IMAM KHUMAINI (R.A) DAGA HAIHUWA ZUWA WAFATI
A
ranar ashirin ga watan Jimada al-Thani 1320 hijira Kamariyya, wadda ta
yi daidai da 30 ga watan Shahribar 1281 hijira shamsiyya (24 ga Satumba
1902 miladiyya) aka haifi wani jariri a garin Khumain, wani gari da ke
lardin tsakiyana Iran. Iyayensa dai mutane ne masu tsoron Allah, masana
ilmummukan Musulunci wadanda kuma suka fito daga zuriyar Nana Fatima
al-Zahra (a.s) inda suka sanya masa suna Ruhullah al-Musawi al-Khumaini.
Shi
dai wannan yaro ya gaji iyaye da kakanninsa ne wadanda daya bayan
dayansu suka dauki nauyin aikin shiryar da mutane da kuma neman ilmi.
Mahaifi marigayi Imam Khumaini (r.a) shi ne Marigayi Ayatullah Sayyid
Mustafa Musawi, daya daga cikin malaman da suka yi zamani da Ayatullah
al-Uzma Mirza Shirazi (r.a). (A bisa al'ada) mahaifin Imam Khumaini ya
tafi birnin Najaf na kasar Iraki don karatun addini inda bayan ya kai
matsayin ijtihadi (matsayin iya ciro hukumce-hukumcen shari'a daga
mabubbuga) sai ya dawo gida wato garin Khumain ya ci gaba da shiryar da
mutane a can. A lokacin Imam yana shekara biyar mahaifinsa ya yi shahada
sakamakon harin da aka kai masa a hanyarsa ta zuwa garin Arak saboda
irin nuna rashin amicewar da yake yi da zaluncin mahukunta na wancan
lokacin. Bayan wannan kisan gilla, danginsa da mutanen garin Khumain sun
fito don nuna rashin amincewarsu, bayan haka kuma suka wuce zuwa birnin
Tehran don isar da kukansu da bukatan da a zartar da hukumci (kisasi) a
kan wadanda suka aikata danyen aikin. Wannan kisan gilla da aka yi wa
mahaifinsa ya sanya Imam (r.a) tun yana karami ya fahimci dacin maraici
da kuma ma'anar shahada. Don haka mahaifiyarsa (Banu Hajar) ita ce ta ci
gaba da kula da kuma tarbiyantar da shi, kasantuwar ita ma ta fito ne
daga madaukakin gida don kuwa ita jika ce wa Ayatullah Khunsari
(marubucin littafin Zubdatul Tasanif) da kuma goggonsa (Sahiba Khanum).
To sai dai lokacin da Imam ya kai shekaru 15 a duniya ya rasa irin
wannan kulawa lokacin da wadannan masu kulawa da shi suka rasu.
HIJIRA ZUWA KUM, DON KAMMALA KARATU DA KARANTAR DA ILIMIN MUSULUNCI
Jin
kadan bayan hijirar Ayatullah al-Uzma Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri
Yazdi, Allah Yayi masa rahama, zuwa birnin Kum a farkon shekara ta 1300
hijira shamsiyya (Rajab 1340), Imam Khumaini shi ma ya yi hijira zuwa
makarantar Hawza ta Kum don ci gaba da karatunsa a wajen manyan malaman
garin. Karatun dai ya hada da karasa karatun littafin Mutawwal wajen
Mirza Muhammad Ali Adib Tehrani, da kuma karasa darasin "Sutuh" wajen
Ayatullah Sayyid Muhammad Taki Khunsari da Ayatullah Sayyid Ali Yathrebi
Kashani; da kuma fikihu wajen shugaban makarantar Hauzar Kum Ayatullah
Sheikh Abdulkarin Ha'iri Yazdi (r.a).
Bayan rasuwar Ayatullah
al-Uzma Ha'iri Yazdi, a bisa bukata da matsin lamban Imam Khumaini da
wasu manyan malamai na makarantar hauzar Kum, Ayatullah Burujerdi ya
dawo birnin Kum don ci gaba da kula da makarantun Hawzan garin a
matsayin shugaba. A daidai wannan lokaci kuwa ana ganin Imam Khumainin a
matsayin daya daga cikin manyan malaman da ake iya komawa gare su a
bangaren fikihu, Usul, falsafa, irfani da akhlak.
Shekara da
shekaru, Imam Khumaini ya yi yana karantar fa fikihu, Usul, sufanci da
akhlak a makarantun Hawza na Kum da suka hada da Makarantar Fa'iziyya,
Masjid al-A'azam, Masjid Muhammadiye, Makarantar Hajj Mullah Sadik da
kuma Masallacin Salmusi da dai sauransu. Har ila yau ya kuma karantar da
fikihu da sauran ilmummukan Ahlulbaiti (a.s) a masallacin Shaikh
al-Ansari (r.a) da ke Najaf na tsawon shekaru 14, inda a nan ne a karon
farko ya bayyanar da ra'ayin gwamnatin Musulunci cikin silsilar darussan
da yake bayarwa na Wilayatul Fakih.
IMAM KHUMAINI (R.A) A FAGEN GWAGWARMAYA
Ruhin
jihadi da gwagwarmaya a tafarkin Allah yana da tushe na akida da
tarbiyya da kuma ta zamantakewa da siyasa duk tsawon rayuwar Imam
Khumaini. Imam ya fara gwagwarmayarsa ne tun lokacin samartaka, kuma ya
ci gaba da hakan a bangarori daban-daban na kyautata ruhi a bangare
guda, a bangare guda kuma kan yanayi na siyasa da zamantakewar al'ummar
Iran da sauran al'ummomin kasashen musulmi. Rikicin da ya faru a
shekarun 1340-1341 hijira shamsiyya (1961-1962) kan (zaben) kananan
hukumomi ya kasance babbar dama ga Imam wajen jagorantar yunkurin
al’umma. Don haka, ana iya cewa, yunkurin gama-gari na malamai da
al'ummar Iran na 15 ga watan Khordad 1342 (5 Yunin 1963) ya kebantu da
wasu siffofi guda biyu su ne kuwa jagorancin Imam Khumaini da kuma riko
da Musulunci, wanda hakan ya zamanto matakin farko na yunkurin al'ummar
Iran wanda daga baya aka fi saninsa da sunan "Juyin Juya Halin
Musulunci".
