Tuesday, 16 July 2013

TARIHIN IMAM KHUMAINI {R.A}

 
 
 
IMAM KHUMAINI (R.A) DAGA HAIHUWA ZUWA WAFATI

A ranar ashirin ga watan Jimada al-Thani 1320 hijira Kamariyya, wadda ta yi daidai da 30 ga watan Shahribar 1281 hijira shamsiyya (24 ga Satumba 1902 miladiyya) aka haifi wani jariri a garin Khumain, wani gari da ke lardin tsakiyana Iran. Iyayensa dai mutane ne masu tsoron Allah, masana ilmummukan Musulunci wadanda kuma suka fito daga zuriyar Nana Fatima al-Zahra (a.s) inda suka sanya masa suna Ruhullah al-Musawi al-Khumaini.

Shi dai wannan yaro ya gaji iyaye da kakanninsa ne wadanda daya bayan dayansu suka dauki nauyin aikin shiryar da mutane da kuma neman ilmi. Mahaifi marigayi Imam Khumaini (r.a) shi ne Marigayi Ayatullah Sayyid Mustafa Musawi, daya daga cikin malaman da suka yi zamani da Ayatullah al-Uzma Mirza Shirazi (r.a). (A bisa al'ada) mahaifin Imam Khumaini ya tafi birnin Najaf na kasar Iraki don karatun addini inda bayan ya kai matsayin ijtihadi (matsayin iya ciro hukumce-hukumcen shari'a daga mabubbuga) sai ya dawo gida wato garin Khumain ya ci gaba da shiryar da mutane a can. A lokacin Imam yana shekara biyar mahaifinsa ya yi shahada sakamakon harin da aka kai masa a hanyarsa ta zuwa garin Arak saboda irin nuna rashin amicewar da yake yi da zaluncin mahukunta na wancan lokacin. Bayan wannan kisan gilla, danginsa da mutanen garin Khumain sun fito don nuna rashin amincewarsu, bayan haka kuma suka wuce zuwa birnin Tehran don isar da kukansu da bukatan da a zartar da hukumci (kisasi) a kan wadanda suka aikata danyen aikin. Wannan kisan gilla da aka yi wa mahaifinsa ya sanya Imam (r.a) tun yana karami ya fahimci dacin maraici da kuma ma'anar shahada. Don haka mahaifiyarsa (Banu Hajar) ita ce ta ci gaba da kula da kuma tarbiyantar da shi, kasantuwar ita ma ta fito ne daga madaukakin gida don kuwa ita jika ce wa Ayatullah Khunsari (marubucin littafin Zubdatul Tasanif) da kuma goggonsa (Sahiba Khanum). To sai dai lokacin da Imam ya kai shekaru 15 a duniya ya rasa irin wannan kulawa lokacin da wadannan masu kulawa da shi suka rasu.



HIJIRA ZUWA KUM, DON KAMMALA KARATU DA KARANTAR DA ILIMIN MUSULUNCI



Jin kadan bayan hijirar Ayatullah al-Uzma Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri Yazdi, Allah Yayi masa rahama, zuwa birnin Kum a farkon shekara ta 1300 hijira shamsiyya (Rajab 1340), Imam Khumaini shi ma ya yi hijira zuwa makarantar Hawza ta Kum don ci gaba da karatunsa a wajen manyan malaman garin. Karatun dai ya hada da karasa karatun littafin Mutawwal wajen Mirza Muhammad Ali Adib Tehrani, da kuma karasa darasin "Sutuh" wajen Ayatullah Sayyid Muhammad Taki Khunsari da Ayatullah Sayyid Ali Yathrebi Kashani; da kuma fikihu wajen shugaban makarantar Hauzar Kum Ayatullah Sheikh Abdulkarin Ha'iri Yazdi (r.a).

Bayan rasuwar Ayatullah al-Uzma Ha'iri Yazdi, a bisa bukata da matsin lamban Imam Khumaini da wasu manyan malamai na makarantar hauzar Kum, Ayatullah Burujerdi ya dawo birnin Kum don ci gaba da kula da makarantun Hawzan garin a matsayin shugaba. A daidai wannan lokaci kuwa ana ganin Imam Khumainin a matsayin daya daga cikin manyan malaman da ake iya komawa gare su a bangaren fikihu, Usul, falsafa, irfani da akhlak.

Shekara da shekaru, Imam Khumaini ya yi yana karantar fa fikihu, Usul, sufanci da akhlak a makarantun Hawza na Kum da suka hada da Makarantar Fa'iziyya, Masjid al-A'azam, Masjid Muhammadiye, Makarantar Hajj Mullah Sadik da kuma Masallacin Salmusi da dai sauransu. Har ila yau ya kuma karantar da fikihu da sauran ilmummukan Ahlulbaiti (a.s) a masallacin Shaikh al-Ansari (r.a) da ke Najaf na tsawon shekaru 14, inda a nan ne a karon farko ya bayyanar da ra'ayin gwamnatin Musulunci cikin silsilar darussan da yake bayarwa na Wilayatul Fakih.



IMAM KHUMAINI (R.A) A FAGEN GWAGWARMAYA



Ruhin jihadi da gwagwarmaya a tafarkin Allah yana da tushe na akida da tarbiyya da kuma ta zamantakewa da siyasa duk tsawon rayuwar Imam Khumaini. Imam ya fara gwagwarmayarsa ne tun lokacin samartaka, kuma ya ci gaba da hakan a bangarori daban-daban na kyautata ruhi a bangare guda, a bangare guda kuma kan yanayi na siyasa da zamantakewar al'ummar Iran da sauran al'ummomin kasashen musulmi. Rikicin da ya faru a shekarun 1340-1341 hijira shamsiyya (1961-1962) kan (zaben) kananan hukumomi ya kasance babbar dama ga Imam wajen jagorantar yunkurin al’umma. Don haka, ana iya cewa, yunkurin gama-gari na malamai da al'ummar Iran na 15 ga watan Khordad 1342 (5 Yunin 1963) ya kebantu da wasu siffofi guda biyu su ne kuwa jagorancin Imam Khumaini da kuma riko da Musulunci, wanda hakan ya zamanto matakin farko na yunkurin al'ummar Iran wanda daga baya aka fi saninsa da sunan "Juyin Juya Halin Musulunci".

Yayin da yake bayani kan abubuwan da ya tuna dangane da yakin duniya na farko, duk da cewa lokacin da aka yi yakin yana da shekaru 12 ne a duniya, Imam Khumaini yana cewa: "Lalle ina iya tuna abubuwan da suka faru a yakukuwan duniya guda biyu…a lokacin ina karami ne amma dai na kan je makaranta kuma ina ganin sojojin tarayyar Sobiyeti a sansanin da muke da shi a nan (garin) Khumain. A yakin duniya na farko a wasu lokuta akan kai mana hare-hare ma". A wani waje na daban Imam Khumaini ya kasance ya kan ambato sunayen wasu daga cikin ashararan da suke fakewa da hukuma wajen kai hare-hare da sace kayayyakin al'umma, inda yake cewa: "Tun ina karami nake cikin yaki….muna cikin mamayan Zulkawa da kai hare-haren Rajab'ali ne duk da cewa mu ma muna da bindiga. Mu kan je kai dauki alhali a lokacin ina cikin shekarun samartaka na ne. Mun kasance mu kan gina ramukan fakewa a inda muke… mu kan shiga cikin wadannan ramuka muna fada da wadannan ashararai da suke son kawo hari da mamaye mu".

A bisa wasu hujjoji na tarihi an tabbatar da cewa gwamnatin Birtaniyya ne ta shirya da kuma goyon bayan juyin mulkin da Ridha Khan ya yi a ranar 3 ga watan Esfand 1299 hijira shamsiyya (1920). Duk da cewa an kawo karshen mulkin Kajariyawa da kuma rage karfin mulkin ha’inai da ashararai, to amma dai ya haifar da wani tsari na kama-karya da wasu ‘yan tsiraru ke mulkan mutanen wata kasa da tsara musu makoma, inda 'yan gidan sarautan Pahlawi suka maye gurbin ashararai.

A irin wannan hali nea, duk da irin musgunawa malamai da gwamnatin lokacin da 'yan amshin shatan Birtaniyya da wasu 'yan boko da aka saya suke yi, amma (malaman) sun tsaya kyam wajen kare Musulunci. A wannan lokaci, bisa gayyatar da malaman Kum suka yi masa, Ayatullah Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri ya yi hijira daga garin Arak zuwa Kum. Bayan wani lokaci kuma sai Imam Khumaini, sakamakon irin kokarin da yake da shi da kuma gama karatunsa na share fage a garuruwan Arak da Khumain, yayi hijira zuwa birnin Kum don ba da tasa gudummawar wajen karfafa sabuwar makarantar Hawzar garin. Daga baya ya yi fice wajen karantar da ilmummukan fikihu, falsafa da sufanci.

Rasuwar Ayatullah Ha'iri a ranar 10 ga Bahman 1315 hijira shamsiyya (10 ga watan Janairun 1937) ta sanya makarantar Hawzar Kum cikin hatsarin rugujewa, sai dai wasu malamai masu sadaukarwa sun ba da ta su gudummawar wajen ganin hakan ba ta faru ba. Cikin shekaru takwas din da aka yi, kula da makarantar ta kasance ne karkashin kulawar manyan malamai irinsu Ayatullah Sayyid Muhammad Hujjat, Sayyid Sadraddin Sadr da Sayyid Muhammad Taki Khunsari. A daidai wannan lokaci, musamman bayan faduwar gwamnatin Ridha Khan, yanayi yayi kyau da ya ba da dama wajen sake samar da cibiyar marja'iyya. A lokacin babu wanda ya dace ya maye gurbin Ayatullah Ha'iri da kuma kare makarantar Hawza daga faduwa kamar Ayatullah Burujerdi. Wannan hukumci na nada Ayatullah Burujerdi ya samu goyon bayan daliban Ayatullah Ha'iri ciki kuwa har da Imam Khumaini. A daidai wannan lokaci Imam da kansa ya yi ta kokari wajen ganin Ayatullah Burujerdi ya dawo garin Kum don rike shugabancin makarantar garin.

Imam Khumaini, sanadiyyar irin sanya ido kan yanayin da al'umma da makarantar Hawzar take ciki, da kuma karance-karance litattafa, jaridu da mujallu da kuma ziyarar da yake kai wa Tehran da ganawa da manyan malamai irin su Ayatullah Mudarris, ya fahimci cewa hanya guda ta magance mummunan yanayin da ake ciki bayan rashin nasarar yunkurin tsarin mulki musamman bayan darewar mulkin Ridha Khan ita ce taka tsantsan din makarantar Hawza, da tabbatar da alaka ta ruhi tsakanin malamai da al'umma.

A wannan kokari da Imam yake yi na karfafa makarantar Hawza ne ya sa a shekarar 1328 (1949) bisa goyon bayan Ayatullah Murtadha Ha'iri suka tsara wani shiri na kawo canji inda suka gabatar da shi ga Ayatullah Burujerdi. Wannan shiri ya fuskanci amincewar daliban Imam da sauran daliban da suke da wayewa.

Sai dai ita gwamnatin ta yi kuskure, saboda a ranar 16 Mehr 1341 (8 ga Oktoba 1962) majalisar hukumar Asadullah Alam ta amince da cire wasu dokokin karamar majalisar kasa, kamar dokar da ta shardanta cewa dole ne dan takara ya zamanto musulmi, rantsuwa da Alkur'ani mai girma, sharadin mazantaka ga 'yan takara da masu jefa kuri'a. Babu makawa akwai wata boyayyiyar manufa cikin amincewa da barin mata su kada kuri'a (da hukumar ta yi), kamar yadda cire sharadin Musulunci da mazantaka shi ma da wata manufa aka yi shi, ita ce kuwa shigar da 'yan Baha'iyya cikin al'amurran gudanarwa da ba su manyan mukamai cikin gwamnati.

Kamar yadda muka nuna a baya, taimako da goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila da fadada alakar Iran da ita na daga cikin sharuddan da Amurka ta kafa wa gwamnatin Shah matukar tana son goyon bayanta. Don haka ne ya zamanto dole a bar 'yan kungiyar Baha'iyya ta 'yan mulkin mallaka su kame manyan bangarorin gwamnati don cika wannan sharadi. Jin kadan bayan watsa wannan labari, Imam Khumaini da wasu manyan malaman biranen Kum da Tehran, bayan wata tattaunawa, suka sanar da rashin amincewarsu da dokar.

Imam Khumaini ya ba da gagarumar gudummawa wajen fallasa asiri da manufofin gwamnatin Shah da kuma bayyana hakikanin nauyin da ya hau kan malamai da makarantun Hawza cikin halin da ake ciki. Hakan ne ya sa aka samu wasu malamai suka aike da wasu wasiku na nuna rashin amincewa ga Shah da priminista Alam, hakan ya faranta wa al'umma rai. Amma wasikun da Imam ya aike wa Shah da priministansa sun fi na sauran malaman tsauri da kuma jan kunne. A cikin daya daga cikin irin wadannan wasiku, Imam yana cewa: "Ina sake muku nasiha da tsoron Allah da kuma bin tsarin mulki, sannan ku guji saba wa Alkur'ani da dokokin malamai da shuwagabannin musulmi da kuma watsi da dokokin kasa; kada ku sanya kasa cikin hatsari da gangan, idan kuwa ba haka ba, malaman Musulunci ba za su daina yin maganganu a kanku ba".

Haka dai wannan batu na dokar kananan hukumomi ya kasance nasara ga al'umma kana kuma lamari mai muhimmanci gare su, musamman ma ganin cewa sun fahimci siffofin mutumin da ya cancanci ya jagoranci al'ummar musulmi. Duk da wannan rashin nasara da Shah ya fuskanta, to amma Amurka ta ci gaba da matsa masa lamba wajen ci gaba da canje-canjen da zai ba ta damar cimma manufofinta. Don haka Shah a watan Dey 1341 (Janairun 1962) ya gabatar da jiga-jigan shirinsa na canji guda shida da kuma bukatar a gudanar da jin ra'ayin al'umma kansu.

Har ila yau Imam Khumaini ya sake bukatar maraja'ai da manyan malaman garin Kum da su zauna don tattaunawa kan halin da ake ciki da kuma yiyuwar sake kaddamar da wani sabon yunkuri.

A ci gaba da goyon bayan da mutane suke nuna wa Imam, al'umma sun kaurace wa bukukuwan "Nuruz" (sabuwar shekara) don nuna rashin amincewa da ayyukan gwamnati. A cikin sanarwar da Imam ya fitar kan hakan, ya ambaci "Farin Yunkuri" (White Rebolution) na Shah da sunan "Bakin Yunkuri" (Black Rebolution), sannan kuma ya tona asirin manufar Shah ta biyan bukatun Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila. A bangare guda kuma, Shah, wanda ya tabbatar wa Amurkawa cewa al'ummar Iran sun amince da canje-canjen da yake son yi don cimma manufofin Amurka da ya ba shi sunan "White Rebolution", ya fahimci cewa rashin amincewar da malamai suke yi gare shi zai haifar masa da matsaloli masu girman gaske.

A cikin hudubobi da jawaban da ya dinga yi a gaban jama'a, Imam Khumaini ya dora alhakin wannan zalunci a kan Shah, kamar yadda kuma yake kiransa da dan koran haramtacciyar kasar Isra'ila da kiran al'umma da su yi masa bore. A wani jawabi da ya gabatar a ranar 12 ga Farbardin 1342 (1 Aprilu 1963) Imam ya yi Allah wadai da shirun da malamai suka yi a garuruwan Kum, Najaf da sauran garuruwan musulmi kan wannan danyen aiki na gwamnatin Shah, yana mai cewa: "Lalle a yau shiru yana nufin nuna goyon baya ga wannan hukuma ta zalunci". Washegari kuma wato ranar 13 ga Farbardin 1342 (2 Aprilu 1963) Imam ya fitar da sananniyar sanarwar nan tasa mai suna "Kaunar Shah Wasoso Ne".

