuqahaa'u" Malamai, har zuwa lokacin da Mazahabobi huxu suka kasance suna bayyana ta a fili a Qarnoni na biyu na uku da na huxu.

Shaida akan haka kuwa shine abinda  Malam Bukhari da Malam Muslim a ingantattun litattafansu na Hadisi suka ruwaito na ruwayoyi daga Salamah binul-Ak-wa'u bn Mu'iid, da Jaabir bn Abdullahil-Ansaariy, da Abdullahi bn Mas'uud, da Ibn Abbaas, da Sabrata bn Mu'iid, da Abu Zarril-Gifaari, da Imraana bn Hasiin, da Ak'wa'u bn Abdullahil-Aslamiy. (duba: Sahih Muslim Sharhin Nawawiy: 9/179 – 189, da Sahihul-Bukhari Kitabut-Tafsir Babi na 33 Hadisi na 4156, da Kitaabun-Nikaah babi na 32 Hadisi na 4724, da Kitabul-I'itisam babi na 28 Hadisi na 6819).

WANDA NI NURU "Ar-raafidiy" INA FAXA DA BABBAR MURYA IDAN WAHABIYAWA ZASU CIKA DUNIYAR NAN DA HADISAN QARYA DA SUKE CE WA WAI ANNABI (S) YA HARAMTA MUTU'A, TO IYA WAXANNAN HADISAN DA MAGANGANUN MANYAN MALAMANKU XIN NAN DA NA KAWO NAN SAMA KAXAN SUN GOGE HADISANKU NA QARYA, KUMA SUNA TABBATAR DA HALASCI AUREN MUTU'A NE TUN DAGA RANAR DA AKA HALASTA TA HAR TASHIN ALQIYAMA!

Maganar kuwa da Ammar ya ke faxa wai "MUTU'A ZINA CE, IN JI MAGABATAN WANNAR AL'UMMA", wallahi wannan ba komai ya ke nunawa ba illa qarancin hankali da ilimi. Su waye magabatan?! Umar bn haxxabiy da 'Yan barandarsa ne magabatan?! Akwai wani magabaci da ya wuce Annabi Muhammad (S)?! manzon Allah (S) y ace Mutu'a halas ce, kuma har ya yi wafati ya bar abin a hakan ga shi nan da shaidar Sahabbai suna tabbatar da ce wa Manzon Allah (S) ya yi wafati ya bari ana yin auren Mutu'a amma wani mutum ya zo da ra'ayinsa ya ce haram ce. Shin wanan ba fito na fit one da Annabi (S) ba?! Shin wannan ba nuna Annabi (S) bai iya ba ne Umar shi kaxai ne ya iya?! Shin ba wannan Ubangij qarara ya hana ba a cikin Qur'ani magirma?! Shin Allah bai hanin; Ubangiji ko Annabinsa su ce ga hukuncin abu wani daban ya ce ga wanda ya fib a?!

Allah maxaukakin Sarki ya na faxa a cikin Suratul-Ahzaab aya ta (36):

" وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا"
Ma'ana:
"Kuma ba ya halasta ga Mumini ko kuma Mumina, idan Allah da Manzonsa suka zartad (Hukunta) wani lamari, wasu suce ga nasu zavin ba na Allah da Manzonsa, wanda kuwa duk ya savawa Allah da Manzon (Cikin umarni, cikin zavi,……) tabbas wannan ya vata vata mabayyani".

Shin ya halasta ga wani ko waye shi, Annabin Allah ya ce abu halas ne shi kuma ya ce haram ne?! wallahi summa tallahi duk wanda kuwa ya aikata wannan to yana daga cikin waxanda wannan aya ta yi musu tambari da vata!

Shi kansa Oga Uban tafiyar ya yarda da cewar Mutu'a Halas har Manzon Allah (S) ya yi wafati, shi ne da son iyawarsa, wataqila ko ya manta da wannan ayar ce, shi ya sa ya ce ya haramta abin da Annabi ya halasta. Inda ya ke ce wa:

"متعتان كانتا على عهد رسول الله (ص) أنهى عنهما وأعاقب عليهما متعة النساء ومتعة الحج"
Ma'ana:

"An kasance ana yin Mutu'a guda biyu zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) to ni na hana kuma zanyi azaba akansu, Mutu'ar Aure da Mutu'ar Hajji" (Sharhul-Ma'aanil-Athar: 2/146, Malam Ahmad bn Muhammad bn Salmatul-Azdiy).