Yayin da yake bayani kan abubuwan da ya tuna dangane
da yakin duniya na farko, duk da cewa lokacin da aka yi yakin yana da
shekaru 12 ne a duniya, Imam Khumaini yana cewa: "Lalle ina iya tuna
abubuwan da suka faru a yakukuwan duniya guda biyu…a lokacin ina karami
ne amma dai na kan je makaranta kuma ina ganin sojojin tarayyar Sobiyeti
a sansanin da muke da shi a nan (garin) Khumain. A yakin duniya na
farko a wasu lokuta akan kai mana hare-hare ma". A wani waje na daban
Imam Khumaini ya kasance ya kan ambato sunayen wasu daga cikin ashararan
da suke fakewa da hukuma wajen kai hare-hare da sace kayayyakin
al'umma, inda yake cewa: "Tun ina karami nake cikin yaki….muna cikin
mamayan Zulkawa da kai hare-haren Rajab'ali ne duk da cewa mu ma muna da
bindiga. Mu kan je kai dauki alhali a lokacin ina cikin shekarun
samartaka na ne. Mun kasance mu kan gina ramukan fakewa a inda muke… mu
kan shiga cikin wadannan ramuka muna fada da wadannan ashararai da suke
son kawo hari da mamaye mu".
A bisa wasu hujjoji na tarihi an
tabbatar da cewa gwamnatin Birtaniyya ne ta shirya da kuma goyon bayan
juyin mulkin da Ridha Khan ya yi a ranar 3 ga watan Esfand 1299 hijira
shamsiyya (1920). Duk da cewa an kawo karshen mulkin Kajariyawa da kuma
rage karfin mulkin ha’inai da ashararai, to amma dai ya haifar da wani
tsari na kama-karya da wasu ‘yan tsiraru ke mulkan mutanen wata kasa da
tsara musu makoma, inda 'yan gidan sarautan Pahlawi suka maye gurbin
ashararai.
A irin wannan hali nea, duk da irin musgunawa malamai
da gwamnatin lokacin da 'yan amshin shatan Birtaniyya da wasu 'yan boko
da aka saya suke yi, amma (malaman) sun tsaya kyam wajen kare Musulunci.
A wannan lokaci, bisa gayyatar da malaman Kum suka yi masa, Ayatullah
Hajj Shaikh Abdulkarim Ha'iri ya yi hijira daga garin Arak zuwa Kum.
Bayan wani lokaci kuma sai Imam Khumaini, sakamakon irin kokarin da yake
da shi da kuma gama karatunsa na share fage a garuruwan Arak da
Khumain, yayi hijira zuwa birnin Kum don ba da tasa gudummawar wajen
karfafa sabuwar makarantar Hawzar garin. Daga baya ya yi fice wajen
karantar da ilmummukan fikihu, falsafa da sufanci.
Rasuwar
Ayatullah Ha'iri a ranar 10 ga Bahman 1315 hijira shamsiyya (10 ga watan
Janairun 1937) ta sanya makarantar Hawzar Kum cikin hatsarin rugujewa,
sai dai wasu malamai masu sadaukarwa sun ba da ta su gudummawar wajen
ganin hakan ba ta faru ba. Cikin shekaru takwas din da aka yi, kula da
makarantar ta kasance ne karkashin kulawar manyan malamai irinsu
Ayatullah Sayyid Muhammad Hujjat, Sayyid Sadraddin Sadr da Sayyid
Muhammad Taki Khunsari. A daidai wannan lokaci, musamman bayan faduwar
gwamnatin Ridha Khan, yanayi yayi kyau da ya ba da dama wajen sake samar
da cibiyar marja'iyya. A lokacin babu wanda ya dace ya maye gurbin
Ayatullah Ha'iri da kuma kare makarantar Hawza daga faduwa kamar
Ayatullah Burujerdi. Wannan hukumci na nada Ayatullah Burujerdi ya samu
goyon bayan daliban Ayatullah Ha'iri ciki kuwa har da Imam Khumaini. A
daidai wannan lokaci Imam da kansa ya yi ta kokari wajen ganin Ayatullah
Burujerdi ya dawo garin Kum don rike shugabancin makarantar garin.
Imam
Khumaini, sanadiyyar irin sanya ido kan yanayin da al'umma da
makarantar Hawzar take ciki, da kuma karance-karance litattafa, jaridu
da mujallu da kuma ziyarar da yake kai wa Tehran da ganawa da manyan
malamai irin su Ayatullah Mudarris, ya fahimci cewa hanya guda ta
magance mummunan yanayin da ake ciki bayan rashin nasarar yunkurin
tsarin mulki musamman bayan darewar mulkin Ridha Khan ita ce taka
tsantsan din makarantar Hawza, da tabbatar da alaka ta ruhi tsakanin
malamai da al'umma.
A wannan kokari da Imam yake yi na karfafa
makarantar Hawza ne ya sa a shekarar 1328 (1949) bisa goyon bayan
Ayatullah Murtadha Ha'iri suka tsara wani shiri na kawo canji inda suka
gabatar da shi ga Ayatullah Burujerdi. Wannan shiri ya fuskanci
amincewar daliban Imam da sauran daliban da suke da wayewa.
Sai
dai ita gwamnatin ta yi kuskure, saboda a ranar 16 Mehr 1341 (8 ga
Oktoba 1962) majalisar hukumar Asadullah Alam ta amince da cire wasu
dokokin karamar majalisar kasa, kamar dokar da ta shardanta cewa dole ne
dan takara ya zamanto musulmi, rantsuwa da Alkur'ani mai girma,
sharadin mazantaka ga 'yan takara da masu jefa kuri'a. Babu makawa akwai
wata boyayyiyar manufa cikin amincewa da barin mata su kada kuri'a (da
hukumar ta yi), kamar yadda cire sharadin Musulunci da mazantaka shi ma
da wata manufa aka yi shi, ita ce kuwa shigar da 'yan Baha'iyya cikin
al'amurran gudanarwa da ba su manyan mukamai cikin gwamnati.
Kamar
yadda muka nuna a baya, taimako da goyon bayan haramtacciyar kasar
Isra'ila da fadada alakar Iran da ita na daga cikin sharuddan da Amurka
ta kafa wa gwamnatin Shah matukar tana son goyon bayanta. Don haka ne ya
zamanto dole a bar 'yan kungiyar Baha'iyya ta 'yan mulkin mallaka su
kame manyan bangarorin gwamnati don cika wannan sharadi. Jin kadan bayan
watsa wannan labari, Imam Khumaini da wasu manyan malaman biranen Kum
da Tehran, bayan wata tattaunawa, suka sanar da rashin amincewarsu da
dokar.
Imam Khumaini ya ba da gagarumar gudummawa wajen fallasa
asiri da manufofin gwamnatin Shah da kuma bayyana hakikanin nauyin da ya
hau kan malamai da makarantun Hawza cikin halin da ake ciki. Hakan ne
ya sa aka samu wasu malamai suka aike da wasu wasiku na nuna rashin
amincewa ga Shah da priminista Alam, hakan ya faranta wa al'umma rai.