Haka nan idan ana son fahimtar irin tasirin da kalaman Imam suke da shi a zukatan masu sauraronsa da har suke iya fita su ba da rayukansu, to dole ne a dubi asali da kiran nasa yake da shi da kuma irin gaskiya ta hakika da ke tare shi.

Shekarar 1342 hijira shamsiyya (1963) ta fara ne da kin fitowar da al'umma suka yi don bukukuwan "Nurooz" (sabuwar shekara) sakamakon kiran da malamai suka yi, da kuma zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba a makarantar Fa'iziyya da ke birnin Kum. A bangare guda, Shah ya dage sai ya aiwatar da shirinsa na kawo canjin da Amurka ta ke bukata, a bangare guda kuma Imam Khumaini ya dage wajen wayar da kan al'umma wajen tsayawa da fuskantar tsoma bakin Amurka cikin al'amurran cikin gidan Iran da kuma ha'incin Shah.

A ranar 14 ga watan Farbardin 1342 (1963), Ayatullah al-Uzma Hakim daga garin Najaf ya aike wa wasu manyan malamai da maraja'ai na Iran da wasika yana kiransu da yin hijira ta gaba daya zuwa garin Najaf. Wannan kira dai an yi ta ne da nufin kiyaye rayuwar malamai da makarantar Hawza.

Imam ya yi kunnen uwar shegu da wannan barazana, don haka sai ya aikewa Ayatullah Hakim amsar wasikar da ya rubuto yana mai ce masa yana ganin babu wata maslaha ta Musulunci cikin yin hijira ta gaba daya da barin Hawzar Kum haka nan.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 12 ga watan Farbardin 1342 (22 Aprilu 1963) a lokacin bukukuwan kwanaki arba'in na shahadar (daliban) Fa'iziyya, Imam Khumaini ya jaddada goyon bayan malamai da al'ummar Iran ga jagororin kasashen musulmi da na larabawa wajen fuskantar haramtacciyar kasar Isra'ila, kamar yadda kuma yayi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sarki Muhammad Ridha Pahlawi da haramtacciyar kasar Isra'ila.



YUNKURIN 15 GA KHORDAD (5 GA YUNI):

Watan Muharram na shekarar 1342 yayi daidai da watan Khordad ne (Yunin 1963) don haka Imam Khumaini ya yi amfani da wannan dama wajen motsa mutane da fuskantar hukumar kama-karya ta Shah.

A yammacin ranar Ashuran ta shekara ta 1383 hijiriyya (3 ga Yunin 1963) Imam ya gabatar da wani jawabi mai cike da tarihi a makarantar Fa'iziyya wanda shi ne matakin farko na yunkurinsa na 15 ga watan Khordad (5 Yuni).

A cikin wannan jawabi, yayin da yake magana da Shah, Imam yana cewa: "Ya Shah ina maka nasiha! Ya kai mai girma Shah, ina maka nasiha da ka janye hannayenka daga wadannan ayyuka naka! Suna yaudarar ka ne. Ba na son in ga mutane suna cikin farin ciki da murna idan har suka yi waje da kai..ina kiranka da ka yi tunani kan abin da suke sa ka fadi…ka saurari nasihata. Mece ce alakar da ke tsakanin Shah da (haramtacciyar kasar) Isra'ila da har 'yan SABAK (jami'an tsaron Shah) suke cewa kada ku fadi magana kan Isra'ila? Shin Shah Ba'isra'ile ne?". Shah dai ya ba da umarnin gamawa da wannan yunkuri. Da farko jami'an tsaro sun kame da dama daga cikin magoya bayan Imam a daren 14 ga Khordad (4 ga Yuni), kusan asubahin washe gari kuwa da misalin karfe 3 na asuba darurrukan 'yan sandan da aka aiko daga Tehran sun kewaye gidan Imam da nufin kama shi a lokacin yana sallar dare. Don haka bayan kama shi sai suka wuce da shi cikin gaggawa zuwa Tehran inda suka fara tsare shi a wajen tsare mutane na 'Officer's Club' daga baya kuma da yamma suka wuce da shi zuwa gidan yarin Kasr na birnin. Da safiyar 15 ga watan Khordad labarin kama Imam ya yadu zuwa garuruwan Tehran, Mashhad, Shiraz da sauran garuruwa lamarin da ya sa aka samu irin yanayin da aka samu a garin Kum na boren jama’a. A cikin littafin da ya rubuta abubuwan da suka faru a rayuwarsa, wani na kurkusa da Shah Janar Fardoust ya bayyana yadda aka zabi jami'an tsaro na musamman bisa taimakon Amurka don kawo karshen wannan yunkuri, sannan kuma yayi bayani kan irin halin damuwa da dar-dar din da Shah, ministoci da jami'an gwamnatinsa, janar-janar da sojinsa da kuma 'yan SABAK suka kasance ciki a wancan lokacin, da kuma yadda Shah da jami'ansa suka ta ba da umarni ba kan gado don kawo karshen boren da jama'a suke yi. Bayan kwanaki 19 a gidan yarin Kasr, hukuma ta dauke Imam daga inda ake tsare da shi zuwa gidan yarin da ke barikin soji na Eshrat Abad.

Ana iya cewa ya zuwa wani haddi an cutar da wannan yunkuri sakamakon kama jagoransa da aka yi a ranar 15 ga Khordad da kuma kisan kiyashin da aka yi wa magoya bayansa. Shi kuwa Imam ya ki ba da hadin kai da amsa tambayoyin masu masa tambayoyi a inda ake tsare da shi yana mai nuna cewa ba sa da hurumin yi masa tambayoyi. Don haka a yammacin 18 ga watan Farbardin 1343 (1964) ba tare da wata sanarwa ba sai gwamnatin ta sake Imam da daukansa zuwa Kum. Jin wannan labari ke da wuya sai dukkan garin ya cika da bukukuwa da farin ciki, aka ci gaba da shirya bukukuwa a makarantar Fa'iziyya da sauran gurare har na tsawon ranaku. An gudanar da bukin shekarar farko ta tunawa da abin da ya faru a ranar 15 ga watan Khordad a shekarar 1343 da wasu bayanan hadin gwuiwa da Imam Khumaini da sauran maraja'ai suka fitar, da kuma wani bayanin na daban da makarantar Hawza ta fitar don girmama wannan rana da sanya mata sunan ranar zaman makomi ta gaba daya.

A wannan rana (ta 4 ga Aban), Imam Khumaini ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa: "Ya kamata al'ummar duniya ta san cewa dukkan wata wahala da matsalolin da al'ummar Iran da na musulmi suke ciki daga Amurka ne, daga baki 'yan kasashen waje ne. Al'ummar musulmi dai ba sa kaunar dukkan bakin haure musamman ma Amurka. Don kuwa Amurka ce take goyon bayan (haramtacciyar kasar) Isra'ila da kawayenta. Amurka ce ta karfafa (haramtacciyar kasar) Isra'ila don mayar da musulmi marasa matsuguni..".

Nuna rashin amincewar Imam ga wannan dokar (ba da kariya ga ‘yan kasar Amurka a Iran) ta sake sanya Iran cikin yanayi na sabon bore da yunkuri a watan Aban 1343 (1964). Da asussubahin ranar 13 ga watan Aban 1343 (1964), jami'an tsaro na musamman da aka turo daga Tehran sun sake mamaye gidan Imam dake garin Kum, inda suka sake kama shi, kamar yadda ya kasance a shekarar da ta gabata, alhali yana cikin salla da addu'oi, suka wuce da shi kai tsaye zuwa filin jirgin saman Mehr Abad da ke Tehran da sanya shi cikin wani jirgin saman soji da daman yake jira sai garin Ankara na kasar Turkiyya. Da hantsin wannan rana, jami'an tsaron SABAK, cikin jaridun kasar, sun sanar da koran Imam saboda zargin barazana ga tsaron kasa. Duk da irin halin dar-dar da ake ciki sai da al'ummar birnin Tehran suka fito don yi zanga-zanga a kasuwar birni don nuna rashin amincewarsu da wannan aiki, sannan kuma aka rufe makarantun Hawza na wani tsawon lokaci kana kuma aka aike da wasiku ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma maraja'ai.

Imam ya zauna a Turkiyya ne na tsawon watannin goma sha daya. A daidai wannan lokaci kuwa gwamnatin Shah ta yi kokari wajen ganin ta gama da sauran kurar bore ta hanyar amfani da karfi sannan kuma ta gaggauta kaddamar da shirin nata da Amurka take son ta gabatar. Imam ya yi amfani da zaman gudun hijira ta dole a kasar Turkiyyan wajen rubuta da tsara shahararren littafin nan nasa mai suna 'Tahrir al-Wasila.



KORAR IMAM (R.A) DAGA TURKIYYA ZUWA IRAKI.

A ranar 13 ga watan Mehr 1344 (13 Oktoba 1965) jami'an tsaro sun tura Imam da dansa Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini zuwa gudun hijira ta biyu wato daga Turkiyya zuwa kasar Iraki. Bayan isarsa birnin Bagadaza, Imam Khumaini ya kai ziyara zuwa hubbarorin tsarkakan Imamai (a.s) da suke garuruwan Kazimain, Samarra da Karbala, daga nan kuma bayan mako guda, Imam ya wuce zuwa sabon masaukinsa da ke birnin Najaf mai tsarki.

Shekaru sha ukun da Imam ya yi a garin Najaf (Iraki), duk da cewa babu matsin lamba na kai tsaye kamar yadda ya fuskanta a Iran da Turkiyya, sun fara ne cikin wani irin yanayi na nuna adawa da cutarwa mai tsanani daga wajen wasu malaman jeka na yi ka da ma'abuta son duniya da suka sanya tufafin ma'abuta addini da har ta kai ma, duk da irin hakurin da aka san shi da shi, a wasu lokuta ya kan fito ya yi magana kan irin wahalar jihadi da gwagwarmaya a wancan lokaci. To sai dai hakan ba su sanya ya ja da baya da barin wannan tafarki da ya zaba wa kansa ba.

Don haka ya fara karantar da fikihu a watan Aban 1344 (Nuwamban 1965) a masallacin Sheikh al-Ansari da ke Najaf duk kuwa da irin matsin lamba da adawar da ya dinga fuskanta, haka dai ya ci gaba da karantarwa har lokacin da ya yi hijira zuwa birnin Paris na kasar Faransa. Irin karfin ilmin fikihu da Usul da dai sauran ilmummukan Musulunci da Imam ya ke da shi ya sanya cikin karamin lokaci, duk da irin matsalolin da yake fuskanta, azuzuwansa sun kasance daga cikin mafi shahara da yawan dalibai a makarantun Hawzan Najaf.

Tun isowarsa birnin Najaf, Imam bai katse alakarsa da mujahidan da suke cikin Iran ba, ya kasance ya kan aika musu da sakonni da wasiku yana mai kiransu da su ci gaba da tsayin daka wajen kiyaye manufar wannan yunkuri na 15 ga watan Khordad.

Duk da irin yanayi mai tsanani da wahala da Imam Khumaini ya ke fuskanta a inda yake gudun hijira, to amma hakan ba su sa shi ya bar tafarkinsa na jihadi da fuskantar gwamnatin Shah ba. A kusan ko da yaushe yana ci gaba da sanya ruhin kyakkyawar fata da nasara a zukatan al'umma ta hanyar jawabai da sakonnin da yake aikewa da su ga mutanensa.

A ranar 19 ga watan Mehr, 1347 (9 ga Oktoba 1968) a wata ganawa da ya yi da wakilin kungiyar Fatah mai fafutukan 'yanto kasar Palastinu, Imam Khumaini ya bayyana mahangarsa kan matsalolin da duniyar musulmi ke ciki da kuma yunkurin al'ummar Palastinu. A yayin wannan ganawa, Imam ya ba da fatawar wajibcin kebance wani sashi na zakka da ba da shi ga 'yan gwagwarmayar Palastinu.

A farko-farkon shekarar 1969 rikicin da ke tsakanin gwamnatin Shah da gwamnatin Ba'athawa ta Iraki kan iyakan kasashen biyu na ruwa ya tsananta. Hakan ya sanya gwamnatin Iraki korar adadi mai yawa na Iraniyawa da ke zaune a kasar, kamar yadda kuma gwamnatin ta yi kokarin amfani da irin adawan da Imam yake yi wa gwamnatin Shah don cimma manufarta.

Shekaru hudu na koyarwar Imam da kuma irin kokarin da yake yi wajen wayar da kan mutane ya sanya an samu 'yan canje-canje a makarantun Hawzan birnin Najaf. A shekarar 1348 (1969) wannan yunkuri na Imam ya samu wasu sabbin magoya baya daga kasashen Iraki, Lebanon da sauran kasashen musulmi wadanda suka dauki yunkurin a matsayin abin koyi.



IMAM KHUMAINI DA CI GABAN GWAGWARMAYA (1350-1356 = 1971-77)



A karshe-karshen shekarar 1971, kai ruwa ranan da ke tsakanin gwamnatin Ba'athawa ta Iraki da gwamnatin Shah ya tsananta lamarin da ya yi sanadiyyar korar dubban Iraniyawa da suke zaune a kasar. Nan take Imam ya aike da wasika zuwa shugaban kasar yana yin Allah wadai da wannan aiki sannan kuma ya sanar da aniyarsa ta barin kasar, sai dai hukumar ta hana shi saboda tsoron abin da zai iya biyo baya. A yayin bukukuwan zagayowar shekarar yunkurin 15 ga watan Khordad a shekarar 1975, dalibai a makatantar Fa'iziyya ta Kum sun gudanar da zanga-zangogi na kawanki biyu cikin makarantar suna masu rera taken "Aminci ya tabbata ga Khumaini", "Mutuwa a kan gidan sarautar Pahlawi". Duk da cewa hukuma ta haramta kungiyoyi da jam'iyyu masu adawa da ita sannan kuma da dama daga cikin ma'abuta addini da 'yan siyasa masu jihadi suna tsare a gidahen yari, amma duk da hakan kungiyoyi masu jihadin sun haifar da gagarumar hasara ga hukumar, hakan ne ya sanya jami'an tsaro (SABAK) suka fada wa makarantar da musguna wa dalibai musgunawa mai tsanani da kuma tsare su a gidajen yari.

A ci gaba da ayyukansa na kiyayya da Musulunci, a watan Esfand 1354 (Fabrairun 1975), Shah ya canza kalandar (kwanakin wata) da hukuma take amfani da ita da ta fara daga hijiran Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya zuwa farkon mulkin mulukiyya Hakhamanshiyyawa. Imam Khumaini ya mayar da kakkausar martini ta hanyar fitar da fatawar haramcin amfani da wannan kalanda. Kamar dai yadda al'umma suka karbi fatawar haramcin shiga jam'iyyar Rastakhiz da Imam ya bayar, haka ma a wannan karon suka karbi wannan fatawa da hannu bibbiyu. Dukkan wadannan abubuwa biyu ana ganinsu a matsayin bugun hanci ga Shah. Hakan ya tilasta masa janye wannan sabuwar kalanda tasa a shekarar 1357 (1977).



KAMARIN JUYIN MUSULUNCI DA YUNKURIN AL'UMMA A 1356 (1977)


Imam Khumaini wanda ya kasance mai sanya ido sosai kan abubuwan da ke gudana a Iran da sauran kasashen duniya, ya yi kokarin amfani da duk wata damar da ya samu. A watan Mordad 1356 (Augustan 1977), cikin wani sako da ya aika, ya bayyana cewar: "Bisa la'akari da yanayin cikin gida da waje, da kuma buga irin ayyukan zalunci da hukuma take yi a jaridun kasashen waje, hakan dama ce ga masana, 'yan jami'a da ke karatu a ciki da wajen kasa da kuma kungiyoyin Musulunci a duk inda suke da ya kamata su amfana da ita wajen fuskantar hukuma".