Amma sai ga shi su Ahlus-sunna xin sun saki hani xaya daga hani biyun da Umar xin yayi sun kama xaya. Domin kuwa har yanzu suna riqo da Mut'atul-haj, wato Hajin Tamattu'i, bayan shi gaba xaya biyun ya hana, wannan wane irin son rai ne?!

Tabbas da ace akwai wani abu dake nuna shafewar daga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da ya xan jona shi a maganar sa, da bai tsaya danganta abin gare shi shi kaxai ba. Don haka a kan kansa, maganganun shafewar inkarin maganar Halifan ne.

Haka nan dai a cikin waxanda suka fitar da wannan Hadisin na maganar Umar xin:
1-      Littafin Ma'rifatus-sunan wal-aathaar na Baihaqiy a babin auren mutu'a.
2-      Haka nan da littafin Sunan Sa'iid bn Manzuur, a babin "Maa jaa'a fil-mut'ah".
3-      Jaami'ul-ahaadith a babin "Musnad Umar bn Khaxxaab".

Shin hanawar Umar bn Haxxabiy a matsayin shi kansa ya savawa Annabi (S) ne, shi ne zai zamar da Halas xin Annabi (S) haram?! Ko kuwa shi ne zai zamar da auren mutu'a zina?!

Shi kansa Umar da ya nuna da bakinsa an kasace ana yin auren mutu'a a zamanin Manzon Allah (S) shi ne ya hana a bayan Halifa Abubakar, sannan a qarshen zamaninsa (Wanda wannan shi ne abin da sukkanin Malaman duniya suka yi ittifaqi akai, na Umar ne ya hana). To ku Wahabiyawa ku sani lokacin da Umar xan Haxxabi ya zo mutuwa sai da ya kasance yana qarfafa cewar irin waxannan karan-tsaye da sassavawa Annabi da ya yi, da faras da sababbain abubuwa da ya yi a bayan Annabin (S), za su iya kai shi ga faxawa azabar Allah.

Ku je ku duba cikin Sahiihul-Bukhaariy a babin da ya ke magana akan darajojin Umar, sai Buhari ya kawo wannan Hadisin:

Hadisin na nan garau a cikin Buhari a juzu'insa na 12, shafi na 454, Hadisi na 3692: daga Miswar bn Makhramata yace; "Ya yin da aka soki Umar (Xan Haxxabi) ya kasance yana jin raxaxi, sai Ibn Abbaas yace masa – kamar yana nuna masa damuwarsa – ya Amiirul-muminina, yaya haka (kake cikin wannan ximuwar mutuwar) bacin ka abokanci Manzon Allah (S) kuma ka kyautata abokantakarsa, sannan kuka rabu da Shi yana mai yarda da kai, sannan ka abokanci Abubakar ka kyautata abokantakarsa, sannan kuka rabu yana mai yarda da kai, sannan ka abokanci Sahabbansu ka kyautata abokantarsu, wanda kuma idan zaka rabu da su zaka rabu da su ne suna masu yarda da kai. Sai (Umar) yace, amma abin da ka ambata na abokantakar Manzon Allah (S) da yardarsa, to haqiqa wannan Baiwa ce daga Allah yayi min Baiwa da ita, amma kuma abin da ka ambata na abokantakar Abubakar da yardarsa, to haqiqa shi ma Baiwa ce daga Allah yayi mini Baiwa da ita, amma abin da kake gani na wannan damuwar tawa da firgici (Jaza'u), yana daga cikin sakamkonka da sakamakon abokanka (wato abin da ya farar a tsakaninsu bayan Manzon Allah ya yi wafati na canja hukuncin Annabi daga Halas ya koma Haram – kamar auren mutu'a, da kuma daga Haram zuwa Halas – irin su Sallar Tarawi da qiyamul-lail a jam'i, ………. ), (sai Umar yace) wallahi da ina da Zinare wanda yawansa zai cika sama da qasa da na bada shi fansar azabar Allah Maxaukakin Sarki tun kafin na ganShi" .