Amma wasikun da Imam ya aike wa Shah da priministansa sun fi na sauran
malaman tsauri da kuma jan kunne. A cikin daya daga cikin irin wadannan
wasiku, Imam yana cewa: "Ina sake muku nasiha da tsoron Allah da kuma
bin tsarin mulki, sannan ku guji saba wa Alkur'ani da dokokin malamai da
shuwagabannin musulmi da kuma watsi da dokokin kasa; kada ku sanya kasa
cikin hatsari da gangan, idan kuwa ba haka ba, malaman Musulunci ba za
su daina yin maganganu a kanku ba".
Haka dai wannan batu na dokar
kananan hukumomi ya kasance nasara ga al'umma kana kuma lamari mai
muhimmanci gare su, musamman ma ganin cewa sun fahimci siffofin mutumin
da ya cancanci ya jagoranci al'ummar musulmi. Duk da wannan rashin
nasara da Shah ya fuskanta, to amma Amurka ta ci gaba da matsa masa
lamba wajen ci gaba da canje-canjen da zai ba ta damar cimma
manufofinta. Don haka Shah a watan Dey 1341 (Janairun 1962) ya gabatar
da jiga-jigan shirinsa na canji guda shida da kuma bukatar a gudanar da
jin ra'ayin al'umma kansu.
Har ila yau Imam Khumaini ya sake
bukatar maraja'ai da manyan malaman garin Kum da su zauna don tattaunawa
kan halin da ake ciki da kuma yiyuwar sake kaddamar da wani sabon
yunkuri.
A ci gaba da goyon bayan da mutane suke nuna wa Imam,
al'umma sun kaurace wa bukukuwan "Nuruz" (sabuwar shekara) don nuna
rashin amincewa da ayyukan gwamnati. A cikin sanarwar da Imam ya fitar
kan hakan, ya ambaci "Farin Yunkuri" (White Rebolution) na Shah da sunan
"Bakin Yunkuri" (Black Rebolution), sannan kuma ya tona asirin manufar
Shah ta biyan bukatun Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila. A bangare
guda kuma, Shah, wanda ya tabbatar wa Amurkawa cewa al'ummar Iran sun
amince da canje-canjen da yake son yi don cimma manufofin Amurka da ya
ba shi sunan "White Rebolution", ya fahimci cewa rashin amincewar da
malamai suke yi gare shi zai haifar masa da matsaloli masu girman gaske.
A
cikin hudubobi da jawaban da ya dinga yi a gaban jama'a, Imam Khumaini
ya dora alhakin wannan zalunci a kan Shah, kamar yadda kuma yake kiransa
da dan koran haramtacciyar kasar Isra'ila da kiran al'umma da su yi
masa bore. A wani jawabi da ya gabatar a ranar 12 ga Farbardin 1342 (1
Aprilu 1963) Imam ya yi Allah wadai da shirun da malamai suka yi a
garuruwan Kum, Najaf da sauran garuruwan musulmi kan wannan danyen aiki
na gwamnatin Shah, yana mai cewa: "Lalle a yau shiru yana nufin nuna
goyon baya ga wannan hukuma ta zalunci". Washegari kuma wato ranar 13 ga
Farbardin 1342 (2 Aprilu 1963) Imam ya fitar da sananniyar sanarwar nan
tasa mai suna "Kaunar Shah Wasoso Ne".
Haka nan idan ana son
fahimtar irin tasirin da kalaman Imam suke da shi a zukatan masu
sauraronsa da har suke iya fita su ba da rayukansu, to dole ne a dubi
asali da kiran nasa yake da shi da kuma irin gaskiya ta hakika da ke
tare shi.
Shekarar 1342 hijira shamsiyya (1963) ta fara ne da kin
fitowar da al'umma suka yi don bukukuwan "Nurooz" (sabuwar shekara)
sakamakon kiran da malamai suka yi, da kuma zubar da jinin mutanen da ba
su ci ba su sha ba a makarantar Fa'iziyya da ke birnin Kum. A bangare
guda, Shah ya dage sai ya aiwatar da shirinsa na kawo canjin da Amurka
ta ke bukata, a bangare guda kuma Imam Khumaini ya dage wajen wayar da
kan al'umma wajen tsayawa da fuskantar tsoma bakin Amurka cikin
al'amurran cikin gidan Iran da kuma ha'incin Shah.
A ranar 14 ga
watan Farbardin 1342 (1963), Ayatullah al-Uzma Hakim daga garin Najaf ya
aike wa wasu manyan malamai da maraja'ai na Iran da wasika yana kiransu
da yin hijira ta gaba daya zuwa garin Najaf. Wannan kira dai an yi ta
ne da nufin kiyaye rayuwar malamai da makarantar Hawza.
Imam ya
yi kunnen uwar shegu da wannan barazana, don haka sai ya aikewa
Ayatullah Hakim amsar wasikar da ya rubuto yana mai ce masa yana ganin
babu wata maslaha ta Musulunci cikin yin hijira ta gaba daya da barin
Hawzar Kum haka nan.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 12 ga
watan Farbardin 1342 (22 Aprilu 1963) a lokacin bukukuwan kwanaki
arba'in na shahadar (daliban) Fa'iziyya, Imam Khumaini ya jaddada goyon
bayan malamai da al'ummar Iran ga jagororin kasashen musulmi da na
larabawa wajen fuskantar haramtacciyar kasar Isra'ila, kamar yadda kuma
yayi Allah wadai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sarki Muhammad
Ridha Pahlawi da haramtacciyar kasar Isra'ila.
YUNKURIN 15 GA KHORDAD (5 GA YUNI):
Watan
Muharram na shekarar 1342 yayi daidai da watan Khordad ne (Yunin 1963)
don haka Imam Khumaini ya yi amfani da wannan dama wajen motsa mutane da
fuskantar hukumar kama-karya ta Shah.
A yammacin ranar Ashuran
ta shekara ta 1383 hijiriyya (3 ga Yunin 1963) Imam ya gabatar da wani
jawabi mai cike da tarihi a makarantar Fa'iziyya wanda shi ne matakin
farko na yunkurinsa na 15 ga watan Khordad (5 Yuni).