Shahadar Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini a ranar 1 ga watan Aban 1356 (1977) da kuma irin tarurrukan zaman makokin da aka shirya a Iran sun kasance abubuwan da suka sake motsa makatantun Hawza da al'ummar Iran wajen sake fitowa don fuskantar hukuma. Shi kuwa a nasa bangaren, Imam Khumaini ya bayyana wannan lamari (na shahadar Sayyid Mustafa) a matsayin wata boyayyiyar ni'imar Ubangiji, wanda hakan ya zamanto abin ban al'ajabi ainun. Gwamnatin Shah ta yi kokarin cin mutumcin Imam ta hanyar watsa wata makala ta cin mutumci gare shi cikin jaridar Ittila'at. Sai dai wannan karon ma shika ta koma kan mashekiya ne, don kuwa maimakon hakan sai ta kasance ummul aba'isin din boren al'umma a ranar 19 ga watan Dey 1356 (9 ga Janairu 1977) da nuna goyon bayansu ga Imam lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar wasu dalibai ma'abuta jihadi da raunana wasu da dama a lokacin da jami'an tsaro suka fada musu. Duk da irin ayyukan zalunci da wuce gona da iri da gwamnatin Shah take yi a kan 'yan gwagwarmaya, sai dai duk da hakan hukumar ta gagara kashe wutan wannan bore. Imam yana ganin babu wani amfani wajen gwagwarmayar 'yan majalisa, jam'iyyun siyasa da karfin soji ba tare da goyon bayan al'umma ba, kamar yadda kuma yake ganin hanya guda da ta rage ita ce kaddamar da jihadi matukar Amurka ta yi tunanin shirya juyin mulkin soji.



HIJIRAR IMAM DAGA IRAKI ZUWA PARIS
A wata tattaunawa da ta gudana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Iraki a birnin New York na Amurka, ministocin biyu sun yanke shawarar korar Imam Khumaini daga Irakin. Don haka a ranar 2 ga watan Mehr 1357 (24 ga Satumba 1978), jami'an tsaro suka mamaye gidan Imam da ke birnin Najaf mai tsarki, hakan dai ya fusata al'umman musulmi na kasashen Iran, Iraki da sauran kasashen duniya.

Don haka a ranar 12 ga watan Mehr (4 ga Oktoban 1978), Imam Khumaini ya bar birnin Najaf ya nufi kasar Kuwaiti, sai dai kasar Kuwaitin ta ki amincewa ya shigo kasar sakamakon matsin lamban gwamnatin Iran. Ganin haka ya sa wasu suka ba da shawarar a tafi kasar Siriya ko Labanon, to sai dai shi Imam Khumaini bayan shawara da dansa Hujjatul Islam Sayyid Ahmad Khumaini, ya yanke shawarar tafiya birnin Paris na kasar Faransa. Don haka Imam ya isa birnin Paris a ranar 14 ga Mehr 1357 (6 ga Oktoba 1978) inda aka saukar da shi a gidan wani Ba'iraniye a unguwar Noefel Le Chateau da ke wajen birnin.

A can ma mahukunta ba su barshi ba don bayan wani lokaci jami'an kasar Faransan sun zo wajensa da nufin sanar da shi mahangar shugaban kasar na lokacin kan zaman Imam a kasar suna masu sanar da shi cewa dole ne ya janye hannayensa daga harkokin siyasa. Imam Khumaini ya mayar da kakkausar martini ga wannan bukata ta su yana mai cewa hakan ya saba wa ikirarin riko da tsarin demokradiyyar da Faransan take yi, yana mai karawa da cewa ko da lamarin zai kai ne ya dinga yawo daga wannan filin jirgi zuwa wancan, ba fa zai bar wannan tafarki nasa ba.



Imam Khumaini, a watan Dey 1357 (Disambar 1978), ya kafa majalisar juyin juya halin Musulunci don share fagen kafa hukuma ta Musulunci da kuma dawowarsa gida. A dai dai wannan lokaci kuwa Shah yana ta shirin gudu ya bar kasar sakamakon yadda ya ga al'amurra suna ta ficewa daga hannunsa. Don haka kwanaki biyu da kafa majalisar shawara da tattaunawa don nema wa gwamnatin Bakhtiyar goyon baya, sai ya gudu ya bar kasar a ranar 26 ga watan Dey 1357 (16 ga Disamba 1978). Jin labarin gudun Shah ke da wuya, jama'a a duk fadin Iran sun fito kan tituna don nuna farin cikinsu.



DAWOWAR IMAM GIDA BAYAN SHEKARU 14 NA GUDUN HIJIRA

Tun farko-farkon watan Bahman 1357 (1979) labarin shawarar da Imam ya yanke na dawowa gida ya yadu ko ina. Jama'a kuwa duk wanda ya ji wannan labari sai ya zubar da hawaye don murna, don kuwa abin da suke jira kenan har na tsawon shekaru 14, duk da cewa suna cikin damuwa kan tsaron lafiyarsa, don har zuwa lokacin gwamnatin jeka na yi kan Shah ita ce ke mulki, sannan ga kuma dokan ta bacin da ta kafa na ci gaba da aiki. Imam Khumaini ya riga da ya dauki matsaya ta karshe, don haka sai ya sanar da al'ummar Iran, cikin wani sako da ya aike musu, cewa yana son ya kasance tare da su a wadannan ranaku masu muhimmanci. Hakan ya sanya gwamnatin Bakhtiyar, bisa hadin gwuiwan Janar Haizer, suka rufe filin jirgin saman birnin Tehran sashin zirga-zirgan waje.

Bayan wasu 'yan kwanaki, gwamnatin Bakhtiyar ta bude filin jirgin sama saboda gagarar da ta yi wajen jure wa wannan bore na al'umma. Daga karshe, a safiyar ranar 12 ga watan Bahman 1357 (1 ga watan Fabrairun 1979) Imam Khumaini ya dawo gida bayan shekaru 14 na gudun hijira. Irin gagarumar tarbar da al'umma suka yi masa ya kai matsayin da hatta kafafen watsa labaran yammaci sun gagara inkarin hakan, inda su da kansu suka ce mutanen da suka tarbi Imam Khumaini sun kai miliyan 4 zuwa 6.



WAFATIN IMAM KHUMAINI: RABUWA DA MASOYA, HADUWA DA ABIN KAUNA:

Hakika Imam Khumaini ya isar da abin da yake son fadi da kuma cimma abin da yake son cimmawa tsawon rayuwarsa a aikace. Don haka a halin yanzu cikin tsakiyar watan Khordad 1368 (farko-farkon watan Yuni 1989) yana ta kan shirye-shiryen ganawa da Abin kaunarsa da ya gudanar da dukkan rayuwarsa don neman yardarSa. Wanda ya kasance bai taba mika kai ga wani bayanSa ba, kamar yadda bai taba zubar da hawaye ba sai don Shi, sannan kuma dukkan wakokin irfanin da ya rera (ko rubutawa) sun kasance suna bayanin kan dacin rabuwa da Abin kauna da kuma shaukin da yake yi na saduwa da Shi. A halin yanzu da lokacin yake gabatowa, duk da cewa abu ne da masoyansa ba za su iya jurewa ba, ya rubuta cikin wasiyyarsa cewa: "Ina muku sallama 'yan'uwana maza da mata, cikin kwanciyar hankali da rai mai natsuwa da ruhi mai farin ciki da zuciya mai fatan falalar Allah, in kama hanya zuwa ga gidana na har abada. Kuma ina mai matukar bukatar addu'arku ta alheri. Sannan ina rokon Allah Mai rahama da jin kai Ya karbi uzurina na karancin hidima da kurakurai da gazawa. Kuma ina fata jama'a za su karbi uzurina cikin kowane karanci na hidima da kurakurai da gazawa, kuma su ci gaba da karfi tare da kakkarfar aniya..

Babban abin ban al'ajabin shi ne cewa tun kafin shekaru da rasuwarsa, Imam Khumaini, cikin wasu baitocin wake ya yi batun rasuwarsa cikin watan Khordad inda yake cewa:

Shekaru suna wucewa abubuwa suna ta faruwa

Ni kuwa ina sauraron nasara a tsakiyan Khordad

Daidai karfe sha daya da minti ashirin na dare ranar asabar 13 ga watan Khordad 1368 (3 ga Yuni 1989) lokacin saduwa da abin kauna ya yi. A daidai wannan lokaci ne zuciyar da ta haskaka zukatan miliyoyi da hasken Allah ta tsaya cak (ta bar aiki). A daidai wannan lokaci masoya Imam sun boye wata kamara (na'urar daukan hoto) a asibitin da yake kwance don daukan abubuwan da ke gudana da aikin da aka masa har zuwa lokacin saduwa da abin kauna. Don haka lokacin da gidan talabijin din Iran ya nuna halin kwanciyar hankalin da Imam ya ke ciki a lokacin, kai kace zukatan al'umma za su fashe saboda shaukin da ba za a iya siffanta shi ba.

A lokacin lebbansa cike suke da ambaton Allah, a daren karshe na rayuwarsa ma'abuciya daukaka a daidai lokacin da dantsensa yake daure da alluran da ake kara masa ruwa, amma sai ga shi ya mike don sallar dare da kuma karatun Alkur'ani mai girma. A daidai sa'oin karshe na rayuwarsa, ba abin da ake gani face kwanciyar hankali da nitsuwa ta Ubangiji yana mai ikirari da kadaitakan Ubangiji da imani da sakon Manzo (s.a.w.a) har lokacin da aka dauki ransa zuwa wajen Ubangijinsa. Wannan rasuwa da ta rura wutan bakin ciki a zukata.

Lokacin da aka watsa labarin rasuwar Imam, kai ka ce wata gagarumar girgizar kasa ce ta faru, ko ina sai bakin ciki idanuwa kuwa a cikin Iran da sauran wuraren da aka san Imam kana kuma shiriyarsa ta shiga sai zubar da hawaye suke. Masoyansa sai fitowa suke suna dukan kawuka da fuskokinsu da alkaluma da duk wani irin bayani ya zaga wajen bayyana hakikanin abubuwan da suka faru da irin bakin cikin da ake ciki. Lalle mutanen Iran da sauran ma'abuta juyi suna da hakkin yin irin wannan kururuwa da tarihi bai taba ganin irin girma da tsananinsa ba, don kuwa sun rasa wani masoyi ne da ya dawo musu da mutumci da daukakan da suka rasa, sannan ya katse hannayen muggan shugabanni da 'yan mulkin mallakan Amurka da sauran kasashen yammaci daga kasashensu, sannan kuma ya raya Musulunci da hakkokin musulmi da mutumcinsu, ya kuma tsai da Jamhuriyar Musulunci, ya tsaya kyam a gaban karfin shaidan don fuskantar darurrukan makirce-makircensu na kawar da gwamnatin Musulunci da haifar da fitinar cikin gida da waje tsawon shekaru goma. Kamar yadda kuma ya jagoranci yakin kariya na shekaru takwas yana fuskantar makiyan da suke samun goyon bayan gwamnatocin gabashi da yammaci ma'abuta girman kai. Hakika al'umma sun rasa jagoransu abin kauna sannan kuma makomarsu na addini kana kuma mai kira zuwa ga Musulunci na hakika.

Mai yiyuwa ne mutanen da suka gagara fahimtar hakikanin wannan lamari su kasance cikin rudani lokacin da – gidan talabijin ya nuna - halin da mutane suke ciki yayin jana'iza da bisne jikin Imam mai tsarki. Mai yiyuwa ne su sha mamaki lokacin da suka ji labarin rasuwar mutane masu yawa da suka gagara jurewa wannan babban rashi don haka zuciyarsu ta tsaya cak ko kuma na faduwar wasu gomomin mutane sakamakon tsananin bakin ciki da dai sauran abubuwa makamantan haka da suka faru. Sai dai mutanen da suka san ma'anar kauna kana kuma zukatansu suka ta'allaka da shi cikin sauki za su iya fahimtar lamarin da kuma ganinsa ba a bakin komai ba. A hakikanin gaskiya al'ummar Iran sun kasance masu tsananin kaunar Imam Khumaini, don haka yayin zagayowar shekarar rasuwarsa suke rera taken: "Kaunar Khumaini kaunar dukkan abubuwa masu kyau ne".

A ranar 14 ga watan Khordad 1368 (4 ga watan Yunin 1989), majalisar kwararru (ta zaban jagora) ta gudanar da taronta, inda bayan da Ayatullah Khamene'i ya karanta wasiyyar marigayi Imam Khumaini da ya dauke sa'oi biyu da rabi, 'yan majalisar suka fara gudanar da tattaunawa da shawara kan wanda zai gaji Imam don zama jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Bayan sa'oi na tattaunawa, dukkan 'yan majalisar sun amince da zaban Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i (wanda a lokacin shi ne shugaban kasa) a matsayin sabon jagora. Ayatullah Khamene'i dai ya kasance daga cikin daliban Imam Khumaini (r.a) na kurkusa kana kuma daga cikin fitattun mutanen da suka ba da gagarumar gudummawa a Juyin Juya Halin Musulunci kuma daga cikin wadanda suka taimaka nesa ba kusa ba wajen kaddamar da yunkurin 15 ga watan Khordad, wanda ya tsaya kafada-kafada da sauran mataimakan juyin da ba da gagarumar sadaukarwa duk tsawon yunkurin Imam Khumaini da kuma dukkanin abubuwan da suka faru daga baya.

Shekara da shekaru kasashen yammaci da 'yan amshin shatansu na cikin gida sun kasance cikin dakon wannan rana ta rasuwar Imam bayan sun yanke kaunar samun nasara a kansa. Sai dai farkawar al'ummar Iran da kuma saurin da majalisar kwararrun ta yi wajen zaban mutumin da ya dace da wannan matsayi na jagoranci da kuma irin goyon bayan da mabiya Imam suka yi wa zaben ta sanya makiyan cikin damuwa da kawo karshen mummunan fatansu. Don kuwa ba ma wai kawai juyin Imam bai zo karshe ba ne (kamar yadda makiyan suka so), face ma dai juyin ya sake bude wani sabon shafi ne na ci gaba da watsuwa da kuma karfi. Shin tunani, alheri da gaskiya suna iya gushewa?

A rana da daren 5 ga watan Yuni 1989 miliyoyin al'umma birnin Tehran da sauran al'ummomin da suka shigo garin daga garuruwa da kauyuka sun taru a babban wajen salla (musalla) na Tehran don yin ban kwana ta karshe da mutumin da ya dawo da mutumcin da daukaka (wa al'umma) a duniyar da take cike da duhu da zalunci ta hanyar yunkuri da juyinsa kana kuma ya watsa yunkurin komawa ga Allah Madaukakin Sarki da daukakar dan'Adam a duk fadin duniya.

Dukkanin abubuwan da aka yi a wajen jana'izar da hannun al'umma aka yi shi, cikin kauna da shauki. An dora jikin Imam mai tsarki a wani waje da kowa zai iya ganinsa yana rufe da koren kyalle tsakiyan miliyoyin masu juyayi, dukkansu cikin bakin ciki da zubar da hawaye alhali suna magana da Imaminsu cikin harshen da ya sawwaka ga kowa. Dukkanin hanyoyi da lungunan zuwa wajen sallar cike suke da jama'an da suke sanye da bakaken kaya don nuna bakin cikinsu, gidaje da shaguna kuwa duk an sanya musu tutocin juyayi da nuna bakin ciki, karatun Alkur'ani kuwa daga ko ina, masallatai, ofisoshi, ma'aikatu da gidaje sai tashi yake yi. Da daddare kuwa ko ta ina sai kyandir kake gani an kunna su don nuna alamun hasken da Imam ya zo da shi, duk sun haskaka wajen sallar da kewaye, alhali iyalai sun kewaye su (kyandir) suna kallon haskensu don tuntuni da irin hasken da jagoransu abin kaunarsu ya zo musu da shi.