A gefe guda kuma ga Aya tana cewa:

"Haqiqa waxanda suka ce, Ubangijinmu Shi ne Allah, sannan suka tsaya cak akan hakan, Mala'iku na sauka garesu (yayin mutuwarsu), (suna ce musu) kada kuji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ana yi muku bushara da aljannar da aka kasance ana yi muku alkawari" (fussilat: 30).

Wanda anan  take zaka ga mutum yana murmushi a xauke ran nasa ma bai sani ba. To wannan fa shi ne qarshen canja Umarni ko Hukuncin Annabin Allah.

Shin tarin Hadisai ba su zo ba a cikin Buhari da Muslim a babukan "Kitaabul-fitan", a inda Manzon Allah (S) ya ke gayawa Sahabbansa yake cewa a ranar alqiyama za a zo mini da wasu mutane (daga cikinku) sun sanni Ni ma Na sansu, ina bakin tafikina na alkauthara na yi haka zan xebo rowan na ba su, sai a jayesu daga gare Ni, sai nace ya Ubangiji, waxannan fa Sahabbai na ne, Sai a Ubangiji yacewa Annabi sun canja addini a bayanka, sai Manzon Allah (S) yace musu shi ma: "Suhqan suhqan liman baddala wa gayyara ba'diy".

Haba jama'ar Wahabiyawa shin duk wannan bai isheku izna ku gane ga babban Limamin naku ya yi furuci da bakinsa ya canja Umarnin Annabi, yace ana yi a zamanin Manzo, amma ni na hana, kuma ga shaidar da ya bayar da bakinsa da zai mutu, kuma ga Hadisan da kuka ruwaito akan mai canjawa da jirkita addini ba, ku sake shi ku zo ku kama Ahalulbayt ba, waxanda Annabi ya basu Tahqiiqi akan ba za su rabu da Qur'ani ba har tashin qiyama ba?! Ku saki waxancan tarkacen da ko a yaqin Uhudu yaqi ya shaede su akan zasu cika da imani ba! Yakamata fa jama'a ayi hattara!

MAGANA KUWA AKAN ZINA.

Amma Magana akan cewa tayi kama da zina ko Mutu'a Zina ce to lallai wani babban haxari ne, koda kuwa an shafe hukuncin halascin balle kuma ba'a shafe ba. Domin kuwa yana nufin ne Mai Shari'a Mai Tsarki (Ubangiji) ya halasta Zina sannan ya haramta ta. Shin Musulmi zai yarda da wannan?!

Ya riga ya gabata cewar auren Mutu'a aure ne kamar auren Da'imi, yana da Sharaxai da Qa'idoji, sune: Xaurin aure, da bada Sadaki, da sanya Lokaci, da Hankali, da Balaga, da rashin samun wani hanzari na Shari'a da zai hana, kamar Nasaba, ko wani dalilin ko an sha Nono tare, ko wani abu makamancin haka. Amma a Zina kuwa ba a Xaura aure, Xa bashi da dangantaka da Mahaifinsa, bazai Gade shi ba, babu wata alaqa ta aure, babu Idda a cikin Zina. Don haka kwatanta ma Mutu'a da Zina wata vatacciyar Maganace, wanda mai faxarta ma wani Wawa ne marar tunani da dalili da son jayayya.

E, yana iya yiwuwa wasu suce shi auren Mutu'a an Shar'anta shi ne abisa domin samun wata fa'ida vangaren yasassiyar zuciya da raunananniya.

Jawabi anan shine: Ita Duniya cike take da abubuwa bayyanannu masu kyau da ke tsaye kyam wajen amfanar da xai-xaikun abubuwa marasa kyau. (Misali, idan muka xauki kamar Wutar Lantarki, zamu ga anyi ta ne don wata fa'ida ga Al'umma, shine; suga Haske, su kunna Na'urori, da sauran su. Amma a vangare daban sai muga tava ta da Hannu ko Jiki kan iya aikawa da mutum Lahira nan take. To shin zai yiwu ace don wannan dalili kwata-kwata ace an hana amfani da Wutar Lantarki? Ko kuma idan muka xauki Batirin mota zamu ga ai don amfanin da aka yi shi, to yaya idan mutum ya zuba a Ido ko uwa-uba ya sha? Shin shima don haka kwata-kwata sai ace a daina yin ruwan Batir gaba xaya?).