A cikin
wannan jawabi, yayin da yake magana da Shah, Imam yana cewa: "Ya Shah
ina maka nasiha! Ya kai mai girma Shah, ina maka nasiha da ka janye
hannayenka daga wadannan ayyuka naka! Suna yaudarar ka ne. Ba na son in
ga mutane suna cikin farin ciki da murna idan har suka yi waje da
kai..ina kiranka da ka yi tunani kan abin da suke sa ka fadi…ka saurari
nasihata. Mece ce alakar da ke tsakanin Shah da (haramtacciyar kasar)
Isra'ila da har 'yan SABAK (jami'an tsaron Shah) suke cewa kada ku fadi
magana kan Isra'ila? Shin Shah Ba'isra'ile ne?". Shah dai ya ba da
umarnin gamawa da wannan yunkuri. Da farko jami'an tsaro sun kame da
dama daga cikin magoya bayan Imam a daren 14 ga Khordad (4 ga Yuni),
kusan asubahin washe gari kuwa da misalin karfe 3 na asuba darurrukan
'yan sandan da aka aiko daga Tehran sun kewaye gidan Imam da nufin kama
shi a lokacin yana sallar dare. Don haka bayan kama shi sai suka wuce da
shi cikin gaggawa zuwa Tehran inda suka fara tsare shi a wajen tsare
mutane na 'Officer's Club' daga baya kuma da yamma suka wuce da shi zuwa
gidan yarin Kasr na birnin. Da safiyar 15 ga watan Khordad labarin kama
Imam ya yadu zuwa garuruwan Tehran, Mashhad, Shiraz da sauran garuruwa
lamarin da ya sa aka samu irin yanayin da aka samu a garin Kum na boren
jama’a. A cikin littafin da ya rubuta abubuwan da suka faru a rayuwarsa,
wani na kurkusa da Shah Janar Fardoust ya bayyana yadda aka zabi
jami'an tsaro na musamman bisa taimakon Amurka don kawo karshen wannan
yunkuri, sannan kuma yayi bayani kan irin halin damuwa da dar-dar din da
Shah, ministoci da jami'an gwamnatinsa, janar-janar da sojinsa da kuma
'yan SABAK suka kasance ciki a wancan lokacin, da kuma yadda Shah da
jami'ansa suka ta ba da umarni ba kan gado don kawo karshen boren da
jama'a suke yi. Bayan kwanaki 19 a gidan yarin Kasr, hukuma ta dauke
Imam daga inda ake tsare da shi zuwa gidan yarin da ke barikin soji na
Eshrat Abad.
Ana iya cewa ya zuwa wani haddi an cutar da wannan
yunkuri sakamakon kama jagoransa da aka yi a ranar 15 ga Khordad da kuma
kisan kiyashin da aka yi wa magoya bayansa. Shi kuwa Imam ya ki ba da
hadin kai da amsa tambayoyin masu masa tambayoyi a inda ake tsare da shi
yana mai nuna cewa ba sa da hurumin yi masa tambayoyi. Don haka a
yammacin 18 ga watan Farbardin 1343 (1964) ba tare da wata sanarwa ba
sai gwamnatin ta sake Imam da daukansa zuwa Kum. Jin wannan labari ke da
wuya sai dukkan garin ya cika da bukukuwa da farin ciki, aka ci gaba da
shirya bukukuwa a makarantar Fa'iziyya da sauran gurare har na tsawon
ranaku. An gudanar da bukin shekarar farko ta tunawa da abin da ya faru a
ranar 15 ga watan Khordad a shekarar 1343 da wasu bayanan hadin gwuiwa
da Imam Khumaini da sauran maraja'ai suka fitar, da kuma wani bayanin na
daban da makarantar Hawza ta fitar don girmama wannan rana da sanya
mata sunan ranar zaman makomi ta gaba daya.
A wannan rana (ta 4
ga Aban), Imam Khumaini ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa: "Ya
kamata al'ummar duniya ta san cewa dukkan wata wahala da matsalolin da
al'ummar Iran da na musulmi suke ciki daga Amurka ne, daga baki 'yan
kasashen waje ne. Al'ummar musulmi dai ba sa kaunar dukkan bakin haure
musamman ma Amurka. Don kuwa Amurka ce take goyon bayan (haramtacciyar
kasar) Isra'ila da kawayenta. Amurka ce ta karfafa (haramtacciyar kasar)
Isra'ila don mayar da musulmi marasa matsuguni..".
Nuna rashin
amincewar Imam ga wannan dokar (ba da kariya ga ‘yan kasar Amurka a
Iran) ta sake sanya Iran cikin yanayi na sabon bore da yunkuri a watan
Aban 1343 (1964). Da asussubahin ranar 13 ga watan Aban 1343 (1964),
jami'an tsaro na musamman da aka turo daga Tehran sun sake mamaye gidan
Imam dake garin Kum, inda suka sake kama shi, kamar yadda ya kasance a
shekarar da ta gabata, alhali yana cikin salla da addu'oi, suka wuce da
shi kai tsaye zuwa filin jirgin saman Mehr Abad da ke Tehran da sanya
shi cikin wani jirgin saman soji da daman yake jira sai garin Ankara na
kasar Turkiyya. Da hantsin wannan rana, jami'an tsaron SABAK, cikin
jaridun kasar, sun sanar da koran Imam saboda zargin barazana ga tsaron
kasa. Duk da irin halin dar-dar da ake ciki sai da al'ummar birnin
Tehran suka fito don yi zanga-zanga a kasuwar birni don nuna rashin
amincewarsu da wannan aiki, sannan kuma aka rufe makarantun Hawza na
wani tsawon lokaci kana kuma aka aike da wasiku ga kungiyoyin kasa da
kasa da kuma maraja'ai.
Imam ya zauna a Turkiyya ne na tsawon
watannin goma sha daya. A daidai wannan lokaci kuwa gwamnatin Shah ta yi
kokari wajen ganin ta gama da sauran kurar bore ta hanyar amfani da
karfi sannan kuma ta gaggauta kaddamar da shirin nata da Amurka take son
ta gabatar. Imam ya yi amfani da zaman gudun hijira ta dole a kasar
Turkiyyan wajen rubuta da tsara shahararren littafin nan nasa mai suna
'Tahrir al-Wasila.
KORAR IMAM (R.A) DAGA TURKIYYA ZUWA IRAKI.
A
ranar 13 ga watan Mehr 1344 (13 Oktoba 1965) jami'an tsaro sun tura
Imam da dansa Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini zuwa gudun hijira ta
biyu wato daga Turkiyya zuwa kasar Iraki. Bayan isarsa birnin Bagadaza,
Imam Khumaini ya kai ziyara zuwa hubbarorin tsarkakan Imamai (a.s) da
suke garuruwan Kazimain, Samarra da Karbala, daga nan kuma bayan mako
guda, Imam ya wuce zuwa sabon masaukinsa da ke birnin Najaf mai tsarki.