Taken "Ya Husain" da masu juyayin suke rerawa alhali suna dukan kirji da kawunansu ya mai da yanayin wajen tamkar yanayin Ranar Ashurar da Imam Husaini (a.s) ya yi shahada. Bisa la'akari da cewa al'umma ba za su sake jin sautin Imam Khumaini dake cike da yanayin tunasar da mutum Ubangiji a Husaniyyar Jamaran ba, hakan ya kasance abin tashin hankali ga al'umma. Haka dai mutane suka ci gaba da zama a gefen jikin Imam mai tsarki duk tsawon dare har garin Allah ya waye, inda da sassafiyar ranar 6 ga Yuni 1989 aka yi masa salla karkashin limancin Ayatullah al-Uzma Golfaygani.

Babu shakka irin yawan al'ummar da suka fito don tarbar Imam Khumaini a ranar 12 ga watan Bahman 1357 (1 Fabrairu 1979) da kuma sake maimaita hakan a ranar jana'izarsa, duk suna daga cikin abubuwan mamaki na tarihi. Kafafen watsa labaran duniya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka fito don tarbar Imam lokacin da ya dawo gida sun kai miliyan shida, amma wadanda suka fito don jana'izarsa sun kai mutanen miliyan tara. Hakan kuwa duk da cewa cikin wadannan shekaru goma sha daya na jagorancin Imam Khumaini kasashen Turai sun yi dukkan abin da za su iya wajen nuna adawarsu ga Jamhuriyar Musulunci da suka hada da kallafa mata yakin shekaru takwas da dai sauran makirce-makirce da ya sanya al'ummar Iran cikin mawuyacin hali na kunci da takurawa da kuma rasa abubuwan kaunarsu masu yawan gaske wanda a bisa dabi'a hakan zai sanya su gaji da kuma watsi da wannan juyi nasu, to sai dai ina hakan bai faru ba daga dukkan bangarori. Don kuwa al'ummar da suka tarbiyyantu a makarantar Imam Khumaini sun tasirantu da kuma imani da kalaminsa na cewa: "A duniya, gwargwadon girma da darajar manufa, gwargwadon karfin jurewa wahala, cutarwa, sadaukarwa da rashi na duniya ne".

Bayan da bisne jikin Imam mai tsarkin ya ci tura sakamakon yawan jama'a, gidan radiyo ya sanar da daga jana'izar har zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba don haka jama'a su koma gidajensu. Sai dai jami'ai sun riga da sun san cewa lokaci bayan lokaci jama'a za su ci gaba da zuwa wajen jana'izar ne, don haka dai aka daure aka gudanar da ita a yammacin wannan rana duk kuwa da irin wahalhalun da ake fuskanta. Wasu kafafen watsa labaran duniya ma sun nuna wani sashi na wannan jana'iza.

Ta haka rasuwar Imam Khumaini, kamar rayuwarsa, ta kasance matakin farko na sabuwar wayewa da gwagwarmaya da kuma tabbatar da tafarki da ambatonsa har abada, don kuwa gaskiya abar tabbata ce matukar duniya tana ci gaba da wanzuwa.

Takaitaccen tarihin rayuwar jagoran harkar musulunci a Nigeria Sheikh Ibrahim Zakzaky (h)



Rana da wajen da aka haifi Sheikh:
An haifi Sheikh ne a ranar 5 ga watan Mayu shekara ta 1953[15 ga Sha'aban 1372 AH] a garin Zaria dake cikin jihar Kaduna a Tarayyar Nigeria, kuma sunan sa Zakzaky kalma ce dake nufin 'mutumin zazzau'.
Sheikh Ibrahim Zakzaky shine dan Yaqoub shi kuma dan Aliyu shi kuwa dan Tajuddin dan Imam Hussain. Shi Imam Hussain wani bawan Allah ne daya fito daga Mali yazo garin Sokoto a lokacin Mujaddadi Sheikh Usman dan Fodio[RA] ya zauna tare da shi a matsayin almajirin sa, ta haka nema a lokacin da Shehu Usman dan Fodio[RA] ya nada Mallam Musa a matsayin Amir na lardin zazzau sai ya hada shi da Imam Hussain a matsayin mai bashi shawara. Ta haka ne a hankali-a hankali auratayya ta rika shiga tsakanin iayalen su kuma suka zama yan uwan juna ta wannan tun a farkon karni na 19.
Mahaifin Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rasu ne tun shekara ta 1972, sai dai mahaifiyar sa har yanzun tana nan raye, Sheikh shine na biyar a wajen mahaifin su.
Karatun sa:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya fara karatu ne tun yana yaro karami a makarantar koyon karatun Al-kurani mai girma a makarantun Allo na al'ada kamar yadda aka saba tare da surkawa da karatun ilmin addinin musulunci wajen manyan malamai na wancan lokacin har ya zuwa lokacin da ya kai shekaru goma sha shida inda ya fara haduwa da tsarin karatu na zamani a shekara ta 1979 inda ya fara karatu a makarantar horar da malaman Arabiyya dake Zaria. Sannan daga shekara ta 1971-1975 ya shiga makarantar koyon larabci ta Kano watau School for Arabic Studies[SAS] wadda aka gina tun 1934 a matsayin makarantar koyon aikin lauya. sannan kuma daga baya ita ce ta haifar da babbar jami'ar Bayero da aka sani a yanzu. Kusan baki dayan alkalin alkalan jihohin Arewa daga wannan makaranta suka sami horon su. Saboda irin yadda Sheikh Zakzaky yake da ra'ayin fadada ilmin sa kan wasu darussa da ba'a koyarwa a wannan makaranta yasa ya gwama karatun nasa na Grade II da wasu maddoji ba tare da yayi su a baya ba kamar sanin gwamnati [Government] da ilmin tattalin arziki[Economics] inda yayi jarabawar GCE a kansu. Daga bisani Sheikh yayi jarabawa ta gaba[Advanced level GCE] akan wadannan maddojin:Government, Economics,Hausa,da kuma Islamic Studies inda ya sami kyakyawan natija wadda ta bashi damar shiga jami'a kai tsaye a shekara ta 1976 zuwa 1979 inda ya fara karatun digirin farko [B. Sc] akan sanin tattalin arziki [Economics].
Sheikh yayi musharaka cikin kungiyar dalibai ta musulmi inda ya zama fitaccen mamba a cikin makaranta da kuma  matsayin kasa baki daya inda a shekara ta 1978 ya zama babban sakataren kungiyar na kasa sannan kuma yayi zama mataimakin shugaban kungiyar bangaren harkokin kasashen waje a shekara ta 1979. Sheikh Zakzaky yana daya daga cikin wadanda suka jagoranci kare Shari'ah a lokacin da aka yi wani jerin gwano na nuna goyon baya ga Shari'ah a baki dayan kasar.
Sheikh Zakzaky bisa sha'awar da yake da ita na fadada karatun sa ya ci gaba da zuwa wajen malamai da suka hada da Malam Sani Abdulkadir, Malam Isa na Madaka, Malam Sani Na'ibi da kuma Malam Ibarhim Kakaki dukkanin su a birnin Zaria. Haka nan kuma a Kano Sheikh yayi karatu wajen Shawish Abdallah na Sagagi da Malam Nuhu limamin Yola.
Ayyukan sa:
Babban aikin da Sheikh Ibrahim Zakzaky ya sanya a gaba shine karatu da kuma yada ilmi tun yana matsayin dan makaranta har ya zuwa wannan lokacin. An mayar da koyarwan sa cikin yan littafai a harshen Hausa da Turanci wadanda aka watsa su a ko ina cikin kasar sannan da yawa daga cikin wa'azuzzukan sa a yanzu suna cikin CD na Computer da kaset-kaset na Recorder a ciki da wajen kasar. Dr. Iqbal Siddiqui ya taba siffanta Sheikh a matsayin "Kashin bayan harkar musulunci a Nigeria"  Babban manufar harkar musulunci da Sheikh yakewa jagoranci shine wayar da kan musulmi abin daya doru a kansu a matsayin su na daidaiku da kuma al'umma. 
Yanzun haka harkar musulunci tana da makarantu dake karkashin ta na Primary da kuma gaba da Primary sama da dari uku wadanda suke a garuruwa daban daban dake fadin kasar. Wadannan makarantu an yi musu suna da makarantun Fudiyya. Haka kuma akwai cibiyoyi da da wuraren bincike da dama a manyan garuruwa na kasar karkashin wannan harka. Harkar ta mallaki jaridar da tafi ko wacce a kasar shiga ko ina da harsheen Hausa wadda ake kira Al-mizan. Sheikh ya sami matsala da hukumomi cikin kaki ko fararen kaya wadanda suke ganin cewa irin salon wa'azin nasa yana barazana ga mulkin su. A lokacin General Sani Abacha an kama Sheikh ne da tuhumar yana wa'azin 'babu hukuma sai ta Allah'.
A halin da ake ciki dai yanzun haka harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta cika shekaru 30 tana kira kan komowa karkashin tsari na musulunci.
Tsawon tsarewar da aka yiwa Sheikh:
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya kwashe shekaru tara a tsare a kurkuku daban-daban na kasar, daga shekara ta 1981-1984 an daure shi a kurkukun Enugu sai kuma kurkukun neman bayanai da bincike na jami'an leken asiri na kasa dake Lagos[Intorregation center] a shekara ta 1984-1985 sai kuma Kiri-kiri a shekara ta 1985 kurkukun Port harcout daga 1987-1989 sannan daga 1996-1997 duk dai a can Port Harcout. Sai kuma kurkukun Kaduna a 1987 sannan daga 1997-1998.
Tafiye-Tafiyen sa:
Sheikh Zakzaky yayi tafiya zuwa kasashe kamar su Britaniya, Saudi Arabia, Iran, Lebanon, Afrika ta kudu, Amurka, da Rasha. Dukkanin wadannan tafiye-tafiye yayi sune ta hanyar gayyata don dalilai na addini ko halartan tarurrukan karawa juna ilmi.
Mata da yara:
Sheikh yana da mace daya da kuma yaya tara.

HUDUBAR MANZON ALLAH (S.A.W.A) Akan Watan Ramadan

DAGA SAIFULLAH M. KABIR

Bislmillahir Rahmanir Rahim
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ahli Muhammad
Sheik as-Sudduk (Allah ya kara masa rahma) ya fitar a cikin littafinsa mai suna “Uyun al-akhbar ar-Ridha (a.s)” da isnadinsa da ya kare da Amirul-mu’uminin Ali bin Abi Dalib (a.s) ya ce:

Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi mana huduba a wata rana (a watan Ramadan), inda yake cewa:

“Ya ku mutane! Lallai hakika watan Allah mai albarka ya zo muku (tattare) da rahama da gafara. Watan da shi ne mafificin dukkan watanni a wajen Allah, ranakunsa kuma su ne mafifitan raneku, sa’o’insa kuma sune mafifitan sa’o’i.

Shi wata ne da aka kira ku zuwa bakuncin Allah a cikin shi, aka kuma sanya ku cikin ma’abota karimcin Allah a cikin shi. Numfashinku a cikin shi ibada ne, haka ayyukanku a cikin shi karbabbu ne, kuma addu’o’inku a cikin shi abin amsawa ne; don haka ku roki Allah Ubangijinku da gasgatattun niyyoyi da tsarkakan zuciya kan cewa Ya sa ku sami dacewa da azumtar sa (watan) da karatun littafinSa (Allah), domin lallai tababbe (na hakika) shi ne wanda ya rasa gafarar Allah a wannan wata mai girma.

Ku tuna da kishirwar lahira ta hanyar yunwa da kishirwanku a cikinshi. Kuyi sadaka ga matalautanku da miskinanku, ku girmama dattawanku, kuma ku tausayawa kanananku, ku kuma sadar da zumuninku. Ku kame harsunanku kuma ku kau da kai daga abubuwan da ba ya halatta idanuwanku su kalla da abubuwan da ba ya halatta kunnuwanku su ji.

Ku tausayawa marayun mutane, ku ma sai a tausaya marayunku. Ku tuba zuwa ga Allah daga zunubanku, ku daga hannuwanku zuwa gare Shi da addu’a a lokutan sallolinku, domin (lokutan sallolin) ne mafifitan lokutan da Allah Madaukaki ke kallon bayinSa da rahama a cikin su, Ya ke sauraron su idan suka gana da shi, Ya kuma amsa musu idan suka roke Shi.

Ya ku mutane! Lallai numfashinku jingina ne ga ayyukanku, don haka ku fitar da su (numfashin) da istigfarinku. Haka bayayyakinku sun nauyaya da ayyukanku, to ku sassauta musu da tsawaita sujjadunku. Ku sani cewa Allah Madaukaki Ya rantse da daukakarSa cewa ba zai azabtar da masu sallah da masu sujjada ba. Kuma ba zai raunana su da wuta a ranar da mutane za su tsaya gaban (Allah) Ubangijin talikai ba.

Ya ku mutane! Wanda ya bude bakin mai azumi mumini a wannan wata, to da hakan yana da ladan (wanda) ya ‘yanta bawa a wajen Allah da gafararta abin da ya gabata na zunubbansa”.

Sai aka ce ya Manzon Allah, ba kowannen mu ne zai iya haka ba. Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce:

“Ku kaucewa wuta ko da da tsagin dabino ne! ku kaucewa wuta ko dad a kurbin ruwa ne!!”

“Ya ku mutane! Wanda ya kyautata halayyarsa a wannan wata zai ketare siradi a ranar da kafafu ke zamewa; kuma wanda ya sassauta ga wadanda ya mallaka Allah Zai saukaka masa hisabinsa; kuma wanda ya kame sharrinsa a cikin shi (wannan wata) Allah Zai kame fushinSa daga gare shi a ranar da zai hadu da Shi, kuma wanda ya kyautatawa maraya a cikin shi Allah zai karrama shi a ranar haduwar su. Haka wanda ya sadar da zumuncinsa a cikin shi Allah zai sadar da rahmarSa gare shi a ranar haduwar su; wanda kuwa ya yanke zumuncinsa Allah zai yanke rahmarSa gare shi ranar da zai hadu da shi.

Wanda ya yi nafilar salla a cikin shi Allah Zai rubuta mishi barranta daga wuta. Wanda ya sauke nauyin farilla a cikin shi kuwa yana da ladan wanda ya sauke nauyin farillai saba’in a wasu watannin da ba shi (Ramadan) din ba; wanda ya yawaita yi mini sati a cikin shi Allah zai nauyaya mishi ma’aunin ayyukansa a ranar da ma’aunan ayyuka ba su da nauyi; wanda ya yi tilawar aya daya daga al-Kur’ani kuwa yana da ladan wanda ya sauke al-Kur’ani a wani wata da ba shi ba.

Ya ku mutane! Lallai an bude kofofin Aljanna, don haka ku roki Ubangijinku da kar Ya rufe su gare ku; kuma an rufe kofofin wuta, to ku roki Ubangijin ku kar ya bude su gare ku; haka an daure shedanu, don haka ku roki Allah kar su sami iko a kan ku.”

Sai Amirul-Muminin Ali (a.s) ya mike ya ce: “Ya Manzon Allah, mene ne mafifiin ayyuka a wannan wata?”

Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya amsa masa da cewa: “Ya kai Baban Hasan! mafificin ayyuka a wannan wata shi ne tsentseni (kame kai) daga abubuwan da Allah Ya haramta.”

ALLAH YA SA MUNA CIKIN WADANDA ALLAH KE GAFARTAMA A WANNAN WATAN

SON ALI (A) DA 'YA'YAN GIDANSA SHINE SHI'ANCI KINSU KUMA SHINE SUNNANCI ( WAHABIYANCI)



SON ALI (A) DA 'YA'YAN GIDANSA SHINE SHI'ANCI KINSU KUMA SHINE SUNNANCI (WAHABIYANCI).

