Tuesday, 16 July 2013

HUDUBAR MANZON ALLAH (S.A.W.A) Akan Watan Ramadan

DAGA SAIFULLAH M. KABIR

Bislmillahir Rahmanir Rahim
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ahli Muhammad
Sheik as-Sudduk (Allah ya kara masa rahma) ya fitar a cikin littafinsa mai suna “Uyun al-akhbar ar-Ridha (a.s)” da isnadinsa da ya kare da Amirul-mu’uminin Ali bin Abi Dalib (a.s) ya ce:

Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi mana huduba a wata rana (a watan Ramadan), inda yake cewa:

“Ya ku mutane! Lallai hakika watan Allah mai albarka ya zo muku (tattare) da rahama da gafara. Watan da shi ne mafificin dukkan watanni a wajen Allah, ranakunsa kuma su ne mafifitan raneku, sa’o’insa kuma sune mafifitan sa’o’i.

Shi wata ne da aka kira ku zuwa bakuncin Allah a cikin shi, aka kuma sanya ku cikin ma’abota karimcin Allah a cikin shi. Numfashinku a cikin shi ibada ne, haka ayyukanku a cikin shi karbabbu ne, kuma addu’o’inku a cikin shi abin amsawa ne; don haka ku roki Allah Ubangijinku da gasgatattun niyyoyi da tsarkakan zuciya kan cewa Ya sa ku sami dacewa da azumtar sa (watan) da karatun littafinSa (Allah), domin lallai tababbe (na hakika) shi ne wanda ya rasa gafarar Allah a wannan wata mai girma.

Ku tuna da kishirwar lahira ta hanyar yunwa da kishirwanku a cikinshi. Kuyi sadaka ga matalautanku da miskinanku, ku girmama dattawanku, kuma ku tausayawa kanananku, ku kuma sadar da zumuninku. Ku kame harsunanku kuma ku kau da kai daga abubuwan da ba ya halatta idanuwanku su kalla da abubuwan da ba ya halatta kunnuwanku su ji.

Ku tausayawa marayun mutane, ku ma sai a tausaya marayunku. Ku tuba zuwa ga Allah daga zunubanku, ku daga hannuwanku zuwa gare Shi da addu’a a lokutan sallolinku, domin (lokutan sallolin) ne mafifitan lokutan da Allah Madaukaki ke kallon bayinSa da rahama a cikin su, Ya ke sauraron su idan suka gana da shi, Ya kuma amsa musu idan suka roke Shi.

Ya ku mutane! Lallai numfashinku jingina ne ga ayyukanku, don haka ku fitar da su (numfashin) da istigfarinku. Haka bayayyakinku sun nauyaya da ayyukanku, to ku sassauta musu da tsawaita sujjadunku. Ku sani cewa Allah Madaukaki Ya rantse da daukakarSa cewa ba zai azabtar da masu sallah da masu sujjada ba. Kuma ba zai raunana su da wuta a ranar da mutane za su tsaya gaban (Allah) Ubangijin talikai ba.

Ya ku mutane! Wanda ya bude bakin mai azumi mumini a wannan wata, to da hakan yana da ladan (wanda) ya ‘yanta bawa a wajen Allah da gafararta abin da ya gabata na zunubbansa”.

Sai aka ce ya Manzon Allah, ba kowannen mu ne zai iya haka ba. Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce:

“Ku kaucewa wuta ko da da tsagin dabino ne! ku kaucewa wuta ko dad a kurbin ruwa ne!!”

“Ya ku mutane! Wanda ya kyautata halayyarsa a wannan wata zai ketare siradi a ranar da kafafu ke zamewa; kuma wanda ya sassauta ga wadanda ya mallaka Allah Zai saukaka masa hisabinsa; kuma wanda ya kame sharrinsa a cikin shi (wannan wata) Allah Zai kame fushinSa daga gare shi a ranar da zai hadu da Shi, kuma wanda ya kyautatawa maraya a cikin shi Allah zai karrama shi a ranar haduwar su. Haka wanda ya sadar da zumuncinsa a cikin shi Allah zai sadar da rahmarSa gare shi a ranar haduwar su; wanda kuwa ya yanke zumuncinsa Allah zai yanke rahmarSa gare shi ranar da zai hadu da shi.

Wanda ya yi nafilar salla a cikin shi Allah Zai rubuta mishi barranta daga wuta. Wanda ya sauke nauyin farilla a cikin shi kuwa yana da ladan wanda ya sauke nauyin farillai saba’in a wasu watannin da ba shi (Ramadan) din ba; wanda ya yawaita yi mini sati a cikin shi Allah zai nauyaya mishi ma’aunin ayyukansa a ranar da ma’aunan ayyuka ba su da nauyi; wanda ya yi tilawar aya daya daga al-Kur’ani kuwa yana da ladan wanda ya sauke al-Kur’ani a wani wata da ba shi ba.

Ya ku mutane! Lallai an bude kofofin Aljanna, don haka ku roki Ubangijinku da kar Ya rufe su gare ku; kuma an rufe kofofin wuta, to ku roki Ubangijin ku kar ya bude su gare ku; haka an daure shedanu, don haka ku roki Allah kar su sami iko a kan ku.”

Sai Amirul-Muminin Ali (a.s) ya mike ya ce: “Ya Manzon Allah, mene ne mafifiin ayyuka a wannan wata?”

Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya amsa masa da cewa: “Ya kai Baban Hasan! mafificin ayyuka a wannan wata shi ne tsentseni (kame kai) daga abubuwan da Allah Ya haramta.”

ALLAH YA SA MUNA CIKIN WADANDA ALLAH KE GAFARTAMA A WANNAN WATAN

No comments:

Post a Comment