Shekaru
sha ukun da Imam ya yi a garin Najaf (Iraki), duk da cewa babu matsin
lamba na kai tsaye kamar yadda ya fuskanta a Iran da Turkiyya, sun fara
ne cikin wani irin yanayi na nuna adawa da cutarwa mai tsanani daga
wajen wasu malaman jeka na yi ka da ma'abuta son duniya da suka sanya
tufafin ma'abuta addini da har ta kai ma, duk da irin hakurin da aka san
shi da shi, a wasu lokuta ya kan fito ya yi magana kan irin wahalar
jihadi da gwagwarmaya a wancan lokaci. To sai dai hakan ba su sanya ya
ja da baya da barin wannan tafarki da ya zaba wa kansa ba.
Don
haka ya fara karantar da fikihu a watan Aban 1344 (Nuwamban 1965) a
masallacin Sheikh al-Ansari da ke Najaf duk kuwa da irin matsin lamba da
adawar da ya dinga fuskanta, haka dai ya ci gaba da karantarwa har
lokacin da ya yi hijira zuwa birnin Paris na kasar Faransa. Irin karfin
ilmin fikihu da Usul da dai sauran ilmummukan Musulunci da Imam ya ke da
shi ya sanya cikin karamin lokaci, duk da irin matsalolin da yake
fuskanta, azuzuwansa sun kasance daga cikin mafi shahara da yawan
dalibai a makarantun Hawzan Najaf.
Tun isowarsa birnin Najaf,
Imam bai katse alakarsa da mujahidan da suke cikin Iran ba, ya kasance
ya kan aika musu da sakonni da wasiku yana mai kiransu da su ci gaba da
tsayin daka wajen kiyaye manufar wannan yunkuri na 15 ga watan Khordad.
Duk
da irin yanayi mai tsanani da wahala da Imam Khumaini ya ke fuskanta a
inda yake gudun hijira, to amma hakan ba su sa shi ya bar tafarkinsa na
jihadi da fuskantar gwamnatin Shah ba. A kusan ko da yaushe yana ci gaba
da sanya ruhin kyakkyawar fata da nasara a zukatan al'umma ta hanyar
jawabai da sakonnin da yake aikewa da su ga mutanensa.
A ranar 19
ga watan Mehr, 1347 (9 ga Oktoba 1968) a wata ganawa da ya yi da
wakilin kungiyar Fatah mai fafutukan 'yanto kasar Palastinu, Imam
Khumaini ya bayyana mahangarsa kan matsalolin da duniyar musulmi ke ciki
da kuma yunkurin al'ummar Palastinu. A yayin wannan ganawa, Imam ya ba
da fatawar wajibcin kebance wani sashi na zakka da ba da shi ga 'yan
gwagwarmayar Palastinu.
A farko-farkon shekarar 1969 rikicin da
ke tsakanin gwamnatin Shah da gwamnatin Ba'athawa ta Iraki kan iyakan
kasashen biyu na ruwa ya tsananta. Hakan ya sanya gwamnatin Iraki korar
adadi mai yawa na Iraniyawa da ke zaune a kasar, kamar yadda kuma
gwamnatin ta yi kokarin amfani da irin adawan da Imam yake yi wa
gwamnatin Shah don cimma manufarta.
Shekaru hudu na koyarwar Imam
da kuma irin kokarin da yake yi wajen wayar da kan mutane ya sanya an
samu 'yan canje-canje a makarantun Hawzan birnin Najaf. A shekarar 1348
(1969) wannan yunkuri na Imam ya samu wasu sabbin magoya baya daga
kasashen Iraki, Lebanon da sauran kasashen musulmi wadanda suka dauki
yunkurin a matsayin abin koyi.
IMAM KHUMAINI DA CI GABAN GWAGWARMAYA (1350-1356 = 1971-77)
A
karshe-karshen shekarar 1971, kai ruwa ranan da ke tsakanin gwamnatin
Ba'athawa ta Iraki da gwamnatin Shah ya tsananta lamarin da ya yi
sanadiyyar korar dubban Iraniyawa da suke zaune a kasar. Nan take Imam
ya aike da wasika zuwa shugaban kasar yana yin Allah wadai da wannan
aiki sannan kuma ya sanar da aniyarsa ta barin kasar, sai dai hukumar ta
hana shi saboda tsoron abin da zai iya biyo baya. A yayin bukukuwan
zagayowar shekarar yunkurin 15 ga watan Khordad a shekarar 1975, dalibai
a makatantar Fa'iziyya ta Kum sun gudanar da zanga-zangogi na kawanki
biyu cikin makarantar suna masu rera taken "Aminci ya tabbata ga
Khumaini", "Mutuwa a kan gidan sarautar Pahlawi". Duk da cewa hukuma ta
haramta kungiyoyi da jam'iyyu masu adawa da ita sannan kuma da dama daga
cikin ma'abuta addini da 'yan siyasa masu jihadi suna tsare a gidahen
yari, amma duk da hakan kungiyoyi masu jihadin sun haifar da gagarumar
hasara ga hukumar, hakan ne ya sanya jami'an tsaro (SABAK) suka fada wa
makarantar da musguna wa dalibai musgunawa mai tsanani da kuma tsare su a
gidajen yari.
A ci gaba da ayyukansa na kiyayya da Musulunci, a
watan Esfand 1354 (Fabrairun 1975), Shah ya canza kalandar (kwanakin
wata) da hukuma take amfani da ita da ta fara daga hijiran Ma'aikin
Allah (s.a.w.a) ya zuwa farkon mulkin mulukiyya Hakhamanshiyyawa. Imam
Khumaini ya mayar da kakkausar martini ta hanyar fitar da fatawar
haramcin amfani da wannan kalanda. Kamar dai yadda al'umma suka karbi
fatawar haramcin shiga jam'iyyar Rastakhiz da Imam ya bayar, haka ma a
wannan karon suka karbi wannan fatawa da hannu bibbiyu. Dukkan wadannan
abubuwa biyu ana ganinsu a matsayin bugun hanci ga Shah. Hakan ya
tilasta masa janye wannan sabuwar kalanda tasa a shekarar 1357 (1977).
KAMARIN JUYIN MUSULUNCI DA YUNKURIN AL'UMMA A 1356 (1977)
Imam
Khumaini wanda ya kasance mai sanya ido sosai kan abubuwan da ke gudana
a Iran da sauran kasashen duniya, ya yi kokarin amfani da duk wata
damar da ya samu. A watan Mordad 1356 (Augustan 1977), cikin wani sako
da ya aika, ya bayyana cewar: "Bisa la'akari da yanayin cikin gida da
waje, da kuma buga irin ayyukan zalunci da hukuma take yi a jaridun
kasashen waje, hakan dama ce ga masana, 'yan jami'a da ke karatu a ciki
da wajen kasa da kuma kungiyoyin Musulunci a duk inda suke da ya kamata
su amfana da ita wajen fuskantar hukuma".