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
ALLAHUMMA SALLI  ALA MUHAMMAD WA ALI MUHAMMAD.

CIKIN WANNAN KARATU DA ZAN GABATARWA MAI KARATU  ZAI BAYYANA AGARESHI YASAN CEWA BA KOMAI AKE NUFI DA SHI'ANCI BA SAI SON IMAM ALI (A) DA 'YA'YAN GIDANSA, SANNAN KUMA BA KOMAI AKE NUFI DA SUNNANCI BA FACE SAI KIN IMAM  ALI (A) DA 'YA'YAN GIDANSA. MAI KARATU ZAI  FAHIMCI HAKA KAI TSAYE TA YANDA ZAI GA ANA TUHUMTAR MUTUM DAYIN SHI'ANCI BA DON KOMAI BA SAI DON  NUNA KAUNARSA DA SOYAYYARSA GA IMAM ALI(A) DA 'YA'YAN GIDANSA DAYAKEYI. AMMA AGEFE GUDA KUMA SAI KAGA MAKIYIN IMAM ALI (A) NA ZAGINSA  AMMA KUMA YA ZAMA  AMINTACCE YARDAJJE. 

IMAMUSH-SHAFI'IY  YANA DAYA DAGA CIKIN MANYAN MALAMAN MAZHABOBI GUDA HUDU WANDA DUNIYAR AHLUS-SUNNAH TAKE YIN TINKAHO DASHI TARE DAYIN RIKO DA MAZHABARSA. AMMA DUK DA IRIN WANNAN MATSAYI DAYAKE DASHI BAI HANA MUTANE  TUHUMATARSA DA ZARGINSA DAYIN SHI'ANCI BA, BA DON KOMAI BA SAI DON NUNA KAUNARSA DA KUMA AMBATON  AHLUL-BAIT DAYAKEYI KAMAR YANDA SHI SHAFI'IY YAKE  BAYYANAWA  ACIKIN BAITOCIN DAYAYI  KAMAR HAKA : 

إذا في المجلس نذكر عليا .. وسبطيه وفاطمة الزكية
يُقال تجاوزا يا قوم هذا .. فهذا من حديث الرافضية
برئت إلى المهيمن من أناس ..  يرون الرفض حب الفاطمية

NUNA ZARGI DA KUMA TUHUMA DAYIN SHI'ANCI BA AKAN SHAFI'IY  KADAI YATSAYA BA, YA SHAFI DUK WANI MUTUM WANDA YA DAUKI GABARAN YADA KAUNA DA KUMA YADA HADISAN DASUKA SHAFI FALALA DA KUMA DARAJOJIN AHLUL-BAITI (A). SABODA HAKA YIN WANNAN AIKI NA YADA KAUNAR AHLUL-BAITI YA JANYOWA WADANSU DAGA CIKIN MANYAN MALAMAN AHLUS-SUNNAH  ZARGINSU DAYIN SHI'ANCI, BAWAI DON YA TABBA CEWA SU 'YAN SHI'A NE NA HAKIKA BA. BARI NA BUGA MAKU 'YAN MISALAI AKAN WANNAN BATU NAWA DANA KEYI GASU KAMAR HAKA :



وقال أبو علي بن الصواف عن عبد الله بن أحمد لما حدث نصر بن علي بهذا الحديث يعني حديث علي بن أبي طالب أن رسول الله صلى الله عليه وسلم أخذ بيد حسن وحسين فقال: "من أحبني وأحب هذين واباهما وأمهما كان في درجتي يوم القيامة" أمر المتوكل بضربه ألف سوط فكلمه فيه جعفر بن عبد الواحد وجعل يقول له هذا من أهل السنة فلم يزل به حتى تركه

YAZO ACIKIN LITTAFIN TAHZIBUT-TAHZIYB NA IBN HAJR AL-ASQALANIY 33/34. AKAR KASHIN TARJAMAR NASRU DAN ALIY. ABU ALIYU BNL SAWWAAF DAGA ABDULLAHI DAN AHMAD YANA CEWA ALOKACINDA NASRU DAN ALIY YA ZANTARDA WANNAN HADISI NA ALIYU DAN ABIY DALIB CEWA ANNABI (S.A.W.)  YAYI RIKO DA HANNUN HASAN DA HUSAINI YACE : WANDA YASONI YASO WADAN NAN YA KUMA SO MAHAIFIYARSU DA MAHAIFINSU, ZAI SAMI KASUNCI  ATARE DANI RANAR ALKIYAMA"  SAI MUTAWAKKIL YA BADA UMARNI DA AYI MASA BULALA DAI-DAI HAR GUDA DUBU. SAI JA'AFAR DAN ABDUL-WAHID YAYI MASA MAGANA YANA CEWA DA ( MUTAWAKKIL) WANNAN MUTUMIN ( MAI FADAR WANNAN HADISI) YANA DAGA CIKIN AHLUS-SUNNAH ( MA'ANA BA DAN SHI'A BANE) BAI GUSHE YANA FADAR HAKA HAR SAI DA ( MUTAWAKKIL ) YA KYALESHI.

TIR KASHI!!! DAGA FADAR HADISIN ANNABI (S.A.W.) SAI CIBI YA ZAMA KARI AHAU KAN MUTUM DA BUGU BAJI BAGANI HAR WAI ACE AYI MASA  BULALA DAI-DAI HAR GUDA DUBU?

DAMA DA ZARAR ANA ZARGIN MUTUM DA FADAR HADISIN KARYA SAI KAWAI YA ZAMANA HANYARDA ZA'ABI WAJEN LADABTAR DASHI ITACE IRIN WANNAN HANYA WADDA ZA'AYIWA DAN ADAM BULALA DAI-DAI HAR GUDA DUBU?

IDAN HAKA ABIN YAKE SHIN AN TABA LADABTAR DA WANIN WANNAN MUTUMIN WAJEN BADA UMARNIN AYI MASA BULALA DAI-DAI HAR GUDA DUBU DAYA?

DAMA DAGA ZARAR MUTUM YA FADI HADISIN ANNABI (S.A.W.) SAI AHAU KANSA DA BUGU BATARE DA AN TAN-TANCE INGANCIN SANADIN HADISIN DAYA KAWO BA?

ATAKAICE  WANNAN SHIKE KARA TABBATAR MANA DACEWA MASOYAN AHLUL-BAITI KO KUMA MAI YADA HADISANSU BAZAI TABA KUBUTA WAJEN  ZARGINSA DAYIN SHI'ANCI BA, KAMAR YANDA GASHI KIRI-KIRI MUTAWAKKIL YANA ZARGIN WANNAN BAWAN ALLAH DAYIN SHI'ANCI BA DON KOMAI BA SAI DON  WANNAN HADISI DAYA FADA AGABAN MUTAWAKKIL, HAR SAI DA JA'AFAR DAN ABDUL-WAHID YA FADA MASA CEWA WANNAN MUTUM BA DAN SHI'A BANE BA YANA DAGA CIKIN AHLUS-SUNNAH.



ولم يكن أحد في رأس الثلاث مئة أحفظ من النسائي، هو أحذق بالحديث وعلله ورجاله من مسلم، ومن أبي داود، ومن أبي عيسى، وهو جار في مضمار البخاري، وأبي زرعة، إلا أن فيه قليل تشيع وانحراف عن خصوم الامام علي، كمعاوية وعمرو... سيراعلام النبلاء.14\133.

ZAHABIY YANA FADA ACIKIN SIYARU DINSA DAN GANE DA IMAMUN NASA'IY CEWA ACIKIN KARNI NA UKU BABU WANDA YAKAISHI SANIN HADISI, KAI BARI SHINE MAFI HAZAKA DA SANIN HADISI DA ILLOLINSA DAKUMA SANIN MAZAJE FIYE DA MUSLIM, DA ABIY DAU'DA DA TIRMIZIY. KAI SAI DAI ASANYA SHI TSARAR IRIN SU BUKHARI DA ABIY ZAR'AH, SAI DAI KUMA CEWA DA AKWAI KAN KANIN SHI'ANCI ATARE DASHI DA KUMA JUYA BAYA GA MUTANEN DA SUKAYI KHUSUMA DA IMAM ALI (A)  KAMAR MU'AWIYA DA AMRU …

DA WANE DALILI NE AKE ZARGIN NASA'IY DAYIN KANKANIN SHI'ANCI, SHIN DA FIFITA ALI (A) AKAN ABUBAKAR DA UMAR KO KUWA SABODA YANA SON ALI (A) ? 

KO KUWA DON SABODA YA JUYAWA WADANCAN SAHABBAI BAYA? IDAN HAKA ABIN YAKE MEYASA MALAMAN DASUKACE FALALOLIN MU'AWIYA GABA DAYA BASU TABBATA BA, BASU ZAMO  ANCE DASU 'YAN SHI'A BA? 

ATAKAICE SUN BAYYANAR DA ZARGI GA MALAMANSU DAYIN SHI'ANCI  KAMAR  IRINSU AL-HAKIMUN NAISABURIY, KAMAR IRINSU AL-HAFIZ AL-IMAMUL-MUHADDIS IBNS SAQQA'I, KAMAR FAKHRUDEEN AL-HAFIZ AL-KANAJIY ASH-SHAFI'IY  DA-DAI SAURANSU.

BAYAGA HAKA GA  DADI AKAN ABINDA YAKE KARA KARFAFAR  GASKIYAR ABINDA NA FADA CEWA SON ALI (A) SHINE SHI'ANCI KINSA KUMA SHINE SUNNANCI?

والتشيع محبة على وتقديمه على الصحابة فمن قدمه على أبي بكر وعمر فهو غال في تشيعه ويطلق عليه رافضي وإلا فشيعي إن فإن انضاف إلى ذلك السب أو التصريح بالبغض فغال في الرفض...هدي الساري مقدمة فتح الباري- ابن حجرالعسقلاني.1\360.

IBN HAJR YANA CEWA : SHI'ANCI SHINE SON ALI (A)  DA KUMA GABATAR DASHI AKAN SAHABBAI. WANDA YA GABATAR DASHI AKAN ABUBAKAR DA UMAR TO WANNAN SHI MAI TSANANI NE ACIKIN SHI'ANCINSA ANA KUMA KIRANSA DA  BARAFIBE , IDAN BA HAKABA TO SHI DAI DAN SHI'ANE KAWAI (MA'ANA IDAN KA FIFITA ALI AKAN ABUBAKAR DA UMAR KAI BARAFIBE NE IDAN KUMA BAKAYI HAKABA KAWAI KANA SON ALI TO KAI DAN SHI'A NE). IDAN YA HADAR DA ZAGI ACIKIN HAKA ( BAYA GA FIFITA ALI AKAN ABUBAKAR DA UMAR) KO KUMA BAYYANAR DA KIYAYYA  TO WANNAN GULLATIN YAN SHI'A KENAN…

WANNAN ZANCE NA IBN HAJR YAKARA  BAYYANA MANA CEWA SON ALI SHINE SHI'ANCI. FADIN IBN HAJR CEWA DA KUMA GABATAR DASHI AKAN SAHABBAI  BAWAI YANA NUFIN ALI(A) BAI FIFICI WADANSU SAHABBAI BA, A'A YANA NUFIN FIFITA ALI (A) AKAN ABUBAKAR DA UMAR SABODA SHI  USMANU AN SAMI SABANI ACIKIN WANDA YAFI TSAKANIN SHIDA ALI (A).  GULLANCI KUWA ACIKIN SHI'ANCI SHINE ZAGIN DUK WANI SAHABIN ANNABI (S.A.W.) AMMA KUMA BANDA ZAGIN ALI (A) DALILI  NA KUWA ANAN SHINE AN SAMI MUTANEN DASUKA ZAGI ALI(A) AMMA BASU ZAMTO ANA KIRANSU DA GULLATUN 'YAN SHI'ABA, BARI SAI MA YABO DA GIRMAMAWA DASUKA SAMU DAGA WAJEN MALAMAN AHLUS-SUNNAH. KUBIYONI ASANNU 'YAN UWA ZAKU TABBATAR DAHAKA.

KAFIN NASHIGA CIKIN WANNAN BAYANI GADAN-GADAN  WAJEN KAWO MUTANEN DASUKE NUNA KIYAYYARSU GA IMAM ALI (A) DA 'YA'YAN GIDANSA ZAN SO NA SAKEYIN SHIMFIDA WAJEN KAWOWA MAI KARATU  KADAN DAGA CIKIN IRIN AQIDUN AHLUS-SUNNAH AKAN SAHABBAN ANNABI  (S.A.W.) WANDA YIN HAKA SHINE ZAI KARA ZAMA MA'AUNIN WACCAN MAGANA TAWA DANA AMBATA TUNDA FARKON FARI :


وقال الإمام أحمد بن حنبل في كتاب السنة: (ومن السنة ذكر محاسن أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم كلهم أجمعين، والكف عن الذي جرى بينهم، فمن سب أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم أو واحداً منهم فهو مبتدع رافضي، حبهم سنة، والدعاء لهم قربة، والاقتداء بهم وسيلة، والأخذ بآثارهم فضيلة.)


IMAM AHMAD YAFADA CEWA YANA DAGA SUNNAH  AMBATON KYAWAWAN AYYUKAN SAHABBAN ANNABI (S.A.W.) BAKI DAYANSU. DA KUMA KAMEWA GA BARIN ABINDA YA GUDANA ATSAKANINSU, WANDA DUK YA ZAGI SAHABBAN ANNABI (S.A.W.) KO KUMA DAYA DAGA CIKINSU SHI WANNAN DAN BIDI'A NE BARAFIBE ( DAN SHI'A) SON SU SUNNAH NE, ADDU'A GARESU KUSANCI NE, KOYI DASU TSANAN TUWA NE, RIKO DA TAFARKINSU FALALA NE.

ونحب أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم، ولا نفرط في حب أحد منهم ، ولا نتبرأ من أحد منهم ، ونبغض من يبغضهم، وبغير الخير يذكرهم، ولا نذكرهم إلا بخير، وحبهم دين وإيمان وإحسان، وبغضهم كفر ونفاق وطغيان. 

MALLAM DAHAWIY YANA FADA ACIKIN LITTAFINSA MAI SUNA AQIDATUL-WASIDIYYAH CEWA : MUNA SON SAHABBAN MANZON ALLAH (S.A.W.) BAMA SHIGE GONA DA IRI ACIKIN SON DAYANSU, BAMA KUMA YIN BARA'A ACIKIN DAYANSU, MUNAKIN MAI KINSU, KO KUMA YAKE AMBATONSU BADA ALKHAIRI BA. BAMA AMBATONSU SAI DA ALKHAIRI, SON SU ADDINI NE DA IMANI DA KYAUTAYI. KINSU KUMA KAFIRCI NE DA MUNAFURCI DA KUMA YIN DAGAWA.

ABIN TAMBAYA ANAN SHINE SHIN DAGASKE HAKA YAKE AWAJEN AHLUS-SUNNAH DUK MAI ZAGIN SAHABIN ANNABI (S.A.W.) DAN BIDI'A NE BARAFIBE NE (DAN SHI'A) KAMAR YANDA AHMAD DAN HANBALI YA AMBATA?

SHIN DAGASKE HAKA YAKE CEWA DUKANIN AHLUS-SUNNAH SUNA KIN DUKANIN MAI KIN SAHABIN ANNABI (S.A.W.)?

SHIN DAGASKE HAKA YAKE CEWA AHLUS-SUNNAH BASA BARA'A GA KOWANE DAYA DAGA CIKIN SAHABBAN ANNABI (S.A.W.)?

SHIN HAKA YAKE DAGASKE AWAJEN AHLUS-SUNNAH HAKA YAKE DUK MAI KIN SAHABIN ANNABI (S.A.W.) KAFIRI NE MUNAFUKI NE MAIYIN DAGAWA NE?