Wanda mafita a kwatankwacin wannan yanayi ba wai sai an haramta ainihin gundarin abin ba. Abin da yake kawai shine samar da wasu hanyoyi na vangaren halastawa tsakanin waxannan fitattun abubuwa masu kyau dake taimakawa ko fa'idantar da abubuwa marasa kyau. Don haka da samuwar Mai Shari'a na Musulunci (Mujtahidi) sai ya sharxanta wasu sharaxai na zamani na dole wajen yin auren Mutu'ar, don kuvutar da wannan halascin Shari'a daga waxancan vatattun.

Hakane abinda yazo mana valo-valo na daga Nassosin Qur'ani mai Girma da Sunnar Manzon Tsira (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Nassosin Sahabbai da Tabi'ai na tabbatar da Shar'ancin auren Mutu'a gaba xaya. Da rashin tabbatar shafewar hukuncin nasa daga mafi yawan Sahabbai da Tabi'ai. Hakan ma a gurin Ahlul-Bait Tsarkaka, sune "Aliyyu" Sayyidul-Awsiyaa' da 'Yayayensa Imamai Ma'asumai (Alaihimus-salam su goma sha xaya) da Malaman Makarantar su ta Fiqhu xaya bayan xaya.

Auren Mutu'a aurene halastacce ga Shar'a kamar auren Da'imi a Shari'a ta Musulunci, wanda ya xan sava a wasu hukunce-hukunce waxanda muka ambata a baya.

Amma kuma ruwayar Umar xan Haxxabi ba wata abar dogaro bace wajen shafe hukuncin auren Mutu'a kamar yadda ya tabbata abaya daga bakunan su kansu Sahabbai da Tabi'ai xin. WANDA yana daga ciki irin raddin da xansa abdullah yayi masa da aka yi masa tambaya akan menene matsayinsa akan auren mutu'a, yace; halas ne. aka ce masa me zai ce ga maganar babansa (umar xan haxxabi) da ya haramta? ya ce shin umarnin babana zan bi ko kuwa umarnin manzon allah?! (bukhari).


Idan kuwa mu ka komo maganar da Ammar ya ke faxa akan Ayar "Famastamta'tum bihi minhunna fa'aatuuhunna ujuurahunna fariidhatan", to ga abin da mke faxa anan a xan faxaxe bad a tsayi ba:

Allah Ta'ala yace:

"فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً"
Ma'ana:

"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, wajibi ne ku basu ladan su (Sadaki)".

Abin da kaxai muka ce akan Malam Xabariy shi ne: a cikin Tafsirinsa Al-Kabiir ya fitar, haka nan Malam Zamakhshari cikin litttafin sa Kashshaaf, sannan Malam Raaziy a Tafsirinsa, sai Sharhin Muslim na Nawawiy a farkon Babinsa na auren Mutu'a cewar: Ubayyu xan Ka'abu, da Ibn Abbas, da Sa'iid xan Jubair, da Ibn Mas'uud da Saddiy suna karanta wannan Aya ne da:

"فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"

Su suna qara kenan:
"إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"
Ma'ana:

"Izuwa qayyadajjen lokaci"

Sannan waxannan Malamai dukkanin sun qarfafa cewar wannan Ayar ta sauka ne akan Mutu'a: Malam Ahmad bn Hanbali a Musnadinsa, hakanan ma Malam Abubakar Al-Jassas cikin Al-Ahkamul-Qur'an, da Malam Abubakar Al-Baihaqiy cikin Sunanul-Kubra, da Malam Al-Qaadiy Al-Baidaawiy a Tafsirinsa, da Malam Ibn Kathiir a nasa Tafsirin, da Malam Jalaaluddin Suyuuxiy a Durrul-Manthur, da Malam Al-Qaadiy Ashshaukaniy a Tafsirinsa, da Malam Shihaabuddin Aluusiy a Tafsirinsa, da Sanaduddukan da suke qarewa da irin su Ibn Abbas, da Ubayyu xan Ka'abu, da Abdullahi xan Mas'ud, da Imrana xan Hasiinu, da Habibu xan Abi Thaabit, da Sa'idu xan Jubair, da Qutaadatah, da Mujahid.