Shahadar Ayatullah
Sayyid Mustafa Khumaini a ranar 1 ga watan Aban 1356 (1977) da kuma irin
tarurrukan zaman makokin da aka shirya a Iran sun kasance abubuwan da
suka sake motsa makatantun Hawza da al'ummar Iran wajen sake fitowa don
fuskantar hukuma. Shi kuwa a nasa bangaren, Imam Khumaini ya bayyana
wannan lamari (na shahadar Sayyid Mustafa) a matsayin wata boyayyiyar
ni'imar Ubangiji, wanda hakan ya zamanto abin ban al'ajabi ainun.
Gwamnatin Shah ta yi kokarin cin mutumcin Imam ta hanyar watsa wata
makala ta cin mutumci gare shi cikin jaridar Ittila'at. Sai dai wannan
karon ma shika ta koma kan mashekiya ne, don kuwa maimakon hakan sai ta
kasance ummul aba'isin din boren al'umma a ranar 19 ga watan Dey 1356 (9
ga Janairu 1977) da nuna goyon bayansu ga Imam lamarin da ya yi
sanadiyyar shahadar wasu dalibai ma'abuta jihadi da raunana wasu da dama
a lokacin da jami'an tsaro suka fada musu. Duk da irin ayyukan zalunci
da wuce gona da iri da gwamnatin Shah take yi a kan 'yan gwagwarmaya,
sai dai duk da hakan hukumar ta gagara kashe wutan wannan bore. Imam
yana ganin babu wani amfani wajen gwagwarmayar 'yan majalisa, jam'iyyun
siyasa da karfin soji ba tare da goyon bayan al'umma ba, kamar yadda
kuma yake ganin hanya guda da ta rage ita ce kaddamar da jihadi matukar
Amurka ta yi tunanin shirya juyin mulkin soji.
HIJIRAR IMAM DAGA IRAKI ZUWA PARIS
A
wata tattaunawa da ta gudana tsakanin ministocin harkokin wajen
kasashen Iran da Iraki a birnin New York na Amurka, ministocin biyu sun
yanke shawarar korar Imam Khumaini daga Irakin. Don haka a ranar 2 ga
watan Mehr 1357 (24 ga Satumba 1978), jami'an tsaro suka mamaye gidan
Imam da ke birnin Najaf mai tsarki, hakan dai ya fusata al'umman musulmi
na kasashen Iran, Iraki da sauran kasashen duniya.
Don haka a
ranar 12 ga watan Mehr (4 ga Oktoban 1978), Imam Khumaini ya bar birnin
Najaf ya nufi kasar Kuwaiti, sai dai kasar Kuwaitin ta ki amincewa ya
shigo kasar sakamakon matsin lamban gwamnatin Iran. Ganin haka ya sa
wasu suka ba da shawarar a tafi kasar Siriya ko Labanon, to sai dai shi
Imam Khumaini bayan shawara da dansa Hujjatul Islam Sayyid Ahmad
Khumaini, ya yanke shawarar tafiya birnin Paris na kasar Faransa. Don
haka Imam ya isa birnin Paris a ranar 14 ga Mehr 1357 (6 ga Oktoba 1978)
inda aka saukar da shi a gidan wani Ba'iraniye a unguwar Noefel Le
Chateau da ke wajen birnin.
A can ma mahukunta ba su barshi ba
don bayan wani lokaci jami'an kasar Faransan sun zo wajensa da nufin
sanar da shi mahangar shugaban kasar na lokacin kan zaman Imam a kasar
suna masu sanar da shi cewa dole ne ya janye hannayensa daga harkokin
siyasa. Imam Khumaini ya mayar da kakkausar martini ga wannan bukata ta
su yana mai cewa hakan ya saba wa ikirarin riko da tsarin demokradiyyar
da Faransan take yi, yana mai karawa da cewa ko da lamarin zai kai ne ya
dinga yawo daga wannan filin jirgi zuwa wancan, ba fa zai bar wannan
tafarki nasa ba.
Imam Khumaini, a watan Dey 1357
(Disambar 1978), ya kafa majalisar juyin juya halin Musulunci don share
fagen kafa hukuma ta Musulunci da kuma dawowarsa gida. A dai dai wannan
lokaci kuwa Shah yana ta shirin gudu ya bar kasar sakamakon yadda ya ga
al'amurra suna ta ficewa daga hannunsa. Don haka kwanaki biyu da kafa
majalisar shawara da tattaunawa don nema wa gwamnatin Bakhtiyar goyon
baya, sai ya gudu ya bar kasar a ranar 26 ga watan Dey 1357 (16 ga
Disamba 1978). Jin labarin gudun Shah ke da wuya, jama'a a duk fadin
Iran sun fito kan tituna don nuna farin cikinsu.
DAWOWAR IMAM GIDA BAYAN SHEKARU 14 NA GUDUN HIJIRA
Tun
farko-farkon watan Bahman 1357 (1979) labarin shawarar da Imam ya yanke
na dawowa gida ya yadu ko ina. Jama'a kuwa duk wanda ya ji wannan
labari sai ya zubar da hawaye don murna, don kuwa abin da suke jira
kenan har na tsawon shekaru 14, duk da cewa suna cikin damuwa kan tsaron
lafiyarsa, don har zuwa lokacin gwamnatin jeka na yi kan Shah ita ce ke
mulki, sannan ga kuma dokan ta bacin da ta kafa na ci gaba da aiki.
Imam Khumaini ya riga da ya dauki matsaya ta karshe, don haka sai ya
sanar da al'ummar Iran, cikin wani sako da ya aike musu, cewa yana son
ya kasance tare da su a wadannan ranaku masu muhimmanci. Hakan ya sanya
gwamnatin Bakhtiyar, bisa hadin gwuiwan Janar Haizer, suka rufe filin
jirgin saman birnin Tehran sashin zirga-zirgan waje.
Bayan wasu
'yan kwanaki, gwamnatin Bakhtiyar ta bude filin jirgin sama saboda
gagarar da ta yi wajen jure wa wannan bore na al'umma. Daga karshe, a
safiyar ranar 12 ga watan Bahman 1357 (1 ga watan Fabrairun 1979) Imam
Khumaini ya dawo gida bayan shekaru 14 na gudun hijira. Irin gagarumar
tarbar da al'umma suka yi masa ya kai matsayin da hatta kafafen watsa
labaran yammaci sun gagara inkarin hakan, inda su da kansu suka ce
mutanen da suka tarbi Imam Khumaini sun kai miliyan 4 zuwa 6.