IDAN HAR WADAN NAN ABUBUWA DANA JERO GASKIYA NE HAKA SUKE AWAJEN AHLUS-SUNNAH BA ALMARA BACE BA, WANE DALILI NE YASA SUKE SIQANTA MUTANEN DASUKE KIN IMAM ALI (A) KUMA SUKE ZAGINSA?
KO KUWA SHI IMAM ALI (A) BAYA DAGA CIKIN JERIN SAHUN SAHABBAN DASUKE  ZAGINSU MUNAFURCI NE DA KAFIRCI?

MATSAYIN MASU KIN ALI (A) :

إبراهيم" بن يعقوب بن إسحاق السعدي أبو إسحاق الجوزجاني سكن دمشق… قال الخلال: "إبراهيم جليل جدا كان أحمد بن حنبل يكاتبه ويكرمه إكراما شديدا" وقال النسائي: "ثقة"
...قلت وقال ابن حبان في الثقات: "كان حروري المذهب ولم يكن بداعية وكان صلبا في السنة 
...وقال ابن عدي: "كان شديد الميل إلى مذهب أهل دمشق في الميل على علي"

YAZO ACIKIN LITTAFIN TAHZIYBUT-TAHZIYB CIKIN TARJAMAR IBRAHIMUL JAWZAJANIY… KHALLAL YACE MUTUM NE MAI GIRMA AHMAD DAN HANBALI YAKASANCE YANA GIRMAMA SHI MATUKAR GIRMAMAWA HARMA YANA RUBUTA HADISANSA. NASA'IY  DASHIDA IBN HIBBAN SUNCE SIQANE. MAZHABIN KHAWARIJAWA KE GARESHI ( WATO MUTANEN DASUKA YAKI IMAM ALI (A) SUKA KAFIRTA SHI) AMMA BAMAI KIRA BANE IZUWA GA MAZHABIN NASA, SANNAN KUMA MAI TSANANI NE CIKIN BIN SUNNAH. MAI TSANANIN KARKATA NE IZUWA GA TAFARKIN MUTANEN DAMASHQ CIKIN JUYAWA ALI BAYA.

MEYASA? MEYASA?? WANNAN MUTUM BAI KASANCE BARAFIBE DAN BIDI'A BA, MEYASA BAI KASANCE MUNAFUKI KAFIRI BA? SAI YA ZAMO MAI TSANANI NE CIKIN BIN SUNNAH??? INA BIN SUNNAH YAKE CIKIN KIN MUTUMINDA SON SA IMANI NE KINSA MUNAFURCI NE?

436 - خ 4 البخاري والأربعة حريز بن عثمان
وقال بن المديني لم يزل من أدركناه من أصحابنا يوثقونه وقال دحيم حمصي جيد الإسناد صحيح الحديث وقال أيضا ثقة
حدثنا إسماعيل بن عياش سمعت حريز بن عثمان يقول هذا الذي يرويه الناس عن النبي صلى الله عليه و سلم أنه قال لعلي أنت مني بمنزلة هارون من موسى حق ولكن أخطأ السامع قلت فما هو فقال إنما هو أنت مني بمنزلة قارون من موسى
قيل ليحيى بن صالح لم لم تكتب عن حريز فقال كيف اكتب عن رجل صليت معه الفجر سبع سنين فكان لا يخرج من المسجد حتى يلعن عليا سبعين مرة وقال بن حبان كان يلعن عليا بالغداة سبعين مرة وبالعشي سبعين مرة فقيل له في ذلك فقال هو القاطع رؤوس آبائي وأجدادي

HARIYZU DAN USMANU BUKHARI YAYI RIWAYA DAGA GARESHI DA RAGOWAR MALAMAI GUDA HUDU… IBNL MADINIY YACE WADANDA MUKA RISKA DAGA ABOKANAN MU BASU GUSHE SUNA SIQANTA SHIBA… ISMA'IL DAN IYASH YACE NAJI HARIYZ YANA CEWA HADISIN MANZILAH GASKIYA NE SAI DAI CEWA MARAWAICIN HADISIN YAYI KUSKUREN JINE, SAI NACE DASHI YAYA LAMARIN YAKE ? SAI YACE : YANDA YAKE SHINE MATSAYINKA (ALI) AWAJENA SHINE MATSAYIN QARUNA AWAJEN MUSA (WAL-IYAZU BILLAHI)… ANCE DA YAHAYA DAN SALIHU MEYASA BAKA RUBUTA HADISAN HARIYZ SAI YACE DON MAI ZAN RUBUTA HADISIN MUTUMIN DANAYI SALLAR ASUBA ATARE DASHI TA TSAYIN SHEKARA BAKWAI, SAI DAI CEWA BAYA FITOWA DAGA CIKIN MASALLACI HAR SAI YA LA'ANCI ALI SAU SABA'IN. IBN HIBBAN YACE YANA LA'ANTAR ALI SAFIYA DA MARAICE SAU SABA'IN SABA'IN, DA AKA TAMBAYESHI MAI YASA YAKEYIN HAKA SAI YACE ALI SHINE YA YANKE KAWUKAN IYAYENA DA KAKANNI NA… TAHZIYBUT TAHZIYZ.8/113.

- عمر" بن سعد بن أبي وقاص الزهري أبو حفص المدني سكن الكوفة… قال العجلي كان يروي عن أبيه أحاديث وروى الناس عنه وهو تابعي ثقة وهو الذي قتل الحسين...


UMAR BN SA'AD DAN ABIY WAQAS (L) AL-IJLIYYU YACE YAKASANCE YANA YIN RIWAYAR HADISAI DAGA BABANSA, HAKA KUMA MUTANE SUNAYIN RIWAYA DAGA GARESHI. SHI TABI'I NE AMINTACCE SHINE MUTUMIN DAYA KASHE HUSAINI (A) (DAN FADIMA (A))…

JAMA'A INA AMINCI YAKE CIKIN MUTUMIN DAYA BADA UMARNI DA AKSHE DAN 'YAR MANZON ALLAH (S.A.W.)?



لمازة1" بن زبار الأزدي الجهضمي أبو لبيد البصري ... ذكره بن سعد في الطبقة الثانية من أهل البصرة وقال سمع من علي وكان ثقة وله أحاديث وقال حرب عن أبيه كان أبو لبيد صالح الحديث وأثنى عليه ثناء حسنا... وقال موسى بن إسماعيل عن مطر بن حمران كنا عند أبي لبيد فقيل له أتحب عليا فقال أحب عليا وقد قتل من قومي في غداة واحدة ستة آلاف وذكره بن حبان في الثقات وقال عباس الدوري عن يحيى بن معين حدثنا وهب بن جرير عن أبيه عن أبي لبيد وكان شتاما قلت زاد العقيلي قال وهب قلت لأبي من كان يشتم قال كان يشتم علي بن أبي طالب
 

LAMAZATU DAN ZABBAR …SIQANE SUNCE SHI MANAGARCIN HADISI NE SANNAN KUMA GA KYAK-KYAWAN YABO DAYA SHA… MADRU YACE MUN KASANCE AWAJEN SHI ABIY LABIYD SAI AKACE DASHI KANA KUWA SON ALI? SAI YACE NA KUWA SO ALI ALHALI YA KASHE DAGA CIKIN MUTANE NA CIKIN SAFIYA GUDA MUTUM DUBU SHIDA. IBN HIBBAN YA AMBACE SHI DAGA CIKIN AMINTATTU. WAHB DAN JARIYR DAGA BABANSA DAGA ABIY LABIYD YAKASANCE MAI ZAGINE… NACE WA YAKE ZAGI SAI YACE YAKASANCE YANA ZAGIN ALIYU BN ABIY DALIB… DUBA TAHZIYBUT-TAHZIYB.8/410.

399- أسد ابن موسى ابن إبراهيم ابن الوليد ابن عبدالملك ابن مروان الأموي أسد السنة صدوق يغرب وفيه نصب من التاسعة مات سنة اثنتي عشرة وله ثمانون خت د س

ASADU DAN MUSA ABIN YIWA LAKABI DA ASADUS-SUNNAH MAI GASKIYA NE YANA ZUWA DA GARIBAN ZANTUKA ATARE DASHI DA AKWAI NASIBANCI (KIN ALI(A)) TAQRIYBUT TAHZIYB.1/104. ASADUS-SUNNAH???

DAGA KARSHE ZAN CIKASHE DA FADIN IBN HAJR AL-ASQALANIY DAKE CIKIN LITTAFIN TAHZIYBUT-TAHZIYB.29/5. DAKE CEWA :

وقد كنت استشكل توثيقهم الناصبي غاليا وتوهينهم الشيعة مطلقا ولا سيما أن عليا ورد في حقه لا يحبه إلا مؤمن ولا يبغضه إلى منافق ثم ظهر لي في الجواب عن ذلك أن البغض ها هنا مقيد بسبب وهو كونه نصر النبي صلى الله عليه وسلم لأن من الطبع البشري بغض من وقعت منه إساءة في حق المبغض والحب بعكسه

SHI KANSA IBN HAJR ABIN YANA RIKITAR DASHI WAJEN SIQANTA NASIBI MAKIYIN IMAMU ALI (A) DASUKEYI TARE DA RAUNATA DAN SHI'A KAI TSAYE DASUKEYI. BALLANTANA KUMA GASHI YAZO ACIKIN HAKKIN ALI (A) BABU MAI SONSA SAI MUMINI, BABU MAI KINSA SAI MUNAFUKI. SANAN SAI YA BAYYANA AGARENI CIKIN JAWABIN HAKA SHINE KIN ALI (A) DA AKEYI ANAN YANA TATTARE DA SABABI, SHINE KASANCEWARSA YA TAIMAKI ANNABI (S.A.W.)  SABODA YANA DAGA DABI'AR DAN ADAM KIN MUTUMIN DAYA MUNANA MASA CIKIN HAKKIN WANDA AKA MUNANAWA , SO KUMA YANA AKASIN HAKA….

ASHE BABU MAMAKI CIKIN FADIN WADANCAN MUTANE CEWA GA DALILINSU NAKIN IMAMU ALI (A) WAI DON SABODA YA YAKI IYAYENSU.SAI DAI KUMA CEWA MUSANI ABINDA IMAMU ALI (A) YA AIKATAWA IYAYEN WADANCAN MUTANE YA KASANCE NE DA UMARNIN ALLAH DANA ANNABINSA. SABODA HAKA MUSANI IYA FITOWA FILI NE BAZUSUYI BA SUCE SUNA KIN MANZON ALLAH (S.A.W.) SABODA HAKA SAI SUKE FAKEWA DAKIN MUTUMIN DAYAKE KINSA KIN MANZON ALLAH NE, ZAGINSA ZAGIN MANZON ALLAH NE, YAKARSA YAKAR MANZON ALLAH NE.

ALHAMDU LILLAHI.

Monday, 15 July 2013

RADDI AKAN MASU KARYATA AUREN MUTU'AH



Daga sheikh Nuru Darus-thaqalaini
Salaamun alaa manit-taba'al-hudaa.

TSOKACI AKAN MAGANGANUN AMMAR ABU TURAB [AL-MUZAWWAR]

Duk mai karatu, kuma ya ke da lura da fahimta da kuma hankalin da Allah ya tanadar masa don tantance gaskiya da qarya, haske da duhu, ko da kuwa bai da ilimi, ya san inda wannan tattaunawa ta fuskanta, ta inda qoqarin da Ammar Abu Turab (Al-muzawwar) ya yi na qwatar xan'uwan Malam Rabi'u bai haifar da wata natija ta hankali ba, balle ma ace ta ilimi, domin ba bu komai a cikin wannan rubutu na sa face maimaici ba komai. Domin dukkanin maganganun na sa xan'uwansa ya kawo mafi jullinsu, kuma mun kawo warwararsu har waxanda shi kansa Malam Rabi'un bai kawo ba. Ya jama'a masu hankali shin wannan ba za mu iya kiransa da vata mana lokaci ba da rashin aikin yi? Ko kuwa irin halin da kuka saba ne da kuyi ta maimaita abu xaya don ku kautar da abinda muke kawowa na tsantsar gaskiya da hujja yankakkiya?!

Alaa ayyi haalin, wannan bai gajiyar da mu wajen sake fitowa da jama'a abin da ya tabbata na gaskiya. Don haka zamu bi maganar Ammar mu xauki masu dama-dama, waxanda ba shirme ba bu maimaici mu fitowa da jama'a wasu nuquxoxi da ya kamata su riqe da suke tabbatar da halascin auren na mutu'a, ba haramcin ba.

Ammar ya fara da maimaici akan ruwayoyin Khaibara, waxanda duk maimaici ne akan maganganun da Malam Rabi'u ya kawo, ta inda tun a baya mun kawo "Tahqiiqaat wat-tanqiihaat" na manyan Malamansu masana ilimin Hadisi waxanda suka tabbatar da waxannan ruwayoyi na hanin auren mutu'a na Khaibara da irin jahilan Wahabiyawa ke riqo da su dukkaninsu na qarya ne, kamar yadda ya gabata a maganganunmu na baya da abin da kowa ya ce akan nuna Hadisan Khaibara na hanin mutu'a duk na qarya ne, mai son qarin bayani ya koma baya [http://www.facebook.com/notes/fayza-ummi-ahmad/raddin-da-mujaheed-nuruddeen-ibn-muhammad-yayi-akan-maganar-muhammad-rabiu-a-sha/167250780004934], wanda daga ciki mun kawo:

1-      Ibn Hajar mawallafin Fat'hul-baariy.
2-      Al-ayniy – daga Ibn Abdul-barr.
3-      Al-qisxalaaniy – daga Baihaqiy.
4-      Ibn Qayyim.
5-      Ibn Kathiir.

Wanda qo an qi ko an so kamar  yadda mu ka sha bayani, shi Hadisi ko Tarihi ya kan zamo tabbatacce kuma ingantacce ya yin da aka sami sanadinsa ya cika dukkanin qa'idojin inganci, sannan kuma da tantancewar Malaman Hadisi da suka tabbatar da ingancin Hadisi. Fat'hul-baariy xin nan kowa yasan Sharhi ne na Sahiihul-Bukhaariy wanda Ahmad bn Aliy Ibn Hajar, wanda aka fi sani da Asqalaaniy ya wallafa, kuma a ciki ya yi tahqiiqi ya tabbatar da waxannan Hadisai da suka nuna hanin auren Mutu'a a Khaibara duk na qarya ne ba su tabbata ba domin ba bu wanda ya san waxannan ruwyoyi daga Malaman Siirah da masu naqalto Hadisi. Haka nan ma sauran Malaman duk Tahqiiqinsu ya na qaryata ruwayoyin Khaibara ne, ga misalign maganganun Malamai uku:
  • Ibn Hajar a cikin sharhinsa na Fat'hul-Baariy daga As-suhailiy yace: "Kuma wannan Hadisin yana tattare ne da tsoratarwa akan matsalolinsa; domin a cikinsa akwai hani akan auren mutu'a ranar Khaibar. Kuma wannan (hanin) babu wanda ya sanshi daga Malaman Sira da Ruwwatul-athar (Masu naqalto Hadisi)" (Malam sai aje a duba: Fat'hul-baariy 9/210).

  • Haka nan dai Malam Ainiy da sharhinsa yace: "Ibn Abdul-barr yace: Kuma ambaton hanin mutu'a a ranar Khaibar kuskure ne (Galax)" (Umdatul-qaariy: 17/246).

  • Haka dai Al-qisxalaaniy shi ma da sharhinsa yace: "Baihaqiy yace: ba bu wanda ya san shi daga cikin Malaman Sira (Tarihi)" (Irshaadus-saariy: 11/397, 9/232).