Don haka a rubutunmu babu inda muka kawo Xabari akan yana daga cikin masu qarfafawa akan ta sauka ne akan auren mutu'a, don haka Ammar sai a sake wata yaudarar.

Bazai iya yiwuwa ace an fassara wannan Aya da cewa tana Magana ne akan auren Da'imi ba, kamar yadda mai Tafsirul-Manar ya qarfafa. Dalilin kuwa da yasa hakan bazai yiwu ba shine, zuwan waxannan dalilai:

1-      Abinda ya gabata na daga wani adadin Sahabbai dake karanta wannan Aya da:

"فما استمتعتم به منهن - إلى أجل مسمى - فآتوهن أجورهن فريضة"
Ma'ana:

"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, izuwa wani qayyadajjen lokacin da aka ayyana, wajibi ne ku basu ladan su (Sadakin su)".

Tare da gwamin jumla mai yin bayani qarara a tsakiya wato:

"إلى أجل مسمى"

"Zuwa wani qayyadajjen lokaci" 

Wanda buqatar su akanta shine bayyana ma'ana da bigire da fassarar ta. Sannnan wannan jumla bayyananna ba zata tava dacewa da auren Da'imi ba face Mutu'a.

2-      haqiqa lafazin "Mutu'a" koda ya kasance dai-dai ko ingantacce akan amfani ko nufin ma'anar auren Da'imi, to amma yafi fitowa valo-valo a sarari akan nufin auren Mutu'a ne. kamar yadda lafazin "Nikaah" koda ya zamanto dai-dai da inganci wajen amfani ko nufin auren Mutu'a, to abinda shima yake valo-valo a sarari shine ana nufin kai tsaye auren Da'imi ne. wanda idan da babu wata alama a sarari, to da bazai yiwu a yarda akan tana nufin auren Mutu'a bane. A sannan sai ya zamo wani lafazi ne dake iya karvar sama da ma'ana guda xaya kenan.

3-      Haqiqa Ayar mutu'a tazo ne cikin Suratun-Nisaa' wacce ta fara da ambaton "An-Nikaah" wato aure da auren Da'imi, da hukuncinsa a cikin Ayoyi na 3, da 4, da 20, da na 23. Idan har ya kasance abinda ake nufi da "Al-Mutu'atu" shine auren Da'imi har wala iyau to da wannan Aya ta zamo maimaici na neman ambaton abinda ya gabata cikin Surar.

4-      Da kuma "Al-Mutu'atu" ta zamo da ma'anar aure ne na Da'imi, to ina amfanin quduri da "An-nuskhu" (wato an shafe ta) kenan? Ko kuwa suna nufin "Nuskhu" da an shafe hukuncin auren Da'imi ne?! To don haka Magana akan "An-Nuskhu" cewar an shafe hukuncin auren zai zamo wani qarfafane akan Ayar Mutu'a, cewar tana nufin Aure ne "Al-mu'aqqit" ai abin yiwa lokaci (Mutu'a) bawai Da'imi ba wato auren mutu-ka-raba.

Amma Magana akan "An-nuskhu" na sha faxa muku ba'ayin Nuskhi a bayan wafatin Annabi (S), domin Wahayi ne dai yake sauka ace an shafe kaza da kaza, to kuwa tun da Annabi ya yi wafati ba'a sake yin Wahayin da za'a isar da saqon Allah ga wasu ba. Su kuwa dukkanin Nuskhu xin nan da yake zuwa a cikin litattafanku na Hadisai, Sahabban suna ruwaitowa akan sun kasance tare da wannan Aya ne ko Qiraa'a tun a zamanin Manzon Allah (S), yanzu kuma bayan wafatinsa sunga babu ita, to waye ya gayawa su su Xabarin an shafeta, wallahi sai dai idan Shaixan ne ya yi musu Wahayi!