WAFATIN IMAM KHUMAINI: RABUWA DA MASOYA, HADUWA DA ABIN KAUNA:
Hakika
Imam Khumaini ya isar da abin da yake son fadi da kuma cimma abin da
yake son cimmawa tsawon rayuwarsa a aikace. Don haka a halin yanzu cikin
tsakiyar watan Khordad 1368 (farko-farkon watan Yuni 1989) yana ta kan
shirye-shiryen ganawa da Abin kaunarsa da ya gudanar da dukkan rayuwarsa
don neman yardarSa. Wanda ya kasance bai taba mika kai ga wani bayanSa
ba, kamar yadda bai taba zubar da hawaye ba sai don Shi, sannan kuma
dukkan wakokin irfanin da ya rera (ko rubutawa) sun kasance suna bayanin
kan dacin rabuwa da Abin kauna da kuma shaukin da yake yi na saduwa da
Shi. A halin yanzu da lokacin yake gabatowa, duk da cewa abu ne da
masoyansa ba za su iya jurewa ba, ya rubuta cikin wasiyyarsa cewa: "Ina
muku sallama 'yan'uwana maza da mata, cikin kwanciyar hankali da rai mai
natsuwa da ruhi mai farin ciki da zuciya mai fatan falalar Allah, in
kama hanya zuwa ga gidana na har abada. Kuma ina mai matukar bukatar
addu'arku ta alheri. Sannan ina rokon Allah Mai rahama da jin kai Ya
karbi uzurina na karancin hidima da kurakurai da gazawa. Kuma ina fata
jama'a za su karbi uzurina cikin kowane karanci na hidima da kurakurai
da gazawa, kuma su ci gaba da karfi tare da kakkarfar aniya..
Babban
abin ban al'ajabin shi ne cewa tun kafin shekaru da rasuwarsa, Imam
Khumaini, cikin wasu baitocin wake ya yi batun rasuwarsa cikin watan
Khordad inda yake cewa:
Shekaru suna wucewa abubuwa suna ta faruwa
Ni kuwa ina sauraron nasara a tsakiyan Khordad
Daidai
karfe sha daya da minti ashirin na dare ranar asabar 13 ga watan
Khordad 1368 (3 ga Yuni 1989) lokacin saduwa da abin kauna ya yi. A
daidai wannan lokaci ne zuciyar da ta haskaka zukatan miliyoyi da hasken
Allah ta tsaya cak (ta bar aiki). A daidai wannan lokaci masoya Imam
sun boye wata kamara (na'urar daukan hoto) a asibitin da yake kwance don
daukan abubuwan da ke gudana da aikin da aka masa har zuwa lokacin
saduwa da abin kauna. Don haka lokacin da gidan talabijin din Iran ya
nuna halin kwanciyar hankalin da Imam ya ke ciki a lokacin, kai kace
zukatan al'umma za su fashe saboda shaukin da ba za a iya siffanta shi
ba.
A lokacin lebbansa cike suke da ambaton Allah, a daren karshe
na rayuwarsa ma'abuciya daukaka a daidai lokacin da dantsensa yake
daure da alluran da ake kara masa ruwa, amma sai ga shi ya mike don
sallar dare da kuma karatun Alkur'ani mai girma. A daidai sa'oin karshe
na rayuwarsa, ba abin da ake gani face kwanciyar hankali da nitsuwa ta
Ubangiji yana mai ikirari da kadaitakan Ubangiji da imani da sakon Manzo
(s.a.w.a) har lokacin da aka dauki ransa zuwa wajen Ubangijinsa. Wannan
rasuwa da ta rura wutan bakin ciki a zukata.
Lokacin da aka
watsa labarin rasuwar Imam, kai ka ce wata gagarumar girgizar kasa ce ta
faru, ko ina sai bakin ciki idanuwa kuwa a cikin Iran da sauran wuraren
da aka san Imam kana kuma shiriyarsa ta shiga sai zubar da hawaye suke.
Masoyansa sai fitowa suke suna dukan kawuka da fuskokinsu da alkaluma
da duk wani irin bayani ya zaga wajen bayyana hakikanin abubuwan da suka
faru da irin bakin cikin da ake ciki. Lalle mutanen Iran da sauran
ma'abuta juyi suna da hakkin yin irin wannan kururuwa da tarihi bai taba
ganin irin girma da tsananinsa ba, don kuwa sun rasa wani masoyi ne da
ya dawo musu da mutumci da daukakan da suka rasa, sannan ya katse
hannayen muggan shugabanni da 'yan mulkin mallakan Amurka da sauran
kasashen yammaci daga kasashensu, sannan kuma ya raya Musulunci da
hakkokin musulmi da mutumcinsu, ya kuma tsai da Jamhuriyar Musulunci, ya
tsaya kyam a gaban karfin shaidan don fuskantar darurrukan
makirce-makircensu na kawar da gwamnatin Musulunci da haifar da fitinar
cikin gida da waje tsawon shekaru goma. Kamar yadda kuma ya jagoranci
yakin kariya na shekaru takwas yana fuskantar makiyan da suke samun
goyon bayan gwamnatocin gabashi da yammaci ma'abuta girman kai. Hakika
al'umma sun rasa jagoransu abin kauna sannan kuma makomarsu na addini
kana kuma mai kira zuwa ga Musulunci na hakika.
Mai yiyuwa ne
mutanen da suka gagara fahimtar hakikanin wannan lamari su kasance cikin
rudani lokacin da – gidan talabijin ya nuna - halin da mutane suke ciki
yayin jana'iza da bisne jikin Imam mai tsarki. Mai yiyuwa ne su sha
mamaki lokacin da suka ji labarin rasuwar mutane masu yawa da suka
gagara jurewa wannan babban rashi don haka zuciyarsu ta tsaya cak ko
kuma na faduwar wasu gomomin mutane sakamakon tsananin bakin ciki da dai
sauran abubuwa makamantan haka da suka faru. Sai dai mutanen da suka
san ma'anar kauna kana kuma zukatansu suka ta'allaka da shi cikin sauki
za su iya fahimtar lamarin da kuma ganinsa ba a bakin komai ba. A
hakikanin gaskiya al'ummar Iran sun kasance masu tsananin kaunar Imam
Khumaini, don haka yayin zagayowar shekarar rasuwarsa suke rera taken:
"Kaunar Khumaini kaunar dukkan abubuwa masu kyau ne".