Shin 'yan'uwa na masu neman gaskiya Tahqiiqin waxannan gingima-gingiman Malaman zamu karva waxanda duniyar Sunna da su take alfahari da riqo, ko kuwa tahqiiqin irinsu Ammar, Rabi'u, za mu karva, waxanda ba bu wanda ya san Shuhurarsu akan wani Ilimi ko da a iya garinsu balle Qasarsu har kuma akai duniya?! Mutanen da na sha faxa su kansu "Muqallidai" ne, su ma riqo suke yi da waxannan Malaman, su kan su tunaninsu, hankalinsu ba hujja ba ne a kansu balle waninsu?! Mu dai akan Hadisan Khaibara na qarya da aka dangantawa Manzon Allah (S) da Wasiyinsa (A), tahqiiqin Malamanku da suka nuna duk na qarya ne ya ishe mu, ba mu buqatar naku 'yan aci a basu!


Ruwayoyin kuwa da Ammaru ya kawo akan haramcin auren mutu'a, ban ga fa'idarsu ba, domin mu da kanmu a rubutun na mum un kawo wasu daga ciki, kuma muka kawo ingantattu da suke karo da su. Wanda daga ciki ne shi Ammar ya kawo Hadisin Sabratal-juhaniy, sai dai abin tausayi shi kansa Malam Rabi'u ya kawo xaya daga cikin Hadisan Sabrata xin inda muka mayar masa da martini kamar haka:

"To amma da shi Malam Rabi'u idanuwansa sun kai kan waxannan Hadisan da suka zo a wannan lamba ta (1406) da bai yi hanzarin kawo shi a matsayin hujja ba. Saboda Hadisin farko ma na wannan lambar (1406) ko kuma a wata Xaba'ar Hadisi na (3485), yana nuna tsantsar halasci ne, kuma Manzon ne ma ya umarta a lokacin da aje ayi auren mutu'ar a wannan Yaqin, wanda qarshen maganar ma ga abin da Manzon (S) ya ce: "….. Duk wanda ya kasance a tare da shi akwai wannan matar ta mutu'a to ya sake ta". Shin ka sani ko fagen fama za'a faxa aka ce su sake su, ko kuwa gida za'a dawo?! Ga nan matanin Hadisin:

"وَحَدَّثَنَا قُتَيْبَةُ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا لَيْثٌ عَنِ الرَّبِيعِ بْنِ سَبْرَةَ الْجُهَنِىِّ عَنْ أَبِيهِ سَبْرَةَ أَنَّهُ قَالَ أَذِنَ لَنَا رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- بِالْمُتْعَةِ فَانْطَلَقْتُ أَنَا وَرَجُلٌ إِلَى امْرَأَةٍ مِنْ بَنِى عَامِرٍ كَأَنَّهَا بَكْرَةٌ عَيْطَاءُ فَعَرَضْنَا عَلَيْهَا أَنْفُسَنَا فَقَالَتْ مَا تُعْطِى فَقُلْتُ رِدَائِى. وَقَالَ صَاحِبِى رِدَائِى. وَكَانَ رِدَاءُ صَاحِبِى أَجْوَدَ مِنْ رِدَائِى وَ كُنْتُ أَشَبَّ مِنْهُ فَإِذَا نَظَرَتْ إِلَى رِدَاءِ صَاحِبِى أَعْجَبَهَا وَإِذَا نَظَرَتْ إِلَىَّ أَعْجَبْتُهَا ثُمَّ قَالَتْ أَنْتَ وَرِدَاؤُكَ يَكْفِينِى. فَمَكَثْتُ مَعَهَا ثَلاَثًا ثُمَّ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- قَالَ « مَنْ كَانَ عِنْدَهُ شَىْءٌ مِنْ هَذِهِ النِّسَاءِ الَّتِى يَتَمَتَّعُ فَلْيُخَلِّ سَبِيلَهَا".

Shi wannan Hadisin da aka ruwaito shi daga Sabratal-Juhaniy ya na da hanyoyi da yawa wasu Hani wasu Halasci, waxanda Muslim da wasunsa sun fitar da su daga Ma'abota Sunan da Musnad, wanda akwai ruwayar da ta ke nuna Hanin ya faru ne a Fat'hu Makkah wato a watan Ramadhaan a shekara ta takwas bayan Hijira".

Sai Hadisin da shi Ammar xin ya kawo na ruwayar Iyaas bn Salamah bn Ak'wa'u, wanda shi kansa tun kafin Ammar xin ya kawo su shi ma mun kawo shi kuma mun yi magana akan sa, inda muka ce:

" Sannan akwai wata ruwayar  daban da aka fitar da ita daga Muslim a cikin Sahihinsa, daga Iyaas bn Salamah bn Ak'wa'u daga Babansa ya ce: "Manzon Allah (S) ya yi rahusa a shekarar "Auxaas" a cikin Mutu'ah sau uku sanan ya hanata".

To abin lura anan shi ne shekarar "Auxaas" shi ne dai shekara ta takwas bayan Hijira, don haka anan akwai rikitarwa da kuma tanaqudi mai ban mamaki ta inda ya tabbata da Hadisan da ma su wannan magana suke quduri da su akan shafewar Halascin, aka Mutu'ah ta kasance Halas har lokacin "Hajjatul-wadaa'i" wato shi ne shekara goma (10) bayan Hijira. Ga Hadisin da ke tabbatar da hakan akan Auren mutu'ar yana nan da Halascinsa har shekara goman bayan Hijira:

Malam Daaramiy ya fitar da shi a cikin Sunan xinsa yace: "Ja'far bn Awn ya bamu labari daga Abdul-Aziiz bn Umar bn Abdul-Aziiz daga Rabii'u bn Sabrata daga Babansa ya bashi labari akan sun kasace tare da Manzon Allah (S) a Hajin ban kwana sai yace: "Ku yi mutu'a daga waxanan matayen, domin mutu'a a wajenmu Aure ne (Wannan maganar kuwa tana dukan bakin masu cewa ba aure ba ne), …………….. [har inda Manzo (S) ya ke ce wa] …. Sai yace: ya ku mutane haqiqa Ni ne na yi muku izini akan yin auren mutu'a da mataye, to ku sani haqiqa Allah ya haramta shi har zuwa tashin Alqiyama …….." (Sunanud-Daaramiy: 2/140)".

Inda mu ka qare da wannan maganar:

"Don haka wannan ruxanin ya afku akan wannan ruwayar yana daxa tabbatar da qaryar Hadisin da ke nuna Hanin, sannan ma kuma ga wasu tilin Hadisan da suke nuna qarya ake yiwa Annabin Allah (S) akan wai ya Hana, dukkanin Sahabbai sun tafi akan Umar xan Haxxabi ne ya hana, kuma ba su yarda da wannan Hanin nasa ba saboda sun san savawa ne da Qur'ani da Sunnar Manzon Allah (S)".

Wanda a bisanin wannan ne ma muka goye da: [KAXAN DAGA CIKIN HADISAN DA SUKE KARO DA WANNAN HADISIN NA HANI].

INDA A WANNAN HADISAN NE MUKA KAWO HADISAI TABBATATTU INGANTATTU DAGA MANYAN MALAMAN SUNNA XIN DA SUKE GOGE DUKKANIN WANI HADISI MA DA YAKE NUNA ANNABI (S) NE YA HARAMTA MUTU'A, ga kaxan daga ciki:

  • Malam Muslim ya fitar a babin "Nikaahul-Mut'ati" ruwayoyi da yawa daga Jaabir bn Abdullah, da Abuz-Zubair, cewar su sun yi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi), da zamanin Abubakar, har lokacin da Umar xan Haxxabi ya hana.

  • A cikin Sahihul-Bukhari kuwa cewa yayi: an saukar da Ayar Mutu'a a cikin littafin Allah, mun aikata ta tare da Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) kuma Qur'ani bai sauka yana haramta ta ba kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) bai hana ba har ya Rasu. Sannan wani mutum kawai yazo ya faxi son ransa. (Sahihul-Bukhari: 5/185).

  • Wani dalilin daban akan rashin shafe ta shi ne Shaharar ta (Mutu'a) ga Sahabbai da Tabi'ai da "Fuqahaa'u" Malamai, har zuwa lokacin da Mazahabobi huxu suka kasance suna bayyana ta a fili a Qarnoni na biyu na uku da na huxu.

Shaida akan haka kuwa shine abinda  Malam Bukhari da Malam Muslim a ingantattun litattafansu na Hadisi suka ruwaito na ruwayoyi daga Salamah binul-Ak-wa'u bn Mu'iid, da Jaabir bn Abdullahil-Ansaariy, da Abdullahi bn Mas'uud, da Ibn Abbaas, da Sabrata bn Mu'iid, da Abu Zarril-Gifaari, da Imraana bn Hasiin, da Ak'wa'u bn Abdullahil-Aslamiy. (duba: Sahih Muslim Sharhin Nawawiy: 9/179 – 189, da Sahihul-Bukhari Kitabut-Tafsir Babi na 33 Hadisi na 4156, da Kitaabun-Nikaah babi na 32 Hadisi na 4724, da Kitabul-I'itisam babi na 28 Hadisi na 6819).

WANDA NI NURU "Ar-raafidiy" INA FAXA DA BABBAR MURYA IDAN WAHABIYAWA ZASU CIKA DUNIYAR NAN DA HADISAN QARYA DA SUKE CE WA WAI ANNABI (S) YA HARAMTA MUTU'A, TO IYA WAXANNAN HADISAN DA MAGANGANUN MANYAN MALAMANKU XIN NAN DA NA KAWO NAN SAMA KAXAN SUN GOGE HADISANKU NA QARYA, KUMA SUNA TABBATAR DA HALASCI AUREN MUTU'A NE TUN DAGA RANAR DA AKA HALASTA TA HAR TASHIN ALQIYAMA!

Maganar kuwa da Ammar ya ke faxa wai "MUTU'A ZINA CE, IN JI MAGABATAN WANNAR AL'UMMA", wallahi wannan ba komai ya ke nunawa ba illa qarancin hankali da ilimi. Su waye magabatan?! Umar bn haxxabiy da 'Yan barandarsa ne magabatan?! Akwai wani magabaci da ya wuce Annabi Muhammad (S)?! manzon Allah (S) y ace Mutu'a halas ce, kuma har ya yi wafati ya bar abin a hakan ga shi nan da shaidar Sahabbai suna tabbatar da ce wa Manzon Allah (S) ya yi wafati ya bari ana yin auren Mutu'a amma wani mutum ya zo da ra'ayinsa ya ce haram ce. Shin wanan ba fito na fit one da Annabi (S) ba?! Shin wannan ba nuna Annabi (S) bai iya ba ne Umar shi kaxai ne ya iya?! Shin ba wannan Ubangij qarara ya hana ba a cikin Qur'ani magirma?! Shin Allah bai hanin; Ubangiji ko Annabinsa su ce ga hukuncin abu wani daban ya ce ga wanda ya fib a?!

Allah maxaukakin Sarki ya na faxa a cikin Suratul-Ahzaab aya ta (36):

" وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا"
Ma'ana:
"Kuma ba ya halasta ga Mumini ko kuma Mumina, idan Allah da Manzonsa suka zartad (Hukunta) wani lamari, wasu suce ga nasu zavin ba na Allah da Manzonsa, wanda kuwa duk ya savawa Allah da Manzon (Cikin umarni, cikin zavi,……) tabbas wannan ya vata vata mabayyani".

Shin ya halasta ga wani ko waye shi, Annabin Allah ya ce abu halas ne shi kuma ya ce haram ne?! wallahi summa tallahi duk wanda kuwa ya aikata wannan to yana daga cikin waxanda wannan aya ta yi musu tambari da vata!

Shi kansa Oga Uban tafiyar ya yarda da cewar Mutu'a Halas har Manzon Allah (S) ya yi wafati, shi ne da son iyawarsa, wataqila ko ya manta da wannan ayar ce, shi ya sa ya ce ya haramta abin da Annabi ya halasta. Inda ya ke ce wa:

"متعتان كانتا على عهد رسول الله (ص) أنهى عنهما وأعاقب عليهما متعة النساء ومتعة الحج"
Ma'ana:

"An kasance ana yin Mutu'a guda biyu zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) to ni na hana kuma zanyi azaba akansu, Mutu'ar Aure da Mutu'ar Hajji" (Sharhul-Ma'aanil-Athar: 2/146, Malam Ahmad bn Muhammad bn Salmatul-Azdiy).

Amma sai ga shi su Ahlus-sunna xin sun saki hani xaya daga hani biyun da Umar xin yayi sun kama xaya. Domin kuwa har yanzu suna riqo da Mut'atul-haj, wato Hajin Tamattu'i, bayan shi gaba xaya biyun ya hana, wannan wane irin son rai ne?!

Tabbas da ace akwai wani abu dake nuna shafewar daga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da ya xan jona shi a maganar sa, da bai tsaya danganta abin gare shi shi kaxai ba. Don haka a kan kansa, maganganun shafewar inkarin maganar Halifan ne.

Haka nan dai a cikin waxanda suka fitar da wannan Hadisin na maganar Umar xin:
1-      Littafin Ma'rifatus-sunan wal-aathaar na Baihaqiy a babin auren mutu'a.
2-      Haka nan da littafin Sunan Sa'iid bn Manzuur, a babin "Maa jaa'a fil-mut'ah".
3-      Jaami'ul-ahaadith a babin "Musnad Umar bn Khaxxaab".

Shin hanawar Umar bn Haxxabiy a matsayin shi kansa ya savawa Annabi (S) ne, shi ne zai zamar da Halas xin Annabi (S) haram?! Ko kuwa shi ne zai zamar da auren mutu'a zina?!

Shi kansa Umar da ya nuna da bakinsa an kasace ana yin auren mutu'a a zamanin Manzon Allah (S) shi ne ya hana a bayan Halifa Abubakar, sannan a qarshen zamaninsa (Wanda wannan shi ne abin da sukkanin Malaman duniya suka yi ittifaqi akai, na Umar ne ya hana). To ku Wahabiyawa ku sani lokacin da Umar xan Haxxabi ya zo mutuwa sai da ya kasance yana qarfafa cewar irin waxannan karan-tsaye da sassavawa Annabi da ya yi, da faras da sababbain abubuwa da ya yi a bayan Annabin (S), za su iya kai shi ga faxawa azabar Allah.

Ku je ku duba cikin Sahiihul-Bukhaariy a babin da ya ke magana akan darajojin Umar, sai Buhari ya kawo wannan Hadisin:

Hadisin na nan garau a cikin Buhari a juzu'insa na 12, shafi na 454, Hadisi na 3692: daga Miswar bn Makhramata yace; "Ya yin da aka soki Umar (Xan Haxxabi) ya kasance yana jin raxaxi, sai Ibn Abbaas yace masa – kamar yana nuna masa damuwarsa – ya Amiirul-muminina, yaya haka (kake cikin wannan ximuwar mutuwar) bacin ka abokanci Manzon Allah (S) kuma ka kyautata abokantakarsa, sannan kuka rabu da Shi yana mai yarda da kai, sannan ka abokanci Abubakar ka kyautata abokantakarsa, sannan kuka rabu yana mai yarda da kai, sannan ka abokanci Sahabbansu ka kyautata abokantarsu, wanda kuma idan zaka rabu da su zaka rabu da su ne suna masu yarda da kai. Sai (Umar) yace, amma abin da ka ambata na abokantakar Manzon Allah (S) da yardarsa, to haqiqa wannan Baiwa ce daga Allah yayi min Baiwa da ita, amma kuma abin da ka ambata na abokantakar Abubakar da yardarsa, to haqiqa shi ma Baiwa ce daga Allah yayi mini Baiwa da ita, amma abin da kake gani na wannan damuwar tawa da firgici (Jaza'u), yana daga cikin sakamkonka da sakamakon abokanka (wato abin da ya farar a tsakaninsu bayan Manzon Allah ya yi wafati na canja hukuncin Annabi daga Halas ya koma Haram – kamar auren mutu'a, da kuma daga Haram zuwa Halas – irin su Sallar Tarawi da qiyamul-lail a jam'i, ………. ), (sai Umar yace) wallahi da ina da Zinare wanda yawansa zai cika sama da qasa da na bada shi fansar azabar Allah Maxaukakin Sarki tun kafin na ganShi" .