Don haka daga qarshe nake rufewa da tunatarwa akan waxannan ingantattun Hadisai daga manyan litattafan Sunna da suke daxa tabbatar da halascin auren mutu'a da babu wata hujja ta nassi ko ta sharhi ko hankali da za ta iya tashin waxannan ingantattu da tabbatattun Hadisai.

1-      ….. Daga Jabir, yace: "Mun kasance muna auren Mutu'a, a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), da zamanin Abubakar, sannan daga baya Umar xan Haxxabi ya hana ….. (Sahihul-Muslim: 4/131, Musnad na Ahmad: 6/405, Fat-hul-Bari: 9/149).
2-      ….. Daga Ibn Abbas: Haqiqa Ayar Mutu'a hukuntacciya ce ba shafaffiya ba. (Al-Kasshaf: 1/498, Al-Ghadir: 6, Al-Khazin: 1/358).
3-      ….. Munyi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) da zamanin Abubakar da rabin zamanin Umar xan Haxxabi sannan daga baya Umar xan Haxxabi ya hana mutane yi. (Bidayatul-Mujtahidi: 2/58, da Al-Ghadir: 6/223 da 207).
4-      ….. Daga Al-Hakim, da Ibn Juraih da wasunsu, sunce: Aliyyu yace: da ba don Umar xan Haxxabi ya hana yin auren Mutu'a ba da babu wanda zai yi zina sai "Shaqiyy" wato ma'ana sai "Qalil" wato mutane kaxan, a wata fassarar kuma akace sai dai Xan iska, amma waccen fassarar ta "kaxan" tafi qarfi. (Tafsirux-Xabari: 5/9, da Tafsirur-Razi: 10/50, da Durrul-Manthur: 2/140).
5-      ….. Daga Imran xan Hasinu, yace: An saukar da ayar Mutu'a cikin littafin Allah Ta'ala, sannan wata Ayar bata sauka mai shafe ta ba, kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) yayi mana umarni da yin auren Mutu'a, kuma munyi Mutu'a tare da manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), sannnan ya Rasu bai hana mu aikata ta ba, sannan wani mutum ya faxi abin da ya so na ra'ayin sa. (Sahihul-Bukhari: 2/168 da 6/33, Sahihul-Muslim: 4/48, Sunanin-Nisa'i: 5/155, da Musnadin Ahmad: 4/426, abisa ingantaccen Sanadi).
6-      ….. Daga qarshe Ibn Juraih shi kaxai ya ruwaito Hadisai goma sha xaya akan halascin auren Mutu'a. (Nailul-Auxar: 6/271, Fat-hul-Bari: 9/150).

Hadisai da Nassosi suna tabbatar da abinda Ayoyi masu Girma suka nuna ne na halascin auren Mutu'a da dawwamamman hukuncin sa har zuwa tashin Al-qiyama. Domin kuwa haramcin ya samu ne daga Umar xan Haxxabi - bawai daga manzon Girma ba (Sallallahu alaiHi wa Alihi). A irin vangare na Makarantar Sunna zai iya yiwuwa ace sun bi hani ko umarni na Halifa Umar a wannan bigire da yayi hani akan auren Mutu'a, da ace ba a sami Aya ko Hadisi da yake umarni akan halascin sa ba. Amma samuwar Aya da Hadisai barkatai sun yanke musu hanzarin riqo da wannan hani na sa, domin kuwa karo ne da Qur'ani da Hadisin wanda shine mai isar da wannan saqo na Musulunci, wato Annabi Muammad (Sallallahu alaiHi wa Alihi). Don kuwa haqiqa wasu tarin Mutane daga Sahabbai da Tabi'ai kai har ma da Abdullahi xan Umar, da Halifa Umar xan Haxxabin kansa sun ci gaba akan halascin auren Mutu'ar ba haramcin sa ba.

Sannan a vari xaya kuma dukkanin Mabiya Mazhabin Shii'ah sun tafi akan halascin ba haramcin Umar xin ba!!!

No comments:

Post a Comment