A ranar 14
ga watan Khordad 1368 (4 ga watan Yunin 1989), majalisar kwararru (ta
zaban jagora) ta gudanar da taronta, inda bayan da Ayatullah Khamene'i
ya karanta wasiyyar marigayi Imam Khumaini da ya dauke sa'oi biyu da
rabi, 'yan majalisar suka fara gudanar da tattaunawa da shawara kan
wanda zai gaji Imam don zama jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Bayan
sa'oi na tattaunawa, dukkan 'yan majalisar sun amince da zaban Ayatullah
Sayyid Ali Khamene'i (wanda a lokacin shi ne shugaban kasa) a matsayin
sabon jagora. Ayatullah Khamene'i dai ya kasance daga cikin daliban Imam
Khumaini (r.a) na kurkusa kana kuma daga cikin fitattun mutanen da suka
ba da gagarumar gudummawa a Juyin Juya Halin Musulunci kuma daga cikin
wadanda suka taimaka nesa ba kusa ba wajen kaddamar da yunkurin 15 ga
watan Khordad, wanda ya tsaya kafada-kafada da sauran mataimakan juyin
da ba da gagarumar sadaukarwa duk tsawon yunkurin Imam Khumaini da kuma
dukkanin abubuwan da suka faru daga baya.
Shekara da shekaru
kasashen yammaci da 'yan amshin shatansu na cikin gida sun kasance cikin
dakon wannan rana ta rasuwar Imam bayan sun yanke kaunar samun nasara a
kansa. Sai dai farkawar al'ummar Iran da kuma saurin da majalisar
kwararrun ta yi wajen zaban mutumin da ya dace da wannan matsayi na
jagoranci da kuma irin goyon bayan da mabiya Imam suka yi wa zaben ta
sanya makiyan cikin damuwa da kawo karshen mummunan fatansu. Don kuwa ba
ma wai kawai juyin Imam bai zo karshe ba ne (kamar yadda makiyan suka
so), face ma dai juyin ya sake bude wani sabon shafi ne na ci gaba da
watsuwa da kuma karfi. Shin tunani, alheri da gaskiya suna iya gushewa?
A
rana da daren 5 ga watan Yuni 1989 miliyoyin al'umma birnin Tehran da
sauran al'ummomin da suka shigo garin daga garuruwa da kauyuka sun taru a
babban wajen salla (musalla) na Tehran don yin ban kwana ta karshe da
mutumin da ya dawo da mutumcin da daukaka (wa al'umma) a duniyar da take
cike da duhu da zalunci ta hanyar yunkuri da juyinsa kana kuma ya watsa
yunkurin komawa ga Allah Madaukakin Sarki da daukakar dan'Adam a duk
fadin duniya.
Dukkanin abubuwan da aka yi a wajen jana'izar da
hannun al'umma aka yi shi, cikin kauna da shauki. An dora jikin Imam mai
tsarki a wani waje da kowa zai iya ganinsa yana rufe da koren kyalle
tsakiyan miliyoyin masu juyayi, dukkansu cikin bakin ciki da zubar da
hawaye alhali suna magana da Imaminsu cikin harshen da ya sawwaka ga
kowa. Dukkanin hanyoyi da lungunan zuwa wajen sallar cike suke da
jama'an da suke sanye da bakaken kaya don nuna bakin cikinsu, gidaje da
shaguna kuwa duk an sanya musu tutocin juyayi da nuna bakin ciki,
karatun Alkur'ani kuwa daga ko ina, masallatai, ofisoshi, ma'aikatu da
gidaje sai tashi yake yi. Da daddare kuwa ko ta ina sai kyandir kake
gani an kunna su don nuna alamun hasken da Imam ya zo da shi, duk sun
haskaka wajen sallar da kewaye, alhali iyalai sun kewaye su (kyandir)
suna kallon haskensu don tuntuni da irin hasken da jagoransu abin
kaunarsu ya zo musu da shi.
Taken "Ya Husain" da masu juyayin
suke rerawa alhali suna dukan kirji da kawunansu ya mai da yanayin wajen
tamkar yanayin Ranar Ashurar da Imam Husaini (a.s) ya yi shahada. Bisa
la'akari da cewa al'umma ba za su sake jin sautin Imam Khumaini dake
cike da yanayin tunasar da mutum Ubangiji a Husaniyyar Jamaran ba, hakan
ya kasance abin tashin hankali ga al'umma. Haka dai mutane suka ci gaba
da zama a gefen jikin Imam mai tsarki duk tsawon dare har garin Allah
ya waye, inda da sassafiyar ranar 6 ga Yuni 1989 aka yi masa salla
karkashin limancin Ayatullah al-Uzma Golfaygani.
Babu shakka irin
yawan al'ummar da suka fito don tarbar Imam Khumaini a ranar 12 ga
watan Bahman 1357 (1 Fabrairu 1979) da kuma sake maimaita hakan a ranar
jana'izarsa, duk suna daga cikin abubuwan mamaki na tarihi. Kafafen
watsa labaran duniya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka fito
don tarbar Imam lokacin da ya dawo gida sun kai miliyan shida, amma
wadanda suka fito don jana'izarsa sun kai mutanen miliyan tara. Hakan
kuwa duk da cewa cikin wadannan shekaru goma sha daya na jagorancin Imam
Khumaini kasashen Turai sun yi dukkan abin da za su iya wajen nuna
adawarsu ga Jamhuriyar Musulunci da suka hada da kallafa mata yakin
shekaru takwas da dai sauran makirce-makirce da ya sanya al'ummar Iran
cikin mawuyacin hali na kunci da takurawa da kuma rasa abubuwan kaunarsu
masu yawan gaske wanda a bisa dabi'a hakan zai sanya su gaji da kuma
watsi da wannan juyi nasu, to sai dai ina hakan bai faru ba daga dukkan
bangarori. Don kuwa al'ummar da suka tarbiyyantu a makarantar Imam
Khumaini sun tasirantu da kuma imani da kalaminsa na cewa: "A duniya,
gwargwadon girma da darajar manufa, gwargwadon karfin jurewa wahala,
cutarwa, sadaukarwa da rashi na duniya ne".
Bayan da bisne jikin
Imam mai tsarkin ya ci tura sakamakon yawan jama'a, gidan radiyo ya
sanar da daga jana'izar har zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba don
haka jama'a su koma gidajensu. Sai dai jami'ai sun riga da sun san cewa
lokaci bayan lokaci jama'a za su ci gaba da zuwa wajen jana'izar ne, don
haka dai aka daure aka gudanar da ita a yammacin wannan rana duk kuwa
da irin wahalhalun da ake fuskanta. Wasu kafafen watsa labaran duniya ma
sun nuna wani sashi na wannan jana'iza.
Ta haka rasuwar Imam
Khumaini, kamar rayuwarsa, ta kasance matakin farko na sabuwar wayewa da
gwagwarmaya da kuma tabbatar da tafarki da ambatonsa har abada, don
kuwa gaskiya abar tabbata ce matukar duniya tana ci gaba da wanzuwa.