A gefe guda kuma ga Aya tana cewa:

"Haqiqa waxanda suka ce, Ubangijinmu Shi ne Allah, sannan suka tsaya cak akan hakan, Mala'iku na sauka garesu (yayin mutuwarsu), (suna ce musu) kada kuji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ana yi muku bushara da aljannar da aka kasance ana yi muku alkawari" (fussilat: 30).

Wanda anan  take zaka ga mutum yana murmushi a xauke ran nasa ma bai sani ba. To wannan fa shi ne qarshen canja Umarni ko Hukuncin Annabin Allah.

Shin tarin Hadisai ba su zo ba a cikin Buhari da Muslim a babukan "Kitaabul-fitan", a inda Manzon Allah (S) ya ke gayawa Sahabbansa yake cewa a ranar alqiyama za a zo mini da wasu mutane (daga cikinku) sun sanni Ni ma Na sansu, ina bakin tafikina na alkauthara na yi haka zan xebo rowan na ba su, sai a jayesu daga gare Ni, sai nace ya Ubangiji, waxannan fa Sahabbai na ne, Sai a Ubangiji yacewa Annabi sun canja addini a bayanka, sai Manzon Allah (S) yace musu shi ma: "Suhqan suhqan liman baddala wa gayyara ba'diy".

Haba jama'ar Wahabiyawa shin duk wannan bai isheku izna ku gane ga babban Limamin naku ya yi furuci da bakinsa ya canja Umarnin Annabi, yace ana yi a zamanin Manzo, amma ni na hana, kuma ga shaidar da ya bayar da bakinsa da zai mutu, kuma ga Hadisan da kuka ruwaito akan mai canjawa da jirkita addini ba, ku sake shi ku zo ku kama Ahalulbayt ba, waxanda Annabi ya basu Tahqiiqi akan ba za su rabu da Qur'ani ba har tashin qiyama ba?! Ku saki waxancan tarkacen da ko a yaqin Uhudu yaqi ya shaede su akan zasu cika da imani ba! Yakamata fa jama'a ayi hattara!

MAGANA KUWA AKAN ZINA.

Amma Magana akan cewa tayi kama da zina ko Mutu'a Zina ce to lallai wani babban haxari ne, koda kuwa an shafe hukuncin halascin balle kuma ba'a shafe ba. Domin kuwa yana nufin ne Mai Shari'a Mai Tsarki (Ubangiji) ya halasta Zina sannan ya haramta ta. Shin Musulmi zai yarda da wannan?!

Ya riga ya gabata cewar auren Mutu'a aure ne kamar auren Da'imi, yana da Sharaxai da Qa'idoji, sune: Xaurin aure, da bada Sadaki, da sanya Lokaci, da Hankali, da Balaga, da rashin samun wani hanzari na Shari'a da zai hana, kamar Nasaba, ko wani dalilin ko an sha Nono tare, ko wani abu makamancin haka. Amma a Zina kuwa ba a Xaura aure, Xa bashi da dangantaka da Mahaifinsa, bazai Gade shi ba, babu wata alaqa ta aure, babu Idda a cikin Zina. Don haka kwatanta ma Mutu'a da Zina wata vatacciyar Maganace, wanda mai faxarta ma wani Wawa ne marar tunani da dalili da son jayayya.

E, yana iya yiwuwa wasu suce shi auren Mutu'a an Shar'anta shi ne abisa domin samun wata fa'ida vangaren yasassiyar zuciya da raunananniya.

Jawabi anan shine: Ita Duniya cike take da abubuwa bayyanannu masu kyau da ke tsaye kyam wajen amfanar da xai-xaikun abubuwa marasa kyau. (Misali, idan muka xauki kamar Wutar Lantarki, zamu ga anyi ta ne don wata fa'ida ga Al'umma, shine; suga Haske, su kunna Na'urori, da sauran su. Amma a vangare daban sai muga tava ta da Hannu ko Jiki kan iya aikawa da mutum Lahira nan take. To shin zai yiwu ace don wannan dalili kwata-kwata ace an hana amfani da Wutar Lantarki? Ko kuma idan muka xauki Batirin mota zamu ga ai don amfanin da aka yi shi, to yaya idan mutum ya zuba a Ido ko uwa-uba ya sha? Shin shima don haka kwata-kwata sai ace a daina yin ruwan Batir gaba xaya?).

Wanda mafita a kwatankwacin wannan yanayi ba wai sai an haramta ainihin gundarin abin ba. Abin da yake kawai shine samar da wasu hanyoyi na vangaren halastawa tsakanin waxannan fitattun abubuwa masu kyau dake taimakawa ko fa'idantar da abubuwa marasa kyau. Don haka da samuwar Mai Shari'a na Musulunci (Mujtahidi) sai ya sharxanta wasu sharaxai na zamani na dole wajen yin auren Mutu'ar, don kuvutar da wannan halascin Shari'a daga waxancan vatattun.

Hakane abinda yazo mana valo-valo na daga Nassosin Qur'ani mai Girma da Sunnar Manzon Tsira (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Nassosin Sahabbai da Tabi'ai na tabbatar da Shar'ancin auren Mutu'a gaba xaya. Da rashin tabbatar shafewar hukuncin nasa daga mafi yawan Sahabbai da Tabi'ai. Hakan ma a gurin Ahlul-Bait Tsarkaka, sune "Aliyyu" Sayyidul-Awsiyaa' da 'Yayayensa Imamai Ma'asumai (Alaihimus-salam su goma sha xaya) da Malaman Makarantar su ta Fiqhu xaya bayan xaya.

Auren Mutu'a aurene halastacce ga Shar'a kamar auren Da'imi a Shari'a ta Musulunci, wanda ya xan sava a wasu hukunce-hukunce waxanda muka ambata a baya.

Amma kuma ruwayar Umar xan Haxxabi ba wata abar dogaro bace wajen shafe hukuncin auren Mutu'a kamar yadda ya tabbata abaya daga bakunan su kansu Sahabbai da Tabi'ai xin. WANDA yana daga ciki irin raddin da xansa abdullah yayi masa da aka yi masa tambaya akan menene matsayinsa akan auren mutu'a, yace; halas ne. aka ce masa me zai ce ga maganar babansa (umar xan haxxabi) da ya haramta? ya ce shin umarnin babana zan bi ko kuwa umarnin manzon allah?! (bukhari).


Idan kuwa mu ka komo maganar da Ammar ya ke faxa akan Ayar "Famastamta'tum bihi minhunna fa'aatuuhunna ujuurahunna fariidhatan", to ga abin da mke faxa anan a xan faxaxe bad a tsayi ba:

Allah Ta'ala yace:

"فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً"
Ma'ana:

"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, wajibi ne ku basu ladan su (Sadaki)".

Abin da kaxai muka ce akan Malam Xabariy shi ne: a cikin Tafsirinsa Al-Kabiir ya fitar, haka nan Malam Zamakhshari cikin litttafin sa Kashshaaf, sannan Malam Raaziy a Tafsirinsa, sai Sharhin Muslim na Nawawiy a farkon Babinsa na auren Mutu'a cewar: Ubayyu xan Ka'abu, da Ibn Abbas, da Sa'iid xan Jubair, da Ibn Mas'uud da Saddiy suna karanta wannan Aya ne da:

"فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"

Su suna qara kenan:
"إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"
Ma'ana:

"Izuwa qayyadajjen lokaci"

Sannan waxannan Malamai dukkanin sun qarfafa cewar wannan Ayar ta sauka ne akan Mutu'a: Malam Ahmad bn Hanbali a Musnadinsa, hakanan ma Malam Abubakar Al-Jassas cikin Al-Ahkamul-Qur'an, da Malam Abubakar Al-Baihaqiy cikin Sunanul-Kubra, da Malam Al-Qaadiy Al-Baidaawiy a Tafsirinsa, da Malam Ibn Kathiir a nasa Tafsirin, da Malam Jalaaluddin Suyuuxiy a Durrul-Manthur, da Malam Al-Qaadiy Ashshaukaniy a Tafsirinsa, da Malam Shihaabuddin Aluusiy a Tafsirinsa, da Sanaduddukan da suke qarewa da irin su Ibn Abbas, da Ubayyu xan Ka'abu, da Abdullahi xan Mas'ud, da Imrana xan Hasiinu, da Habibu xan Abi Thaabit, da Sa'idu xan Jubair, da Qutaadatah, da Mujahid.

Don haka a rubutunmu babu inda muka kawo Xabari akan yana daga cikin masu qarfafawa akan ta sauka ne akan auren mutu'a, don haka Ammar sai a sake wata yaudarar.

Bazai iya yiwuwa ace an fassara wannan Aya da cewa tana Magana ne akan auren Da'imi ba, kamar yadda mai Tafsirul-Manar ya qarfafa. Dalilin kuwa da yasa hakan bazai yiwu ba shine, zuwan waxannan dalilai:

1-      Abinda ya gabata na daga wani adadin Sahabbai dake karanta wannan Aya da:

"فما استمتعتم به منهن - إلى أجل مسمى - فآتوهن أجورهن فريضة"
Ma'ana:

"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, izuwa wani qayyadajjen lokacin da aka ayyana, wajibi ne ku basu ladan su (Sadakin su)".

Tare da gwamin jumla mai yin bayani qarara a tsakiya wato:

"إلى أجل مسمى"

"Zuwa wani qayyadajjen lokaci" 

Wanda buqatar su akanta shine bayyana ma'ana da bigire da fassarar ta. Sannnan wannan jumla bayyananna ba zata tava dacewa da auren Da'imi ba face Mutu'a.

2-      haqiqa lafazin "Mutu'a" koda ya kasance dai-dai ko ingantacce akan amfani ko nufin ma'anar auren Da'imi, to amma yafi fitowa valo-valo a sarari akan nufin auren Mutu'a ne. kamar yadda lafazin "Nikaah" koda ya zamanto dai-dai da inganci wajen amfani ko nufin auren Mutu'a, to abinda shima yake valo-valo a sarari shine ana nufin kai tsaye auren Da'imi ne. wanda idan da babu wata alama a sarari, to da bazai yiwu a yarda akan tana nufin auren Mutu'a bane. A sannan sai ya zamo wani lafazi ne dake iya karvar sama da ma'ana guda xaya kenan.

3-      Haqiqa Ayar mutu'a tazo ne cikin Suratun-Nisaa' wacce ta fara da ambaton "An-Nikaah" wato aure da auren Da'imi, da hukuncinsa a cikin Ayoyi na 3, da 4, da 20, da na 23. Idan har ya kasance abinda ake nufi da "Al-Mutu'atu" shine auren Da'imi har wala iyau to da wannan Aya ta zamo maimaici na neman ambaton abinda ya gabata cikin Surar.

4-      Da kuma "Al-Mutu'atu" ta zamo da ma'anar aure ne na Da'imi, to ina amfanin quduri da "An-nuskhu" (wato an shafe ta) kenan? Ko kuwa suna nufin "Nuskhu" da an shafe hukuncin auren Da'imi ne?! To don haka Magana akan "An-Nuskhu" cewar an shafe hukuncin auren zai zamo wani qarfafane akan Ayar Mutu'a, cewar tana nufin Aure ne "Al-mu'aqqit" ai abin yiwa lokaci (Mutu'a) bawai Da'imi ba wato auren mutu-ka-raba.

Amma Magana akan "An-nuskhu" na sha faxa muku ba'ayin Nuskhi a bayan wafatin Annabi (S), domin Wahayi ne dai yake sauka ace an shafe kaza da kaza, to kuwa tun da Annabi ya yi wafati ba'a sake yin Wahayin da za'a isar da saqon Allah ga wasu ba. Su kuwa dukkanin Nuskhu xin nan da yake zuwa a cikin litattafanku na Hadisai, Sahabban suna ruwaitowa akan sun kasance tare da wannan Aya ne ko Qiraa'a tun a zamanin Manzon Allah (S), yanzu kuma bayan wafatinsa sunga babu ita, to waye ya gayawa su su Xabarin an shafeta, wallahi sai dai idan Shaixan ne ya yi musu Wahayi!

Don haka daga qarshe nake rufewa da tunatarwa akan waxannan ingantattun Hadisai daga manyan litattafan Sunna da suke daxa tabbatar da halascin auren mutu'a da babu wata hujja ta nassi ko ta sharhi ko hankali da za ta iya tashin waxannan ingantattu da tabbatattun Hadisai.

1-      ….. Daga Jabir, yace: "Mun kasance muna auren Mutu'a, a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), da zamanin Abubakar, sannan daga baya Umar xan Haxxabi ya hana ….. (Sahihul-Muslim: 4/131, Musnad na Ahmad: 6/405, Fat-hul-Bari: 9/149).
2-      ….. Daga Ibn Abbas: Haqiqa Ayar Mutu'a hukuntacciya ce ba shafaffiya ba. (Al-Kasshaf: 1/498, Al-Ghadir: 6, Al-Khazin: 1/358).
3-      ….. Munyi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) da zamanin Abubakar da rabin zamanin Umar xan Haxxabi sannan daga baya Umar xan Haxxabi ya hana mutane yi. (Bidayatul-Mujtahidi: 2/58, da Al-Ghadir: 6/223 da 207).
4-      ….. Daga Al-Hakim, da Ibn Juraih da wasunsu, sunce: Aliyyu yace: da ba don Umar xan Haxxabi ya hana yin auren Mutu'a ba da babu wanda zai yi zina sai "Shaqiyy" wato ma'ana sai "Qalil" wato mutane kaxan, a wata fassarar kuma akace sai dai Xan iska, amma waccen fassarar ta "kaxan" tafi qarfi. (Tafsirux-Xabari: 5/9, da Tafsirur-Razi: 10/50, da Durrul-Manthur: 2/140).
5-      ….. Daga Imran xan Hasinu, yace: An saukar da ayar Mutu'a cikin littafin Allah Ta'ala, sannan wata Ayar bata sauka mai shafe ta ba, kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) yayi mana umarni da yin auren Mutu'a, kuma munyi Mutu'a tare da manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi), sannnan ya Rasu bai hana mu aikata ta ba, sannan wani mutum ya faxi abin da ya so na ra'ayin sa. (Sahihul-Bukhari: 2/168 da 6/33, Sahihul-Muslim: 4/48, Sunanin-Nisa'i: 5/155, da Musnadin Ahmad: 4/426, abisa ingantaccen Sanadi).
6-      ….. Daga qarshe Ibn Juraih shi kaxai ya ruwaito Hadisai goma sha xaya akan halascin auren Mutu'a. (Nailul-Auxar: 6/271, Fat-hul-Bari: 9/150).

Hadisai da Nassosi suna tabbatar da abinda Ayoyi masu Girma suka nuna ne na halascin auren Mutu'a da dawwamamman hukuncin sa har zuwa tashin Al-qiyama. Domin kuwa haramcin ya samu ne daga Umar xan Haxxabi - bawai daga manzon Girma ba (Sallallahu alaiHi wa Alihi). A irin vangare na Makarantar Sunna zai iya yiwuwa ace sun bi hani ko umarni na Halifa Umar a wannan bigire da yayi hani akan auren Mutu'a, da ace ba a sami Aya ko Hadisi da yake umarni akan halascin sa ba. Amma samuwar Aya da Hadisai barkatai sun yanke musu hanzarin riqo da wannan hani na sa, domin kuwa karo ne da Qur'ani da Hadisin wanda shine mai isar da wannan saqo na Musulunci, wato Annabi Muammad (Sallallahu alaiHi wa Alihi). Don kuwa haqiqa wasu tarin Mutane daga Sahabbai da Tabi'ai kai har ma da Abdullahi xan Umar, da Halifa Umar xan Haxxabin kansa sun ci gaba akan halascin auren Mutu'ar ba haramcin sa ba.

Sannan a vari xaya kuma dukkanin Mabiya Mazhabin Shii'ah sun tafi akan halascin ba haramcin Umar xin ba!!!